Ba fushin Allah ga mutum ne ka sawa kaga yana cutuwa ko ya fada cikin musifa ba. 'Dabi'a ce ta Allah barin azzalumai su cutar da bayinsa salihai ta yadda har sai wasun su sun qosa wajen ganin jinkirin samun sauqi daga Allah.
Mutanen Annabi Isah (A.S) sun kai yadda har zarto ake sanyawa a tsakiyar kansu a raba su gida biyu, amma fa hakan bai sa sun canza ko juya baya daga abinda suke kai ba.
Sannan kuma wannan abu rubutacce ne daga Allah cewa za a cutar dasu ('yan shi'ah), ba wai haka kawai abin ke faruwa ba, a'a, da sanin Allah, kuma komai na da lokaci.
Allah (T) na cewa;
" BABU WATA MUSIFA DA ZA TA AUKU A CIKIN QASA (ta jarrabawa) ko a cikin rayukanku (ta hanyar karkashe ku) FACE (tuntuni) TANA NAN (rubuce) CIKIN LITTAFI A GABANIN MU HALITTA TA (na faruwar abinda ke faruwa a kanku), LALLE WANNAN GA ALLAH MAI SAUQI NE.
(Allah na yin haka nr) DOMIN KADA KUYI BAQIN CIKI KAN ABINDA YA KUBUCE MUKU (na 'yanci, lafiya da kuma rayuwa ta walwala), KUMA KADA (ku azzalumai, fajirai, fasiqai) KUYI MURNAR ALFAHARI DA ABINDA YA BA KU (na mulki da makaman da kuke kashe bayinsa). KUMA ALLAH BA YA SON DUKKAN MAI TAQAMA (da mulki) MAI ALFAHARI (da makaman zalunci) ."
(HADID, AYA TA 22-23)
Saboda haka, wannan abinda ku kaga ana yiwa 'yan Shi'ah shine hanyar daukakarsu duniya da lahira.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
~ 20th October, 2019
Tags:
Taskar ilimi