✍️ Musa Ibrahim Daura
3-9-2019.
Babbar matsalar masu ba shugaban kasa shawara musamman abin da yashafi halin da kasa take ciki ta fannin tattalin arziki, a Abuja suke zaune, suci su sha ba tare da wata wahala ba.
Amma da ace shugaban kasa zai hada wani zama na sauraren halin da yan' kasa suke ciki yaji daga bakin mutane masu karamin karfi, ta hanyar daukar murya, shi kuma yanaji daga Inda yake wallahi BABA BUHARI DA SAI KAYI KUKA, DOMIN TSANANIN YAYI TSANANI.
A magana ta gaskiya tun shigowar gwamnatin nan ake fama da matsin rayuwa, to amma ganin cewa jagoranta mutumin kirki ne mai kishin kasa da al'umma, wannan tasa mutane sukayi hakuri da kyakkyawan fatan samun sauki. To amma ina! Abubuwa kullum sai gaba suke, ga lokaci na tafiya, har ta kai mutane masu raunin zuciya sun fara yanke kauna da samun sauki a wannan gwamnati da sukayi fafutukar kafawa.
WALLAHI, duk Wanda yace babu tsananin rayuwa a wannan lokacin son zuciyar sa ne kawai yafadi, matukar mutum yana da imani yana kuma shiga cikin al'umma yasan ana shan yar'tselen uwar wuya. Amma kuma wannan bayana nufin babu inda akayi nasara ba, akwai gurare da dama inda za'ace Sam barka. Illa iyaka dai matsin tattalin arzikin ne yakai TSANANI.
Yan kasuwa masu manyan jari sun rikito kasa, masu matsakaitan jarin sun durkusa, masu kana nan jari miliyan biyar zuwa daya sun cinye jarinsu, ba'a maganar masu dubu daruruwa, domin sun koma leburori. Kowa nafsi nafsi yake, saidai kalilan.
Shiko talakka Dan kwadago mai futa kullum ya samo, ya zama mabaraci domin baya iya samun abin da zaikai bakinsa sai yayi bara. Wannan shine halin da kasar nan take ciki a halin yanzu ko dai shugaban kasa yasani ko kuma bai sani ba.
Kudinmu sun lalace basu da daraja ko kadan yanzu zaka canza naira dubu wallahi yanzu zata kare kuma ba tare da kayi wani abin azo a gani ba, alhali kuma samun naira dubun abune mai wahalar gaske. Duk Wanda ke kasar nan yasan haka, SHIYASA NACE TSANANIN YAYI TSANANI.
Na kasance daya daga masoya wannan gwamnati na hakika Wanda banason a ga gazawarta, kullum bukatar mu ayi nasara, BUHARI yaba marada kunya, amma ganin yadda lamura ke tafiya yasa dole mu ja hankalin gwamnati wala'alla ko an samu canji tunda har yanzu da sauran lokaci.
Mutum zai sha mamaki idan yaje asibiti ko wajansa sayen magani, inda zakaga anba mutum katin magani amma ya zabi wasu yace abashi abar wasu, ko kuma kaga yadda magidanta ke fafutukar samun abin da za'a karya da safe alhali gari ya waye, mutum da iyali amma baisan yadda zasu karya da safe ba, ga kudin ruwa, gana itace, gana nika ga na kayan miya ga Wanda ya samu abin dafawar kenan. Wasu kuma wallahi sau daya sukecin abinci a rana, wani zai aurar da diyarsa baisan yadda zaiyi ba, wani matarsa zata haihu baya da sisin kwabo, kai abubuwa gasu nan barkatai, Idan aka zauna hira zakaga mutum yayi shiru shi kadai yana lissafin da babu samu a cikinsa.
Don haka a zance na gaskiya tattalin arzikinmu yana cikin mawuyacin hali, gaya kuma kusan duk wani tsari da gwamnati takawo na inganta tattalin arzikin sai an samu yan zagon kasa sun lalata shi, ta yadda bazai amfani al'umma ba, kamar HARKAR NOMA, HARKAR CIYAR DA YAN MAKARANTA, TALLAFAWA MASU SANA'OI, Duk an cuda karya da gaskiya shiyasa abin bayayin tasirin da za'a gani. Dama yanzu batun samun aiki sai mai uwa a gindin murhu.
Dawannan nake kira ga shugaban kasa matukar zai samu irin wannan bayanin nawa yayi kokarin ganin ya amfani sauran lokacinsa wajan sauya akalar tattalin arzikin kasar nan cikin gaggawa ta yadda mutane zasu gamsu cewa lallai kai MAI KAUNAR TALAKKA NE KUMA MAI SON RAYUWARSA TA INGANTA, amma matukar aka tafi a haka har karshe to zaiyi wuya WASU TALAKKAWAN SU YARDA BUHARI MAI KAUNAR SU NE, kuma a haka za'a lalata duk wani dazai yunkuro da siffa irin ta BUHARI.
Tags:
Daga marubata
