Ashe haka Qur'anin yan shi'a yake??

Wata sabuwa:- Ko kataba ganin Qur'anin yan shi'a!?

Ma'asumah Nigeria News Update 
Tare da Ishaq Muh'd Suleiman 

Qur'anin Ƴan Shia; yana da surori 114. Ayoyi 6236. Kalmomi; 77,439. Harrufa; 323,015. Juzi'i; 30. Hizfi 60. Rubu'i 240. Ushuri 480.

Surorin da aka saukar a Makkah a Qur'anin Ƴan Shia; 85 ne. Surorin Madinah; 29 ne. Surarin da suka fara da 'Alhamdu'; 5 ne. Surorin da suka fara da Tasbihi; 6 ne. Surorin da suka fara da harrufa; 19 ne.

Surah da ta fi tsawo a Qur'anin Ƴan Shia ita ce; Suratul-Baqara, ayoyin ta 286.

Aya mafi tsawo a Qur'anin Ƴan Shia ita ce aya da tayi magana akan bashi, aya ta 282 a Baqara, kalmomin ta 128.

Kalma mafi tsayi a Qur'anin Ƴan Shia ita ce; ﻓَﺄَﺳْﻘَﻴْﻨَﺎﻛُﻤُﻮﻩُ (Fa'asqainaakumuhu), (Hijir : 22), tana da harrufa 11 a rubutun ta na larabci.

Qur'anin Ƴan Shia; an saukar da shi cikin shekaru 23.

Qur'anin Ƴan Shia yana da sunaye kamar haka: Al-furqan, At-tanzeel, Az-zikir, Al-kitab, Al-wahayi, Ahsanul Hadith, As-siradul Mustaqim, Al-urwatul Wuthqa, Ar-ruhu...

Qira'ar da tafi shahara wajen karata Qur'anin Yan Shia ita ce ruwayar Hafs daga Asim..., (Qira'ar da isnadita yake tuƙewa zuwaga Imam Ali (As). Hafs ya bar duniya a shekara ta 180 H, Asim kuma 127H.

Annabin da aka fi ambaton sunansa a Qur'anin Ƴan Shi'a shine; Annabi Musa (As); a ambace shi sau 136.

Surorin da aka ambace su da sunan dabbobi a Qur'anin Ƴan Shia; Baqara (Saniya), Namli (Tururuwa), Ankabut (Gizo-Gizo, Nahli (Zuma), Fiyl (Giwa)...

Surorin da aka ambace su da sunayen Annabawa a Qur'anin Ƴan Shia; Suratu Yusuf (As), Suratu Hud (As), Suratu Ibrahim (As), Suratu Muhammad (saw), Suratu Nuh(As), Suratu Yunus (As)...

Surorin da aka ambace su da sunayen taurari a Qur'anin Yan Shia; Suratut Najm, Suratul Qamar, Suratud Dariq, Suratush Shams, Suratul Buruj...

Surorin da aka ambace su da sunayen lokuta a Qur'anin Ƴan Shia; Suratul Fajr, Suratul Laili, Suratud Dhuha, Suratul Asr...

Tsuntsaye da Dabbobin da aka ambace su cikin Qur'anin Yan Shia; Al-ba'ula (Sauro), As-Salwa, Al-Guraab (Hankaka), Al-Jarad (Fara), An-Nahl (Zuma), Az-Zubab (Kuda), Al-Baqara (Saniya), Zubaab (Kuda), Namli (Tururuwa), Al-Hudahuda, Naaqah (Raquma), Khail (Doki), Al-Bighaal (Alfadari), Al-Himar (Jaki), Az-Zi'b (Kyarkeci), Al-Kalb (Kare), Al-Fil (Giwa), Ankabuut (Gizo-Gizo, Al-Ibil (Rakumi)...

Sunayen Mala'ikun da suka zo cikin Qur'anin Ƴan Shia; Jibril (As), Mi'ika'il (As)...

Daular da aka ambata a Qur'anin Ƴan Shia ita ce; daular Rumawa - Rom,

Qabilar da aka ambata a Qur'anin Ƴan Shia ita ce; Quraishawa - (Quraish).

Littattafan Tafsiri da suka fi shahara a wajen Ƴan Shia; Al-mizan - Tabtaba'i, Tafsirut Tabari, Tafsiru Ibn Kasir, Tafsiru Ruhul Ma'ani - Aluusi, Tafsirul Qurdabi, Tafsiru Mafaatihul-Gaib...

Gurare 4 sunan Annabi Muhammad (S) ya zo kakara a Qur'anin Ƴan Shia: Aali Imran aya ta 144, Ahzab aya ta 40, Muhammad aya ta 2, Fathi aya ta 29.

Qur'anin 'yan Shia: littafi ne da Allah Ta'ala ya saukar wa Annabi Muhammad (S) wanda Allah Ta'ala yayi alƙawarin karewa daga canzawa ko jirkitawa.

Yarda da cewa akwai wani Qur'ani daban da Qur'anin da Allah Ta'ala ya saukarwa Annabi Muhammad (S) tamkar ƙaryata ayoyin da suka tabbatar da cewa ba wanda ya isa ya iya ƙirƙirar wani littafi irin Qur'ani:

Tabbas ayoyin Qur'ani sun tabbatar mana da cewa ba zai yiwu a canza Qur'ani ko a kirkiri wani irinsa ba:

Allah Ta'ala a Suratul-Hijr Aya ta 9, yana cewa:

ﺇِﻧَّﺎ ﻧَﺤْﻦُ ﻧَﺰَّﻟْﻨَﺎ ﺍﻟﺬِّﻛْﺮ ﻭَﺇِﻧَّﺎ ﻟَﻪُ ﻟَﺤَﺎﻓِﻈُﻮﻥَ

"Tabbas mu muka saukar da Qur'ani sannan tabbas mu ne zamu kareshi.."

A wannan ayar Allah yana tabbatar mana da cewa ba wani dan Adam da zai iya kara wani abu a cikin Qur'ani, saboda Allah yayi alƙawalin kare Qur'ani.

A wata ayar Allah Ta'ala yana cewa:

ﻟَّﺎ ﻳَﺄْﺗِﻴﻪِ ﺍﻟْﺒَﺎﻃِﻞُ ﻣِﻦ ﺑَﻴْﻦِ ﻳَﺪَﻳْﻪِ ﻭَﻟَﺎ ﻣِﻦْ ﺧَﻠْﻔِﻪِ ۖ ﺗَﻨﺰِﻳﻞٌ ﻣِّﻦْ ﺣَﻜِﻴﻢٍ ﺣَﻤِﻴﺪٍ .

"Barna (canji) ba ya zowa masa (Qur'ani)...."

(41 / ﻓﺼﻠﺖ 42/ ).

Wannan ayar ta ƙara tabbatar mana da cewa babu yadda wani zai iya jirkita Qur'ani ta hanyar kari ko ragi.

A wata Ayar Allah Ta'ala yana cewa:

"ﻭﺍﻥ ﻛﻨﺘﻢ ﻓﻲ ﺭﻳﺐ ﻣﻤﺎ ﻧﺰﻟﻨﺎ ﻋﻠﻰ ﻋﺒﺪﻧﺎ ﻓﺄﺗﻮﺍﺑﺴﻮﺭﺓ ﻣﻦ ﻣﺜﻠﻪ"

‏( ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ / ٢٣ )

"In kuna shakka akan abinda muka saukarwa bawanmu (Annabi (saw) (Qur'an) to ku zo da wata sura misalin tasa (Qur'ani) 

Da Allah Ta'ala yayiwa Kafirai wannan kulen suka kasa, sai Allah Ta'ala yace;

"ﻗﻞ ﻟﺌﻦ ﺍﺟﺘﻤﻌﺖ ﺍﻻﻧﺲ ﻭﺍﻟﺠﻦ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﻳﺄﺗﻮﺍ ﺑﻤﺜﻞ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﻻ ﻳﺄﺗﻮﻥ ﺑﻤﺜﻠﻪ ﻭﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﻟﺒﻌﺾ ﻇﻬﻴﺮﺍ "

‏(ﺍﻹﺳﺮﺍﺀ : 88).

"Ka gaya musu; lallai da Mutane da Aljannu za su haɗu don su kawo irin wannan Qur'anin ba zasu iya kawo irinsa ba; duk taimakekeniyar da zasu yi a tsakaninsu".

A Waɗannan Ayoyin da  Wasu Masu Yawa  A Qur'ani Allah Ta'ala Ya Tabbatar Da Cewa Babu Wanda Ya Isa (Mutum Ko Al-jani) Ya Kawo Sura Ko Aya Daya Tal Irinta Qur'ani. 

A shia, duk wani hadisi da ya saɓawa ayar Qur'ani; to ba zancen Annabi Muhammad (saw) da Imaman Ahlul-bayt (as) bane ba, ba zai yiwu maganar Allah Ta'ala da ta Annabi (S) suyi karo ba. Don haka, duk wata ruwaya da tazo a littafan Shia ko Ahlus-Sunnah game da canzawa ko rashin cikar Qur'ani ɓatacciya ce (bata inganta ba).

Ma'asumah Nigeria News Update
Ishaq Muh'd Suleiman 
08132933333 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post