Falalar Sahabban Manzon Allah (S.a.w.w) !!!


DAGA CIKINSU AKWAI SALIHAN BAYI

A tarihin muslimci ya kawo mana halayya ta mutane daban-dabam da suka rayu a qarnuka daban-dabam. Daga cikin su ana samun salihai, kuma daga cikin su ana samun akasin haka.

Babu wani Annabi da ya rayu face ya sami Sahabban sa kala biyu, wasu muminai wasu kuma masu rauni (weak) .

Daga cikin muminan za ka ji rawar da suka taka wajen taimakawa wannan Annabin da suke tare da shi ta hanyar taimakon sa wajen isar da saqon Allah, wasu kuma sai ka ji irin zaqon qasa da suka riqa yiwa muslumci ta bayan fage.

Daga cikin falalar salihai cikin Sahabban Manzon Allah (S.A.W.W) ta kai wani abu na baiwa ko mu'ujizozi na bayyana tare da su.

Ya zo cikin Bukhari inda yake cewa;

Aliyu Bn Muslim ya bamu labari, Habbanu Bn Hilal ya bamu labari, Hammam ya bamu labari, Qatadata ya bamu labari daga Anas (R.A)  cewa; lalle wasu mutane biyu (2) sun fito daga wajen Annabi (S.A.W.W) cikin wani dare mai duhu 🌑, sai ga wani  💡 🏮 a gaban su har suka rabu (zuwa gidajen su), sai wannan haske ya rabu tare da su (ya bi kowanne daga cikin su).

Ma'amar yace, daga Sabit, daga Anas cewa " USAIDU BN HUDHAIR NE DA WANI MUTUM DAGA MUTANEN MADINA."

Hammad yace; Saabit ya bamu labari daga Anas cewa; " USAID BN HUDHAIR DA ABBAADU BN BASHRI NE A WAJEN ANNABI (S.A.W.W) ."

  (Bukhari, hadisi na 3805)

Irin wannan falala tana bayyana tare da mabiyan Limaman Ahlul-Bait (A.S) da kuma muminai na wannan zamani.

Sahidai sun kasance babban misali gare mu.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

     08126385470

4th November, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post