Mun ji cewa kungiyar nan ta Action Aide Nigeria watau AAN ta yi kira da cewa ayi maza a rage yawan abin da ‘yan majalisun kasar nan su ke tashi da shi a matsayin albashi da alawus a ofis.
Wannan kungiya mai zaman kanta ta na so a rage adadin abin da gwamnati ta ke kashewa a kan masu mulki wadanda su ka hada da ‘yan majalisu da duk wasu masu rike da babban ofis a kasar.
AAN ta ce wannan zai sa a adana kudin da za ayi wa Najeriya ayyukan gina kasa da more rayuwa. Kungiyar ta bayyana wannan ne bayan taron da ta shirya a Ranar Lahadi, 27 ga Oktoba, 2019. Shugabaar majalisar amintattu watau BOT na wannan kungiya, Dr. Jummai Umar-Ajijola, ita ce ta yi magana a madadin kungiyar a karshen zaman da su ka yi domin duba halin da kasa ta ke ciki. Jummai Umar-Ajijola ta bukaci gwamnatin kasar ta yi gaggawan rage yawan ma’aikatu da hukumominta. A cewar ta, hakan ya zama dole ganin irin kalubalen da ke tattare kasafin kudi.
Tags:
Labaran Duniya