Kashi na (2)daga fudiyya maraba

*KASHI NA (2) DAGA FUDIYYAH MARABA ABUJA*
🇳🇬MA,ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE🇳🇬
✍BY SHARHABIL USMAN PANDOSS
Cigaba Da Taron
Makon Hadinaki Na Yan Uwa Musulmi a Abuja Ranar Farko.
An shiga zango na biyu a rana ta farko da fara gabatar da taron shekara shekara na hadinkan yan uwa Musulmi a Abuja, wanda Harka Islamiyya Karkashin Jagoranci Sayyid Zakzaky ta saba shiryawa, bayan gabatar da sallar magrib da Insh'ai, anci gaba da taron makon hadin kan yan uwa Musulmi.
Yanzu mawaka ne ke rera wakokin yabon Manzon Allah (S) kafin mai jawabi na gaba ya fara a muhallin Fudiyya Maraba Abuja, ancika an batse wuri yayi wuri masoya Manzon Allah anhadu don murna da zuwar Annabi Muhammad (S).
Kai Tsaye Daga Fudiyya Maraba Abuja. 09/11/2019

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post