- Jagororin Kabilar Ibo sun dage a kan batun samun mulkin kasa a 2023
- Shugabannin Yankin sun fara kokarin hada-kai domin cin ma nasara - Ana kokarin jawo duka Attajirai da Sarakuna da ‘Yan siyasar Yankin Mun samu rahoto daga Jaridar The Telegraph cewa mutanen Kudu maso Gabas sun fara harin mulkin Najeriya a shekarar 2023 gadan-gadan inda su ke ta shirya taro iri-iri domin su kai labari. Manyan ‘yan boko da ‘yan siyasa da kuma Attajirai da ‘ya kasuwa da Sarakunan gargajiyan yankin su na halartar wannan taro da ake yi a gidan wani tsohon gwamna kamar yadda mu ka ji.
Yunkurin da ake yi shi ne ayi watsi da duk wani banbancin siyasa a ba Inyamuri tuta a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 kamar yadda PDP da AD su ka tsaida Yarbawa a 1999.
Wani ‘dan majalisar yankin, Honarabul Benjamin Kalu ya bayyana cewa da gaske su ke harin shugaban kasa a 2023. ‘Dan majalisar tarayyar ya ce ya kamata a ba kowace kabila damar mulki. An rahoto Kalu ya na cewa: “Mun fi karfi idan mu ka hada kai idan har mu na so mu karbi kujerar farko a kasar.” Dan majalisar yace za a fi samun zaman lafiya idan kowane yanki ya yi mulki.
Jita-jitar da ke yawo shi ne wani Mai kudi a shiyyar Kudu maso Gabashin kasar zai saki makudan kudi saboda ganin mulkin Najeriya ya koma hannun Ibo, abin da ba a taba yi ba a farar hula.
by Muhammad Malumfashi
Madogara legit.hausa.com
Tags:
Labaran Duniya