ILIMI YA FI GIRMA DA TARIN SHEKARU
Cigaba:-
(2)- Bayahude yace; " To, ai ga Annabi Nuhu (A.S) ya haqurae d cutarwa da muzgunawa."
Sai Imam Ali (A.S) yace;
" EH HAKANE ! TO, AMMA HAQURIN ANNABI (S.A W.W) GUN ISAR DA SAQON ALLAH YA FI HAKA, DOMIN MUTANENSA SUN QUNTATA MASA, SUN QARYATA SHI, SUN KORE SHI KUMA SUN JEFE SHI. ABU LAHABI HAR MAHAIFAR RAQUMA YA JEFA MASA A KANSA, AMMA DUK YA HAQURA HAR SAI DA ALLAH YA TURO JIBRILU YA TAMBAYI ANNABI YA BA SHI IZNI YA CICCIBI DUTSE YA MIRGINA SHI A KANSU YA HALAKAR DA SU. AMMA ANNABI (S.A W.W) YACE;
" AI AN AIKO NI NE DON NA ZAMA RAHMA GA MUTANE. UBANGIJI KA SHIRYI AL'UMMATA, DON BA SU SANI BANE."
(3)- Bayahude ya qara cewa, " Allah (T) ya fidda Taguwa ga Annabi Salihu don ta zama aya ga jama'arsa."
Sai Imam Ali (A.S) yace;
" AN BAWA ANNABI MUHAMMAD (S.A.W.W) FIYE DA HAKA. ITA DAI TAGUWAR SALIHU BA TAYI MAGANA DA ANNABI SALIHU BA, KUMA BA TA TABA CEWA SHI ANNABI BANE. AMMA ANNABI MUHAMMAD (S.A.W.W) WATA RANA MUN JE DA SHI WANI YAQI SAI GA WANI RAQUMI YA YI MAGANA DA IKON ALLAH YACE;
" YAA MANZON ALLAH, WANI YA CI MORIYATA, GA SHI NA TSUFA SANNAN KUMA YANZU SO YAKE YA YANKA NI, DON HAKA NA ZO GUNKA INA NEMAN KARIYA."
SAI ANNABI (S.A.W.W) YA NEMI FABSARSA YA FANSA, SAI ANNABI (S.A.W.W) YA SAKE SHI."
Za mu cigaba insha Allah.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
~ 7th November, 2019.
Tags:
Taskar ilimi
