Muhimmiyya Huduba Daga Bakin Ali Ameerul mu'mineen ( as)




⇀Ameerul Mu'mineen Ali (As) yake fadi a wata Khuduba tashi, abinda da na fi tsoro muku sune abubuwa guda biyu: Aiki don bukatunku da tsawaita buri.

⇀Aiki domin bukatu, yakan kangare mutum daga gaskiya. Tsawaita buri kuma kan saka mutum ya manta akwai wata rayuwa a gaba.

⇀Ya kamata ku sani duniyar nan tana tafiya da sauri-sauri, kuma babu abinda zai saura na daga cikinta, sai wani kwallin abu kamar hanyar jini da wani ya maida shi fanko (babu jini a ciki).

⇀Muyi hattara, rayuwa ta gaba kullum gabato wa take garemu. Kuma dukkan daya daga cikin rayuwoyin nan tana da 'ya'ya (Mabiya).

⇀Ya kamata ka zama dan wancen duniyar ne ba dan wannan duniyar ba. Sabida a ranar sakamako kowan ne da zai makale wa uwa tasa ne.

⇀Yanzu lokacin aiki ne, gobe kuma lokacin kididdige ayyuka. Kuma in ranar tazo babu damar koma wa  baya kace zaka cenja domin aikata aikin alkairi.

⇀Ya yan uwana karfa mu sha'afa, yanzu ne muke da damar cenja munanan ayyukanmu, mu musanya su da kyawawa domin tsira daga azabar Allah. Kar sai lokaci ya kure mu zam cikin masu cewa; In ama-inama.. alhali lokacin komi yazo karshe.

⇀Allah ya tabbatar damu, ya bamu ikon aiki tukuru domin samun tsira gobe kiyama.

      ⇀ʘBιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυʘ↼

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post