No title


CIKIN WATANNI 7 MAHARA SUN KASHE FIYE DA MATASA 60 A GARIN UDAWA DAKE JIHAR KADUNA.

🇳🇬MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE🇳🇬

Daga: sharhabi usman pandoss



Abin takaici da ban tausayi shine yadda marayu ke Kara yawaita a garin Udawa dake jihar kaduna sanadiyar kissan kiyashi da mahara keyi a garin da sauran kauyuka dake kewaye, wannan lamari yayi kamari sosai dukda gwamnati na iya kokari ganin an kawo karshen lamarin.



Maharan sun fara kisan ne tun shekaru uku da suka gabata inda suke tare hanya, bin kauyuka da Kuma Kai Hari Kai tsaye cikin gari sukashe rayukan al'umma, sace matan su da Kuma yaye dukiyar su.

Daga watan mayu na shekarar 2019 zuwa satumbar 2019 maharan sunkai hare-hare har sau hudu a lokuta daban-daban inda a cikin hare-haren sun kashe akalla mutane sittin ciki harda kwamandan Yar banga na yankin (MRG. Bala Commander) da sauran mutane Wanda harin ya ritsa dasu. sa shin direbobi Kuma an rasa akalla direbobi 17 daga watan junairun shekarar 2019 zuwa satumbar 2019 



Abin tausayi da gigitarwa shine yadda marayu ke Kara yawaita a kauyen ba masu kula dasu, karatun su ya lalace, tarbiyar su na sanyi sannan Babu wani Mai tanadar masu abinyi domin dogaro da kansu nan gaba. Baya ga haka ga Yan gudun hijira daga kauyuka duk sun cike kauyen Babu wurin zama, Babu isasshen abinci, Babu sana'ar yi haka dai suke zama abin tausayi Musamman mata da kananan yara.



Ya zama dole gwamnati ta Kara waiwayo wannan gari da agaji na tsaro da Kuma duba haryar bayarda ingattacciyar ilimi ga marayu da Kuma koya musu sana'oi domin dogaro da kansu.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post