–Bilal Nasir Umar Sakkwato
“Ina mana kira da babbar murya akan cewa ƴan uwa mu haɗa kai, Allah (T) ne kaɗai ya san fa'idar haɗin kammu kuma shi ne kaɗai yasan musibar da take tattare da rabuwarmu, saboda haka dole ne mu yi haƙuri da juna, domin a gudu tare a tsira tare. Ya haɗinkai yake a Harka ? Amsa, shi ne, kada ka yarda da cewa shaksiyarka ta zamanto ita ce damuwarka da har zai kasance ka yi faɗa da wani, Malam (H) yana cewa, “idan wani mutum ya yi maka ba daidai ba, kaima sai ka biye masa ka rama, to ya zama malaminka kenan” ya yi mugunta kaima ka yi masa, ya yi rashin haƙuri kaima ka yi rashin haƙuri, wannan bai kamata ba, abin da yake shi ne ɗan uwa ya kasance mai haƙuri yayin da wani ya cutar dashi.”
“Babu wani haɗinkai a inda aka taɓa shaksiyar Muhammadurrasulullahi (S), ga Sahabbai ga Manzon Allah (S), sai wani ya taɓa mutunci Manzon Allah, to anan kam babu zancen haɗinkai, ba a haɗa inuwa balle haɗinkai da wanda zai soki Annabi (S). Haka kuma a ɓangaren mai kira zuwa ga shiriya, haka akan tafiyarnan ta Malam (H), babu zancen haɗinkai da duk wanda zai fito ya ci mutuncin Malam (H), abin da Malam (H) ya ɗora mu akai, to a kan shi ne ake tafiya, ba a kaucewa, Sayyid (H) ya ɗora mu akan cewa duk wanda aka kashe a tafarkin Allah Shahidi ne, to idan wani ya zo ya ce da mu ana kashe mutane a banza, to a wannan fahimta ta wannan mutumen ba gurin da za a yi haƙuri bane, sai dai ma ka yi ƙoƙari ka lurar dashi akan ya dawo akan hanya.”
“Duk wanda ƙoƙarinsa shi ne ya cire son Shahada a zukatan ƴan uwa, to yana ƙoƙarin rusa wannan Harkar ne, kuma ba zancen yin shiru ga masu ƙoƙarin taɓa fikirar wannan Harka, sam ba a kyalewa, Malam (H) ya ce a yi kaza, sai wani ya ce ai ba dole sai an yi ba, a wannan gaɓar take za a gyara ne idan ba haka ba kuma sai kowa ya kama gabansa, shiyasa ka ga, ƴan Zuhudu suka zo suka tafi, ƴan Tawayiya suka zo suka tafi, ƴan Taƙalidi suka tafi, haka wannan tafiyar take, sai dai mutum ya tafi, amma fikirar Malam (H) ita ce kaɗai ba a tambayar ya aka yi aka yi kaza da kaza, idan aka ce Malam (H) ya ce, to zance ya ƙare, mu ƴan Malam ne, saboda haka wannan jagora mai girma kuma shi ne mujaddadi, kiransa ne muka amsa, to abin da ya kamace mu shi ne mu yawaita jin jawaban Malam (H) don kada guguwa ta je ta ɗebi mutum a banza.”
“Mu tashi tsaye mu cigaba da aiki domin cigabantar da wannan Harka, mu tsayu akan fikirar Jagora, kada mu yarda da duk abin da zai taɓa fikirar jagora, a Harkarnan dole ne a bada rayuwa, a Harkarnan dole ne a sami Shahidai, a Harkarnan dole ne a samu kamu ɗauri da kisa, cire wannan a Harka rusa ta ne, dole ne mu yi addu'a mu kuma fito mu bada rayukanmu, Shahidai yanzu aka fara ɗiba, ba mu da wannan labarin cewa, a jamhuriyar Musulunci ta Iran, an taɓa wayuwar garin da aka sami Shahidi dubu shabiyar a rana ɗaya. Karsashi na kawo sauyi dole ne ya tabbata a cikin zukatanmu.”
Tags:
Tunatarwa