HAQQI NE DA YA HAU KAN KOWANNE UBA
Kamar yadda iyaye ke da haqqoqi kan 'ya'yayensu haka ma 'ya'ya ke da haqqi kan mahaifansu, duk wanda bai sauke haqqin da ya hau kansa ba, to Allah zai tuhume shi.
Annabi Luqman (A.S) ya yi gargadi ga dansa (BASAR) kan abubuwa masu girma guda tara (9), ga su kamar haka:-
(1)- SHIRKA
(2)- SALLAH
(3)- UMARNI DA KYAKKYAWA
(4)- HANI GA MUMMUNA
(5)- HAQURI
(6)- WALAQANTA MUTANE
(7)- GIRMAN KAI
(8)- YADDA AKE YIN TAFIYA
(9)- LADABIN MAGANA
Wannan gargadi nasa ya zo ne cikin littafin Allah mai tsarki cikin surar da aka yi mata laqabi da sunansa (LUQMAN), inda yake cewa ;
" YAA QARAMIN 'DANA! KADA KAYI SHIRKA GANE DA ALLAH, LALLE SHIRKA WANI ZALUNCI NE MAI GIRMA." (13)
" YAA QARAMIN 'DANA! LALLE ITA (shirka) IDAN TA KASANCE GWARGWADON QWAYAR KOMAYYA CE (saboda qanqanta) , KUMA TA KASANCE CIKIN DUTSE, KO KUMA A CIKIN SAMMAI KO CIKIN QASA, ALLAH ZAI KAWO TA. LALLE ALLAH MAI TAUSAYI NE MASANI." (16)
" YAA QARAMIN 'DANA ! KA TSAIDA SALLA, KUMA KA YI UMARNI DA ABINDA AKA SANI, KUMA KA YI HANI GAME DA ABIN QI, KUMA KAYI HAQURI AKAN ABINDA YA SAME KA (na jarrabawa). LALLE WANCAN NA DAGA AL'AMRA MASU GIRMA." (17)
" KUMA KADA KA KARKATAR DA KANKA (don girman kai) GA MUTANE, KUMA KADA KA YI TAFIYA A CIKIN QASA KANA MAIE NUNA FADIN RAI (proud). LALLE ALLAH BA YA SON DUKKAN MAI TAQAMA MAI ALFAHARI." (18)
" KUMA KA TAQAITA A TAFIYARKA (moderate), KUMA KA RUNTSE GA SAUTIKA (yayin magana). LALLE MAFI MUNIN SAUTUKA (Voices) SHINE SAUTUKAN JAKUNA." (19)
Ishara ga dukkan mai hankali.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
~ 10th November, 2019.
Tags:
Tunatarwa
