{M.N.N.U} Shafi Domin Kai Da Al'Ummar ka.
Matashi: Shine saurayin da yake cikin ganiyar samartakarsa, sannan yakasance yana tafiyar da rayuwarsa da ma'amalarsa tsakaninsa da mutane da dabbobi da duk sauran Abubuwan dake kewaye dashi a zamaninsa cikin wannan duniyar bisa hanyar da musulunci ya tanadar sannan ya kyautata alakarsa da mahaliccinsa Allah (T), ta Hanyar Ibada (Aamal), da kyawun hali (Mukharimul Aahalaq), da iya zaman takewa da Mutane Mabanbanta Fahimta ta Addinai daban daban da kuma kyautatawa kowa Zato na Alheri. Kuma ita Samartaka tana farawa ne daga lokacin da mutum yake balaga zuwa lokacin da zai cika shekara Arba'in (40), Wannan shine matashi na hakika.
TA WACE HANYA AKE GINA RAYUWAR MATASHI
Ana gina Matashi ne tun ranar Haihuwarsa ta Hanyar Kulawar dan Tsaro tsalkakake Wato (Uwa da Uba) wadannan Sune Farkon ginin Matashi. Sai kuma Tarbiyar, Makaranta ta Addini ta Hannun Malamai Domin Samar da Imani da koyarda kyawawan Dabi"u kamar Yadda Allah (T) yake Fada akan (Matasan Ashahabul Kahafi )
Allah (T) yana cewa: "Su Matasa ne da Sukayi Imani da Ubangijinsu Sai Muka karramasu da Shirya"
Shi Matashi Mutum ne Mai Sabuwar kwakwalwa da gangar jiki mai karfi Wanda Idan Ba'ayi Masa Tanadi Mai inganci ba Sai Ya kasa bada Gudumuwar da ta dace a Addinin Musulunci. Haka kuma Idan Matasa Suka gina Shahasiyyarsu da Riko da Addini Musulunci to Alamace ta Karfin Addini da kuma Babbar Alama ta dawowar Daular Musulunci.
BABBAR GUDUWAR DA YAKAMATA YAN UWA MATASAN GWAGWWRMAYA SU BAYAR ITACE
Kamar Yadda A wani Jawabi na Jagoran Harkar Musulunci Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) Yake cewa: "Guduwar da Kowane Dan uwa Dan Gwgwarmaya Zai bayar a Wannan Tafiyar Shine Yazamana Ka gyra mana kanka" . Jagora ya cigaba yana cewa Idan Ana Maganar Sadaukarwa a Gwagwarmaya kai a kashin kanka yaya kake, Idan kuma akwai Amana kai a kashin kanka yaya kake, Idan Ana Maganar Ibada Kai akashin kanka yaya kake kana Ibadar ne.
To kunga Anan Dole yazamana Matasa yan Gwagwarmaya Sun samu Wannnan Qualities din.
*Sun Inganta Imaninsu
*Sun Siffantu da Kyakyawan Dabi'u
*Sun Kasance Masu Neman Ilimi
*Su kasance Masu Tsayawa da Ibada
Domin Matasa ko wane Zamani na Da'awar Dukkan Manzanni, Annabawa da kuma Salihan Bayin Allah ne.
Matasa Sune kashin bayan tabbatar Addini da kawo Sauyi a kowace Al'umma Saboda Haka gyaruwarsu Shine gyaruwar Al'umma, Hakama lalacewarsu Shine lalacewar Al'umma Shi yasa ma Matasa Suka kasance Abinda Hukumomin Zalunci a Duniya Suke Sama ido da yin Abinda Zasu Iyayi na ganin Matasa basu Zama Masu tarbiyya da Riko da Addinin Musulunci. Domin Sun Riga Sun San cewa Matasa Suna da karfin Azama da Jarumta na kawo Sauyi da cigaba ga Duk Abinda Suka Sa gaba.
Matashi Bai Iya bada Gudumawa a tafiyar Addini Matukar Bai ginu Akan Abubuwan Guda 4, da nayi Magana abaya ba. Saboda Sune (Asahabul Kahfi) Suka ginu akansu Sai Allah ya karamasu Shiriya daga Wurinsa Har suka Jajirce sukayiwa Sarki (DAQA YANUSA) tawaye kuma Suka dake Hakama Sauran Duk Matasan Zamani.
Haka Abin Yake a Yanzu Matasan Zamanin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) Mazlumin Wannan Zamani Yakamata ace Mun Dabbaka Sai Mu Zama Abin tarihi ga Wannan Da'awa ta Jagoran Gaskiya.
[9/15, 6:41 PM] Hassan Musa Shinkafi:
A KARSHE
Dole ne Matasa Masu Gwagwarmayar tabbatar da Addinin Musulunci Mu Farka, Mugane cewa Mune Mukafi Yawa a wannan Harkar Ta Musulunci (Gwagwarmaya) kasancewar Matasa Sunfi yawa yananuna mana Addini Zai tabbata a kasar nan Insha Allahu
kuma Gudumuwar Matasa da Rikon mu da Addini da Neman Ilmi,
itace take nuna Za'asamu Qa'id-Qa'id da Ayaullahi dama Sauran tsofaffin kirki Masu Hukunci a Daular Musulunci.
Haka kuma Rashin karatu da Gyaruwar Rayuwar Matasan Gwagwarmaya Yana tabbatar da Babu Marika Daular Musulunci koda ta kafu (Wal'iyazibillah).
kamar Yadda Jagora Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) Yake cewa _"Wani lokaci Idan naga Dan uwa Yana Dabi'ar Najeriyanci Sai naga Ba fata"_
Ina fatan dai Yan uwa Sun san Ko minene Najeriyancin nan da Su Malam Suke yaki dashi axikin mu.
Kuma Idan Dan uwa Matashi yayi Wafati kafin Tabbatar Addini Alhali yana Mai gina Shahasiyyarsa shine na farkon Mutane bakwai da Allah yayima Alfarma na shiga Innuwarsa a Ranar gobe kiyama Ranar da Babu wata Innuwa Sai Innuwarsa Madaukakin Sarki.
Wannan jawabin Musa Hassan Shinkafi ne dayayi a wajen Birthday din Jabir Bello
Shafin Ma'asumah Nigeria News Update ya nakalto muku.
Tags:
Tunatarwa