🇳🇬MA,ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE🇳🇬
✍BY SHARHABIL USMAN PANDOSS
Yadda Taron Makon Hadin Kan Musulmi Rana Ta Farko Ya Fara Gudana A Fudiya Maraba Abuja.
Bayan an bude taro da addu'a da kuma karatun Al'qur'ani mai girma, wakokin yabon Annabi (S) daga mawakan harka ya gudana, daga bisani kuma sai aka gabatar da mai jawabi.
Malam Ibrahim Gwantu shine wanda ya fara gabatar da jawabi a wurin taron na makon hadin kan yan uwa Musulmi na bana, wanda zai gudana tsawon kwanaki 5 a Abuja, yaune Ranar farko, yan haka anshiga salla da cin abinci, daga bisani zaa dawo fili don cigaba da gudanar da wannan taron.
09/10/2019
Tags:
Munasabobi



