Inji Jagora Sayyid Zakzaky (H) a inda yake cewa:
"Tsoron wa muke ji? Bindiga? Ta yi kadan! Ai an sha gwada mana ita. Har kwaraf, kwararaf a ja da nufin a harba an yi ya fi a kirga.
![]() |
Shaikh Ibraheem Zakzaky |
"Kuma ba muna yi ne don mutane su bi mu ba. Wanda duk ya saurari wa'azinmu in ya dauka mai yi yana yi ne don a bi shi, don Allah don Annabi kar ya bi ni! Cewa nake, a bi Allah, a bi Manzo. In yabi Allah ya bi Manzo toh Alhamdulillah dama Allah ya dora min na bi Allah da Manzo ya kuma dora mishi, ni kuma ina tunatarwa ne. Illa iyaka. Saboda haka ba bukatar har in boye wani abu wai don mutane su bi ni, kar ma a bi. In dai ka wa'azutu Alhamdulillah.
"Wajibi ne da ya hau kawukanmu, mun wayi gari muna Musulmi amma ba Musulunci ke iko da mu ba. Kuma Allah zai tambayemu gobe Kiyama. Kuma in da akwai wata mafita da wani zai gaya min, yace ba komai zauna kawai ko ba a addini. Kai dai mangare dan uwanka Musulmi kawai, Shine mafita. Da zai kawo min hujja na yarda da sai mu bi irin nashi.
"Amma na san ina jin tsoro gobe Kiyama in na tsaya gaban Allah (T), yace min, "Me yasa ka shantake a Nijeriya alhali ka san ba dokar Allah take bi ba? Me yasa ka zauna a Nijeriya alhali ba da shari'ar Musulunci ake yi ba?" Ina jin tsoro, ban san abin da zan cewa Allah ba.
"Saboda haka ya zama wajibi na na ga cewa lallai gwargwado ni na barrantar da kaina. Saboda haka ma ban yi wata - wata ba, da taimakon Allah da BaiwarSa da ya min, na mike, na ayyana, nace;
Kunga ku wadannan mutane da kuke kiran kawukanku Shuwagabanni, to Dawagitai kuke! Ni kam ba shuwagabannina kuke ba! Kunga abin nan da kuke ce masa Kwansutushen ko tsarin mulki, to ban yarda da shi ba! Kunga dokoki da ka'idojinku da kuke dorawa sabanin na Allah, na ki na bi! In kuna da Jahannama ku saka ni. Jahannamar Allah (T) nake tsoro. In kuma wani abu ne za ku bani in lasa wai sai na abin nan, to ba ku da wani abu da za ku bani. Akwai abin da nake bukatar a bani in taba sosai, Aljanna nake so. Na san kuwa ba wani Dagutun da ke da ita. In kuma yana da Aljanna a Duniyar nan bani bukata. Ya rike kayansa. Amma in yana da Jahannama a Duniyar nan ya saka ni, don na san Jahannamarsa za ta kare.
"Wannan ba wani boye - boye. In har ban boye wannan ba to me kuma zan boye? Abin da muke bayyanawa shi ke cikin zuciyarmu da zahirinmu da badininmu abu guda ne. *Mun ki yarda wani abu ya yi iko da mu in ba addinin Musulunci ba. Mun ki yarda! Saboda haka muka ce kun gammu nan, mu 'Yan Tawaye ne ga duk wanda yace ba za a bi Allah ba. Shi da ya ma Allah da Manzo Tawaye har zai yi mamaki in mun masa tawaye, don yana da bindiga? Ya harba mana!!!"
— Shaikh Ibraheem Zakzaky a garin Jega, shekaru fiye da 20 da suka gabata.
Tags:
Jawaban Sheikh Zakzaky