DA HANKALI DA ILIMI SHEIKH ZAKZAKY YA KIRA MU ZUWA GA ADDINI
Ma'asumah Nigeria News Update
Da Hankali, Ilmi, sanin ya kamata da girmama
al'umma aka gina wannan da'awan. Duk wanda kagani a wannan tafiyan ta su Sayyid
Zakzaky (H) to waɗannan ababen ya Kawo shi, koda ko a cikin tafiyan aka haifeka, to ka tashi kaga iyayenka tattare da waɗancan abu bawan da na zaiyana.
To mai yasa a yanzu muke ƙoƙarin kawo wasu irin halayan da bamu sansu a wannan tafiyan ba? Sam taurin kai da rashin kunya bai taba zama acikin wannan tafiya ba. Zakaga Ƴan Uwa anzo wajan Muzahara amma
wasu sai kaga hanƙoron su shine Yiwa jama'ar
gari ko kuma in an haɗu da Jahiliya tsawa da wasu zare zaren Idanuwa, kai kace sunzo yiwa jahiliya aiki ne, don su aka sani da wannan hali.
MISALI.
A lokacin wata Muzahara a garin da nake da
zama, sanda Jahiliya tazo tana shirin afkawa Ƴan Uwa, da zuwan su sai suka fara koran jama'a da Muzaharan ta tasamma wajan zaman su zata wuce, koda zuwan Yan sandan tayar da tarzoma, kawai sai suka dira akan jama'an gari da ihu, da zare musu Ido, wannan yasa su jama'a suka fara musu ihu da fadin kuje Sambisa mana. To kunga
anan shi ihu da zare idanu da fita cikin haiyaci
da wasu Yan uwa keyi bashine mafita garemu
ba, tunda ga mai Bindiga ma da yayi jama'a sun
kare da yi masa ihu da raddi.
A wata Muzahara da akayi nan kusa kusa a
Abuja Yan uwa lallai wasu sun fita hanyaci su
kuma lallai ana ɗaukan su a matsayin sunzo wa
jahiliya aikine.
Ya kai Ɗan uwa mai daraja kayi kokari ka riƙa
tsayar da kanka a bisa lizamin da kasan su
Sayyid (H) sun gina harkannan dashi.
Hankali, Ilmi, sanin ya kamata da girmama
al'umma.
Kai mai da'awa ne, so kake kowa da kowa ya
fahimce ka, yazo yayi abun da kakeyi, ba faɗa
dashi ba.
A wani mafarki da wani Dan uwa ya tabayi dasu
Sayyid a inda ake tsare dasu a yanzu, duk da
baifa taba zuwa ba. Amma yayi mafarki dasu
Sayyid da inda suke kai harda jahiliyan dake
gadin inda su Sayyid suke sai da ya gansu a
mafarkin.
Yace Waɗanda suke gadin ranan da za'a
canza su tazo, basu son a canzasu, saboda irin
kyakkyawan mu'amalan da mai wannan da'awan
yake da ita harga jami'an Tsaro.
Amma abun takaici Gabana wani Ɗan Uwa an tashi Muzahara a Abuja muna tahowa zamu hau mota mu koma Masauki Sega Wani Bawan Allah bakin Titi Galadima Junction yanata Zagi wai ana Zagin Matan Annabi da Sahabbai waye waye yana aibata mu, se wani Ɗan Uwa daga Suleja yake masa magana ta hankali cewa abun duk ba haka bane, kamar ya ɗauki maganar yace ayi haƙuri be san abun haka yake ba, se gashi gobe ma mun sake samunsa nan wajen yanata faman zage zage, nan take wani Ɗan Uwa ya ɗauko dutse wai zai fasa masa kai, seda muka hanashi,
To a takaice dai abun ba zafin kai bane, Hankali, Ilimi, Sanin Ya kamata, da Girmama Jama'a ne.
Ma'asumah Nigeria News Update
Ishaq Muh'd Suleiman
08132933333
Tags:
Game damu