ZAMAN JUYAYIN MAJALISUL AZAH NA(7)AGARIN MALUMFASHI

ZAMAN JUYAYIN MAJALISUL AZAH NA(7)AGARIN MALUMFASHI


Ban garen yan uwa maza

 Malam Abbas Muhammad Malumfashi kenan awajen zaman juyayin MAJALISUL azag

Wani bangare na yan uwa awaken zaman juyay

Zaman juyayin majjalisul azah zama na bakwai da ake cigaba da gudanarwa agarin malumfashi wanda malam abbas muhhammad malumshi ke ci gaba da gudanar wa a harabar makarantar fodiyyah k/kudu ga abinda shehin malamin ke cewa
zuwan shimru  ga kwamanda umar bn sa'ad,shimru yazo wajen umar bn sa'ad yakawo masa takarda yunqurin mugun nufinsu akan imam Husain bayan umar yakaranta takarda sai yace ma shimru cikin fushi yana fadin,meya sameka ya shimru kada allah yakusantaka da rahamarsa wallahi ina zaton kai kaba gwamna wannan shawarar kuma kabata mana lamarinmu kuma bazaka samu nasaraba

Sai shimru yace Ya umar idan bazaka iya aiwatar da abinda aka umurcekaba to kasauka kabani waje
Sae umar bn sa'ad yace  lallai baka da albarka domin kazo da mugun sako,amma bazan sauka daga wannan kujerarba nizanyi wannan aika aikar don haka shimru nabaka mukami kaine kwadan mayaka nakan dawaki

    Bayan sunyi shirin yakar imam awannan daren sai yatsaya dafda masaukin imam Husain yace ina yaran yar'uwarmu suke?
Yana nufin Abbas usman jafar da yan'uwansa,sai imam yace masu Ku amsa koda fasikine sai sukace mekake so kuma mekake nema awajenmu
Yace kusani cewa kuna cikin aminci kuma kada kukashe kanku tareda husain. Sai Abbas yace allah yawadaranka kana nufin zaka bamu kariya amma imam Husain bashida kariya tir dakai kana umurtarmu da mubar dan'uwanmu

Dayaji haka saiya koma sai umar yacema rundunar yazidu yaku rundunar allah kuhau dawakanku albishirinku da aljanna.
Ibn sa'ad ya isa wajen imam Husain saiya yamu imam azaune   rike da takobinsa har barci yadaukesa,anacikin haka saiga rundunar mahara kan hemarsa sai zainab aqila taje wajen imam tace sun kusantomu sai yace ya yar'uwata baga manzon allah acikin mafarkina mynanan xuwa garesa nan bada jimawaba

Bayannan saiga dan'uwansa Abbas shina yazo sai yake cewa ya dan'uwana husain gasunan sun iso sai imam yace ma Abbas hau doki katunkaresu kace meke  tafe daku kuma mikuke nufi damu,Abbas yahau doki atare dashi akwae mutane ashirin daga cikinsu akwai zuhair dasauransu

Bayan Abbas yatambayesu meke tafe dasu sai sukace umurnine daga amir kokubi umarnin komu gama daku,saiya Abbas yakoma yafadama imam,sai imam yace ka koma kafadamasu   idan zaiyiwu sukyalemu su bamu wannan daren domin muyi sallah domin allah yasani ni maison ibadane da karanta littafinsa inason inyi addua ga ubangijina

Daga Mudansir Bara'a Malumfashi
Da Khadija hamza

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post