ABINDA YA FARU A WAKI'AR KATSINA YAU TALATA...


Da misalin karfe 7:00 na safiyar yau talata 10,9,2019, 'Yan'uwa
Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na garin katsina suka fara haramar fita Muzaharar lumana don juyayin Kisan gillar da
akayiwa

Zuriyar Annabi su Imam Hussain (a.s) a karbala,
wanda duk shekara suka saba yi kuma a tashi lafiya, Yan'uwan
sun fara haduwa a unguwar darma inda daga nan aka tsara
muzaharar zata daga.

Kwatsam ba ayi aune ba sai ga Jami'an tsaron 'Yan sanda
cikin shigar yaki dauke da muggan makamai, kuma da zuwansu
suka Shiga kakkama 'Yan'uwa maza da mata. To ashe sun
rarraba ne a fadin garin suna bi suna kama duk wanda suka
ganshi da bakaken kaya ko alamar Ashura musamman Mata,
wanda sun kama adadi mai yawa tun kafin asa sahun
Muzaharar.

Duk da kame da bugun 'Yan'uwa da sukeyi sai da Muzaharar ta
Ta tashi daga nan darma har zuwa asibitin Malam Barau inda a nan aka rufe.

Anan ma azzaluman 'Yan sandan basu hakura ba
suka sake biyo 'Yan'uwan da ba abinda ke hannunsu sai
Tasbaha, Sai Labbaika ya Hussain da suke furtawa da baki,
suka ci gaba da dukansu da hantara gami da sa barkonon
tsohuwa (tear Gas).

Ganin Yadda suka takura yin Muzaharar yadda aka tsara, sai
aka kasa jerin gwanon inda 'Yan'uwa na yankuna da basu samu
karasowa ba suka taso tasu Muzaharar daga Unguwanninsu,
kamar unguwar Farin Yaro, da sabuwar kofa, da yankin dutsen
Amare, sai yankin da Shaikh Yaqub Yahya Katsina da kansa ya
jagoranta inda aka taso daga Markaz kuma aka rufe a titin
sabuwar kasuwa (Daki tara).

'Yan'uwan sun dunguma Maza da mata zuwa Markaz don
gudanar da Addu'a kan halin da ake ciki da niyyar Allah ya
kawo daukinsa. Duk da har a lokacin jami'an tsaron na ci gaba
da kama Yan'uwa tare da karkasasu a sassan mahadan tituna ko shatale-tale (Round about).
  
Ashe wasa sabon aji, kwatsam
ana tsakar yin addu'a sai kawai gasu aguje da zuwansu suka
fara antaya ma 'Yan uwa tiya gas dai-dai lungun gidan
'Yandoma. 

Suna sa tiya gas su kuma 'Yan'uwa sun dake suna
kabbara da kiran Labbaika Ya Hussain, amma duk da haka
wannan tiya gas ya rika kai 'Yan'uwa kasa saboda zafinsa da
radadi.

An ci gaba da fafatawa, wanda daga bisani suka gangara zuwa
bakin k/marusa kuma a Nanne suka fara sa harsashi mai rai
(live bullet) inda suka harbi mutum guda kuma suka dauke shi
suka tafi dashi. Har ya zuwa hada wannan rohoton ba a
tabbatar da inda suka tafi dashi ba.

An jikkata mutane da daman gaske wanda akasarinsu da tiya
gas ne a bakin kofar marusa.
Ana haka dai 'Yan'uwa na fafatawa wasu kuma na addu'a a
cikin Markaz, kafin kace me lungun Markaz ya cika makil da
Al'ummar garin suna fadin lallai sai dai a hada damu amma ba
zamu bari a kai ga Malam Yaqubu ba. 

Wannan kyakkyawar
Gudunmawa da jama'ar gari suka bada ta taimaka wajen dakile
shirin su na karasowa a bakin Markaz din, musamman da suka
lura ma ashe mutanan garin ne ke jifarsu da duwatsu suna
cewa; Ku tafi batsari mana ga 'Yan ta'adda can amma don
zalinci kun zo ga bayin Allah kuna harbinsu, haka dai sunayi
suna yi masu eho hadi da aiken duwatsu. 

Wani bangaren mutanan garin Masoya Annabi na cewa; wannan wani shiri ne na
 hana Mauludin Annabi (S) bana na shekekarar 1441BH,
wasu kuwa na cewa wannan Sharrin Izalah ne kuma ba zamu
yarda ba...
Kowa dai na tofa albarkacin bakinsa na la'anta da Allah
wadarai kan wannan mummunan aiki kan 'Yan kasa kuma 'Yan
asalin jihar Katsina.
Da dai suka ga ba has sun nemi a daina jifarsu zasu tafi
alhalin harda Al'ummar gari ke jifarsu suna cewa ku tafi
batsari, suna tsinuwa garesu da tir da wannan danyen aiki.

"Lafiya lau suke yin abinsu duk shekara amma bana wadannan
azzaluman sun zo sun tada masu hankali" inji; wasu al'umar
gari. Su kuwa 'Yan'uwa a cikin Markaz dai an dukufa ana ta
gaya ma Allah (S.w.t).

Shaikh Yaqub Yahaya Katsina ya 
gana da 'Yan jarida kuma ya
bayyana masu halin da ake ciki kuma sun gane ma idonsu
wanda har lokacin ganawar ana jin karar tashin harsasai da tiya
gas suna dukan bangwan Markaz. A nasa bayanin yayin
ganawar Shaikh Yaqub Yahaya Katsina ya bayyana cewa "mu
dai ba zamuje ko'ina ba suzo su kashemu anan".

Kuma wata majiya ta tabbatar mana cewa an ga sadda suke
Harbin motarsu da kansu kuma suna daukar hoto da bidiyo
wanda da alamar akwai sharrin da suke so su kala ma
Almajiran na Shaikh Zakzaky a katsina,

Zuwa hada wannan rohoton dai 'Yan sandan mashaya jini sun
janye jiki daga Markaz din suka nufi Headquarter da kuma
CPS, sai dai bayanin da ke yawo shi ne akwai yiwuwar cewa
zasu dawo da dare....kuma har yanzu ba a tantance yawan
'Yan'uwan da suka kama ba, wanda akawai adadi mai yawa...

Media Forum Katsina

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post