Babbar magana: Masu garkuwa da mutane sun sace 'yan sanda a Ribas

Babbar magana: Masu garkuwa da mutane
sun sace 'yan sanda a Ribas

by Sharhabil usman pandoss

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace jami'an 'yan sanda guda biyu a garin Ngor, hedikwatar karamar hukumar Andoni a jihar Ribas.

 Dukkan jami'an 'yan sandan na aiki ne tare da hedikwatar rundunar 'yan sandan jihar Ribas, kuma an sace su ne ranar Litinin. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ribas, DSP Nnamdi Omoni, ya tabbatar da faruwar lamarin.

 Sai dai, har yaznu rundunar 'yan sandan jihar Ribas ba ta bayyana sunayen jami'anta da 'yan bindigar suka sace ba. DSP Omoni ya yi alkawarin fitar da jawabi a hukumance, nan bada dade wa ba. Za mu kawo karin bayani

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post