SHAHADAR ABULFADAL ABBAS(AS)

SHAHADAR ABULFADAL ABBAS(AS)

MA'ASUMA NAGERIAN NEWS UFTADE




 Yarage afilin karbala abulfadal ne yarage ankashe dukkan sahabban imam Husain(as),ankashe jikokin manzon allah(s)maza dasuke tare da imam husain,yanzu abulfadal Abbas ne kadai yayi saura.
     Jariri da mata kawai kake change kwance akan sahara mai tsananin zafi suna kuka suna neman taimakon ruwa saboda tsananin kishin ruwa dake addabarsu,ihun yara da kukan mata ya gauraye sansanin imam Husain tako ina kaduba yarane da  mata keneman temako abasu ruwa susha kira Duke"ya Husain ruwa,ya abbanmu ruwa,atemakemu da ruwa musha!!!
      Hankalin imam husaini yatashi ya waiga kudu da arewa gabas da yamma baiga ruwa dazai basu sushaba,rundunar azzalumai mabiya yazidu(LA)sun kange ruwan sun hana jama'ar imam husaini diban ruwan susha,sai abulfadal ya durkusa gaban wansa imam Husain yanemi izinin yakar kafirannan,sai imam Husain yace masa;kafin kafita fagen fama kanemowa wadannan jaririran ruwa susha ko kadanne

Abulfadal yadauko abin dibar ruwa yazo wajen dakarun ibn sa'ad yayi masu wa'azi da nasiha amma sukace saidai duk su mutu da kishi bazasu ruwa sushaba
      Abulfadal yadawo bayateda yasamo ruwaba yana isowa sansanin da mata suka ganshi da abin diban ruwan sunyi zaton yakawo masu ruwane,sai sukayo kansa da gudu suna cewa;RUWA!RUWA!!RUWA!!!Da abulfadal yaga haka saiya juya da hanzari yahau dokinsa yatunkari kogin furat,yana isa saiyaga dakaru dubu hudu sun kewaye kogin, yarinka yaki dasu har saida yakashe mutun tamanin80 acikinsu yaisa bakin kogin ya dabo ruwa

    Bayan yaciki abin dibar ruwansa,yadiba zaisha saiya tuna irin kishin ruwan da imam Husain yake fama dashi,saiya fasa sha,yadauki jakar ruwan yahau dokinsa zaije yakaimasu ruwan saiyaga dinbin dakaru suntare hanya nantake suka kewashi tako ina,yasoma yaki dasu yana kashesu,can saiwani mai suna Azraq yasaremasa hannun dama,sai abulfadal yacafke jakar da hannun hagu,sai naufal yasare hannunsa na hagu,sai abulfadal yacafke jakar da hakoransa sai suka harbi jakar ruwan da kibiya jakar tayage sai ruwan ya rinks tsiyaya a kasa
     Kafin abulfadal yadago kai ya kalli inda imam Husain suke saiyaji sukar kibiya maidafi a kirjinsa nantake yafado daga kan dokinsa ya kwalla kira yace;ya Husain ka riskeni!!!
         Imam Husain yanajin sauti nadan'uwansa yataho aguje kamar walkiya yafada kan abulfadal ya tallafoshi yadaga yana cewa;yadan'uwana wayyo Abbas dina!wayyo masoyin raina!!
           Imam Husain yana kuka yasharema abulfadal kasar dake kansa,sai imam Husain yayi runkurin daukeshi yakaishi hema sai abul fadal yace masa;yadan'uwana don darajar kakanka manzon allah(s)karka daukeni  zuwa hema kabarni anan domin inajin kunyar diyarka sukainah,nayi mata alkawari zankawo mata ruwa amma abin ya gagareni sai imam Husain yafashe da kuka
     Bajimawa abulfadal yayi bankwana da dan'uwansa yakoma ga rahamar ubangijinsa da imam Husain yaga abulfadal yayi shahada saiya daga sauti yana kuka yana cewa;shikenan yanzu sun karyamin kashin bayana dubarata ta qaranta.Imam Husain yayi kuka mai tsanani akan gawar abulfadal sannan yadubi abulfadal yace"Allah yasaka maka da mafificin alkhairi abisa hidimar dakayi"hakika kayi jihadi don allah da hakikanin jihadi,sannan imam Husain (as) yadaukeshi zuwa hema wajen su sayyida ZAINAB (as).

 Daga Khadija hamza Malumfashi

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post