YAN" KWANKWASIYYA SUNYI DAIDAI ABUNDA SUKAYIWA DR.FANTAMI_INJI BABBAN JIGO A KUNGIYAR IZALA

WROTE BY SHARHABIL USMAN PANDOSS
Babban jigo a kungiyar Izala kuma dan gwagwarmayar nan, Abdul’aziz Saeed Marafa, ya ce bai ga laifin ‘yan Kwankwasiyya da suka yiwa Dr. Isa Ali Pantami ihu tare da jifar sa a filin sauka da tashin jiragen sama na malam Aminu Kano ba, domin Ministan sadarwa suka jefa ba wai malamin addini ba.

Abdul’aziz Marafa, ya bayyana hakan ne yau a zantawar sa da wakilin Jaridar Hausa7, Muhammad Lawal dake jihar Kano, inda yace “An yi lokacin da Pantami ya rika cin mutuncin Rabi’u Musa Kwankwaso har yake cewa ko matsayin mai wankin masallaci Kwankwaso bai isa yayi ba a Najeriya.”

“A don haka Pantami dan siyasa ne dole ayi masa ihu, a Najeriya kowa yasan lokacin da Pantami ya rika yiwa Atiku Abubakar kazafi, wanda kuma wannan ba karantarwar addinin musulunci ba ne yiwa jama’a kazafi.”

“Ana nan Pantami ya amshi mukamin D.G NITDA a gwamnatin Buhari bayan ya gama zagin su Bukola Saraki da Eke Ekweremadu da tsohon gwamnan jihar Pilato Joshua Dariye da Obasanjo a wajen karatun sa.”

“Ita kan ta ta’aziyyar da yazo Kano ai siyasa ce, saboda mutum nawa suka mutu a jihar Kano bai zo ba sai dan majalisa kuma dan jam’iyyar su ta APC.” A cewar Abdul’aziz Saeed Marafa.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post