Tunda safiyar yau Talata 11 ga Almuharram 1441BH 10/09/2019
'Yan'uwa almajiran Sayyid Zakzaky (h) Mazansu da Matansu
suka hadu a babban Masallacin jumma'a na garin Dutsinma da
Misalin karfe 8:00 na safe, aka tashi muzahara ta gangaro
hayin gada da aka zo kofar gidan D.T.C sai aka yo kwana sai
aka dawo ta bakin tasha ana tafiya cikin tsari ana wakokin
juyayin Ashura.
Na kasance a tare da wakilin yan'uwa na garin
Dutsinma Malam Nuradeen Abdullahi Muna hira dashi ina
Mashi tambayoyi na makasudin fitowarsu wannan muzahara
na bada amsa a tambayata ta karshe dashi itace wane kira
yake dashi ga Azzaluman mahukunta da suke kokarin
Afkamana?
Ban gama Rufe baki ba sai ga jami'an tsoro a gabanmu kawai sai
suka bude mana wuta da tiyagas da harsashe mai rai. To
sakamakon wuri ya turnuke da hayaki sai na tsaya na samu
wani wuri na tsaya na cigaba da aiki to shi kuma Malam
Nuraddeen ya tsaya shima ya dake sosai shine suka kamashi da
Malam salihu sabon garin fauguwa da sister Hajiya Aisha
Abubakar Matsiga da wata karamar yarinya, sai wani dan'uwa da suka harba a hannu.
Akwai wasu yan'uwa da aka kama a Fudiyya wadanda bamu tantace yawansu ba.
Lalle Mutanan gari sun nuna ma halacci inda sahun
manyan sistoci suka shiga cikin tashar dake garin Dutsinma,
suka ce ma jami'an tsaro babu ubanda ya isa ya shiga cikin
tashar ya kama wata mata yasha ta mu ce.
Dole suka hakura
suka juya baya aka biyosu ana masu ihu da e'ho ana ce masu
Azzaluman banza ma tsorata Ku tafi daji mana inda barayi
suke, sai kuzo Ku afka ma wadanda basu da makami gaskiya
mutanan garin Dutsinma sun tausayawa yan'uwa, kuma sunyi
tofin Allah ya tsine ga gwamantin Buhari yau har wanda suke
son Buhari naji da kunnena suna tsine Mashi, saboda wasu sun
sha tiyagas wasu kuma sun ga zalunci karara wanda ba a taba
ganin irinsa ba a garin na Dutsinma. Yanzu dai komi ya lafa in
banda jami'an tsoro dake sintiri a garin.
#Dutsinmediawatch
#Ashura1441
Tags:
MUNASABAR ASHURA
