TSUFAN NAJERIYA A SHEKARA HAMSIN DA TARA AMMA BA HANKALI.

✍️
Musa Ibrahim Daura
2-10-2019,


A addinance ko a al'adance daga shekara sha takwas mutum ya balaga, ana sa ran zai fara shiga hankalinsa, bare kuma ace yakai shekara arba'in to daga wannan lokacin yagama kammala hankalinsa. Idan kuma yakai shekara sittin yazama dattijo mai fada da cikawa abin girmamawa abin koyi ga al'umma. Saidai ana iya samun akasin haka idan rayuwa tayi gardama.

A jiyane najeriya ta cika shekara hamsin da Tara da samun yan'cin kai, daga turawan ingilishi, a bisa al'ada duk shekara ana tunawa da irin wannan rana ta samun yanci. A baya har bukukuwa ake gudanarwa a fadin kasar baki daya dayin fareti da kuma wasanni don nuna murna.

Tabbas! Kakaninmu da iyayenmu sunyi matukar kokari domin ganin sun sama mana yan'ci daga turawan mulkin mallaka ta yadda zamuci moriyar arzikin da Allah ya horewa kasar mu, Allahu Akbar Allah jikan su SIR ABUBAKAR BALEWA, SIR AHMADU BELLO SARDAUNAN SOKOTO, MALAM AMINU KANO, MALAM SA'ADU ZUNGUR DA SAURANSU, YA KUMA SA A RIKA TUNAWA DA SU AWOLOWO, NMANDI AZIKWE, JOSEPH TARKA DA MAKAMANTANSU.

Yan'ci ya samu Bayan ansha fama da gwagwarmaya, samuwar yan'cin tasa  jin dadi da walwala tare da tunanin cewa rayuwa zata inganta, ta fannin ILIMI, LAFIYA, NOMA, KIWO, ZAMAN LAFIYA DA KUMA SAMUWAR ARZIKI. Haka wannan fata yasoma tabbatuwa abubuwa suka fara tafiya yadda aka tsarasu, MALAMAI SUNA AIKI KOYARWA DON KISHIN KASA A lokacin mutane so suke ace su malamai ne masu koyawa, saboda yadda ake kallon malanta a lokacin, wannan tasa ake ganin kimarsu tare da girmamasu fiye da kowa cikin al'umma, FANIN LAFIYA yana tafiya yadda akeso asibitoci suna aiki, ga kayan aiki ana fita aiki kan lokaci ana daratta marar LAFIYA, ana bada magani kyauta, ana kula da marar LAFIYA kamar kwai. Fanin NOMA yana tafiya yadda akeso gwamnati na taimakon manoma ta hanyar sayen kayan da suka Noma, haka kiwo anayinsa ta yadda har wasan nuna iya kiwo akeyi ga sarakuna da shugabanni, abin da ake kira da (wasan show) FANIN ZAMAN LAFIYA, Mutane suna zaune cikin aminci da kwanciyar hankali, babu wata fargaba, ko ina sai mutum ya ajiye kayansa, Idann kwana yakamaka a dokar daji sai kasamu waje ka kwanta babu darurar komai, a lokacin sarakuna suna taka rawa wajan kula da al'umma, shugabanni babu son zuciya a wajansu, ga kuma kishin al'ummarsu ta yadda basu kaunar abin da zai taba mutanen su.

Sannu a hankali wannan kyakkyawan fata yafara gushewa abubuwa suka fara tabarbarewa, yazamana najeriya tana girma tana kara Shiga daji, wato irin girman Dan SARKIN BAKA, maimakon ana girma ana kara hankali, amma sai yazamana ana girma ana RASHIN HANKALI.

Yau shekara hamsin da Tara da samun yan'cin NAJERIYA, amma abin takaici komai ya tabarbare mun koma rayuwa marar tsari, duk abubuwan da muka taso dasu na kishin kasa duk sun tarwatse, ILIMI, NOMA, LAFIYA, TSARO DA TATTALIN ARZIKI DUK SUN RUSHE, KUMA BABU ALAMAR NAJERIYA ZATAYI HANKALI A Matsayinta na DATTIJIWA MAI SHEKARA HAMSIN DA TARA.

Daga karshe ina fatan Allah yasa najeriya tayi karko irin na DABINO, wato karshen lamarinta yazama mai zaki. Amma fa hakan bazai yiwuba sai mun tashi da kanmu mun canza munsa kishin kasa a zukatanmu, kada mu dauka bikin zagayowar ranar yan'ci da murna zasu sa muci gaba.

Wannan shine sakona na ranar samun yan'ci ga NAJERIYA.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post