MENE NE DALILAN NEMAN TATTAUNAWA 'RUWA A JALLO' DA IRAN DA SAUDIYYA TAKE YI?
✍️
Muhammad Awwal Bauchi.
IRIB Hausa - Tehran, Iran.
12/10/2019
A yau, Asabar, ne ake sa ran firayi ministan kasar Pakistan, Imran Khan, zai iso Tehran, babban birnin kasar Iran, don gudanar da wata ziyarar aiki a kasar da nufin tattaunawa da jami’an kasar musamman kan alakar Iran da Saudiyya da hanyoyin da za a magance kai ruwa ranar da ke tsakanin kasashen biyu.
Kafin hakan dai jaridar New York Times ta Amurka ta jiyo jami’an kasashen Iraki da Pakistan suna cewa Yarima mai jiran gado na Saudiyyan, Muhammad Bin Salman, ya bukaci shugabannin kasashen na su da su taimaka masa wajen bude kofar tattaunawa da Iran don magance matsalolin da ke tsakanin kasashen biyu.
Kafin hakan ma dai firayi ministan Pakistan din, a taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, ya sanar da cewa Saudiyya ta bukace shi da ya taimaka mata wajen shiga tsakani don magance rikicinta da Iran.
Ko shakka babu wannan wani lamari ne abin maraba da shi, don ko ba komai idan har aka yi nasara za a rage irin rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta tsakiya da ci gaba da zubar da jinin da ke faruwa a can din.
To amma abin tambaya a nan shi ne mene ne dalilin da ya sanya Saudiyya neman tattaunawa da Iran a wannan lokacin alhali tun da jimawa Iran ta jima tana kiran Saudiyyan zuwa ga sulhu da tattaunawa don magance wadannan sabani da ke tsakaninsu amma Saudiyyan ta ki?
A ra’ayi na akwai wasu dalilan da suka sanya Saudiyyan neman tattaunawa da Iran ‘ruwa a jallo’ a halin yanzu da suka hada da:
1). Rashin nasara daya bayan daya da Saudiyya take fuskanta a yakinta da al’ummar Yemen musamman bayan harin da dakarun Yemen suka kai kan matatun manta guda biyu (na Abqaiq da Khurais) lamarin da ya sanya Saudiyya ci gaba da hasarar biliyoyin daloli a kowace rana da kuma harin baya-bayan nan na Najran da dakarun Yemen din suka kai da kuma nasarar kame dubban sojojin Saudiyya da kawayenta a matsayin fursunonin yaki.
2). Juya bayan da Amurka ta yi wa Saudiyyan da kuma fitowa fili da shugaba Trump yayi na cewa Amurka dai ba a shirye take ta shiga yaki (da Iran) saboda Saudiyya ba, a bangare guda kuma ga gazawar da makaman Amurkan suka yi wajen kare Saudiyya daga wadannan hare-hare.
3). Tsaka mai wuyan da firayi ministan ‘Isra’ila’, Netanyahu, yake ciki sakamakon rashin nasara da ya fuskanta a zaben baya-bayan nan da aka yi a can, lamarin da watakila ma nan da dan wani lokaci zai iya samun kansa a tsare a gidan yari sakamakon zargin rashawa da cin hanci da ake masa, wanda da man mahukutan Saudiyya sun dogara sosai da shi wajen kaddamar da yakin da suke fatan gani a kan Iran.
4). ‘Mummunar’ makoma da ke jiran Saudiyyan wanda wasu daga cikin masu fadi a ji da kuma ‘ya’yan gidan sarautar kasar suka fara hangowa sakamakon abin da wasu suka kira ‘siyasar rashin mafadi’ da yarima mai jiran gadon kasar yake gudanarwa da ya ke ci gaba da sanya kasar cikin hatsari da tsaka mai wuya.
5). A bangare guda kuma nasarar da Iran take ci gaba da samu wajen magance matsalar takunkumin da Amurka ta sanya mata ta yadda a halin yanzu duk da takunkumin amma tana iya sayar da wani bangare na man fetur dinta da aka ce ya kai sama da ganga miliyan guda a kowace rana sakamakon yadda China ta yi kunnen uwar shegu da batun takunkumin tana sayen mai din Iran da aka ce ya kai ganga dubu 500 a kowace rana, Turkiya ta sanar da cewa ita ma za ta yi watsi da takunkumin Amurka wajen sayen man Iran, haka nan ga kasar Iraki ta zamanto wata hanya ta fitar da man Iran, ga kasar Siriya ma wacce take sayen man Iran sannan kuma ga nasarar da aka samu na bude mashigar Bu Kalam na kasar Siriya wanda hakan ya kara bude hanyar fita da kayayyakin Iran. Haka nan kuma a daidai lokacin da Saudiyya da wasu kasashen larabawa suke ci gaba da kashe ‘yan’uwansu a Siriya da Libiya da Yemen, ita kuma Iran tana ci gaba da karfafa kanta wajen kera makaman kariya da ya sanya ta a halin yanzu dai tana nema ta zama ‘gagara badau’ in ma ba ta zama din ba kenan a yankin.
Dukkanin wadannan suna daga cikin abubuwan da suka tilasta wa Saudiyya neman zama teburin tattaunawa da Iran don nema wa kanta mafita daga wannan ‘tsaka mai wuyan’ da take ciki.
Fatanmu dai a kullum shi ne samun nasarar irin wadannan tattaunawa don a samun dawwamammen sulhu da zaman lafiya a kasashen musulmi da kawo karshen zubar da jinin bil’adama da ake yi.