DOMIN KAI DA UWAR GIDA PART 4
Babban abin da mai son jin dadin aure ya kamata ya lura da shi shi ne: Mace ta gari, ita za ta iya zama masa zinariya, duk lokacin da ta yi datti in aka wanke sai qyalqyalinta ya fito sarari, amma aure don kyau (wanda shi muke yi yanzu) kamar baqin qarfe ne da aka shafa masa kumfar zinare, yana daukan ido da ban sha'awa, da zarar ka yi amfani da shi Daya, Biyu qyalqyalin zai fita munin kuma ya bayyana, daganan ba sauran sha'awa kuma, galibi qyalqyal-banza dinnan su maza suka fi so, shi ya sa mai haja yake tallata musu don samun kasuwa, maganar gaskiya duk wani dan kasuwa riba yake nema.
Mace ta gari za a same ta da:
Mace ta gari za a same ta da:
• KAMEWA:- daga duk wani abu da zai sosa wa maigidanta rai, a kanta ne ko gidansa ko abincinsa da sauransu.
• GASKIYA:- In za ta yi magana ba ta qarya, domin samun riqe gidan gaba daya.• ZA'BIN MIJINTA A KANTA:- tana buqatar abu amma in baya so za ta barshi, ko ta yi don shi yana so koda kuwa ba ta so.
• AMINCEWA:- duk abin da yake so ta yi ta amince, don yarda da cewa ba zai halakar da ita ba, tana qaunarsa.
• TAWALI'U:- Ta qanqar da kai gare shi koda kuwa tana da ilimi, arziqi da shekaru sama da shi, kamar dai sayyida Khadeejah (As) da Annabi SAWW).
• TAWALI'U:- Ta qanqar da kai gare shi koda kuwa tana da ilimi, arziqi da shekaru sama da shi, kamar dai sayyida Khadeejah (As) da Annabi SAWW).
• NATSUWA:- Kar ta riqa tuno abubuwan da suka gabata, kuma ta dena tsoron masu zuwa.
• KUNYA:- Ta riqa jin kunya, wannan ado ne gare ta, musamman in tana tare da mijinta a cikin jama'a, wannan zai qara masa qaunarta.
• KWANCIYAR HANKALI:- mantawa da matsalolin rayuwa da qoqarin tura farin ciki ga mai gida koda suna cikin matsala.
• GODIYA:- duk abin da ya zo da shi a nuna masa jin dadin zuwa da shi komai girmansa komai qanqantarsa.
• HAQURI:- A kan duk abin da zai bayyana daga miji (wannan ne kawai muka dauka alhali suna da yawa).

• TSAYUWA QYAM:- a wajen bauta da qarfafa mijin da 'yansu.
• AMANA:- ta zama mai amana, kar ta yarda maigidanta ya ga ha'incinta koda kuwa sau Daya ne, ta riqa gaya masa abin da za ta yi domin maganin shedan.
• CIKA ALQAWARI:- Yana daya daga adon mace da namiji.
• TSORON ALLAH:-a duk abin da za ta yi.
• DANNE ZUCIYA:- yayin da aka baqanta mata rai.
Wadannan abubuwa guda 15 su suke nuna mace ko miji nagari, kada ka riqa binciken qyalqyal banza, ke ma ki dai na kallon kudi ki duba rayuwarki idan kin shiga gidansa, komai kudinsa in ba kwanciyar hankali ba za ki ji dadinsu ba.

Tags:
Taskar Ma'aurata