Yadda Dan jarida yakamata ya nadi Rahoto.

A hannun dama Shugaban Gidan Radio Shafin Ma'asumah Comr Nazir Sa'idu Gusau Sai Mas'udu Dan Masani Shinkafi A Tsakiya Tare da P.R.O na gidan Radio Abubakar Ibraheem Kudan


A'uzu billahi minashaidanirrajim!

Bismillahirrahamanirrahim !!

Innalillaha wamala'ikatuhu yusalluna alan nabiyi, ya ayyu hallazina amanu sallu wasallimu taslima!!
Barkammu da kasancewa adai dai wannan lokaci, me tarin albarka

Babu shakka ance nayi bayani akan mau'du i mai taken  'Hanyoyin da akebi wajen nadar murya'

Wato recoding voice.!


Alhamdulillah.

Nafarko inaso musan wani abu daya.

A gidan jarida,akwai wasu gidaje daban daban.
Ko muce, department daban daban.

1. Akwai sashen shireye shirye

2. Akwai sashen  tallace tallace

3. Akwai sashen muhimman ayukka.


To bisa dibo da wadannan gidaje dake garemu agidan aikin jarida, zamu dauki daya daga cikin wadannan miyi bayani akai.

Wato, sahsen muhimman ayukka.

Wannan sashe. 

Ana amfani dashi ne,wajen yin wasu ayukka na musamman.

Misali:
Matsayinka na ma aikacin jarida ana iya turaka wajen wani muhimmin aiki na dauko rahoto.

Zamu iya kiran wannan aiki dasuna reporters.

Shi wannan aiki na dauko rahoto, yata allaqa ne  ga kwararren ma aikacin jarida.

Shi wannan aiki yanada sharudda,dakuma qalu bale mai tarin yawa.

zamu dauki daya muyi bayani akai.!!

1. Qalu balen dake cikin dauko rahoto.

So dayawa ma'aikacin jarida wato reporter  zai dauko rahoto, amma daga baya se aikin yabashi mastala, ko kuma yabashi Ruwa!

Wanda ta sanadiyar shi yayi sanadiyar zuwanshi gidan yari.

Abu na biyu duk dai acikin qalubale!

So dayawa ma'aikacin jarida, kuma kwararre.

Zaiga ya kammala aiki,amma se kaga Ansamu matsala wadda zaiyita kokarin samun mafita,daga qarshe dai lokaci yazo yayi halinsa, ma'ana lokacin da anka dibabarma  shirin yazo yawuce batare da an cimma biyan buqataba.

__ duk dai acikin qalubalen da dan jarida yake samu acikin aikin shi.

Wani lokacin kana kwance agida kawai se kaji ance  kaje waje kaza!
Munaso kadauko muna rahoto akan abu kaza!

Babu shakka wannan qalu bale ne me qarfi,wanda duk dan'jarida ,. Musamman me dauko rahoto yafi kowa shan wahala acikin wannan aikin.
___Akwai buqatar idan an turaka dauko rahoto amatsayinka na wakili, na gidan jaridar da kake wa aiki.

Katsaya kayi aiki me ma'ana, wanda za ayi alfahari dashi.

__Akwai buqatar  kanatsu wajen dauko sahihin sako acikin rahoton da zaka dauko.

__Akwai buqatar  kasanya hikima da dubaru wajen dauko rahoto na musamma wanda watakila kai ne mutun na farko wanda zaka yada wannan sako.


___Akwai buqatar  kadinga aiki a asirce  saboda gudun fadawa tarkon miyagun mutane.

______Haka kuma akwai buqatar kayan aiki masu kyau.
Wadanda suke sunyi dai dai da na zamani.

So dayawa zakaje dauko rahoto,se kaga anki a barka kashiga wajen da yakamata ka dauko wannan rahoton, to a aikin jarida akwai wasu dubaru da ake amfani dasu wajen cimma kudurinka na dauko rahoto.

Bubarar ita CE.

Akwai yan'uwanka yan'jarida wadanda sunsamu damar shiga wajen.
Idan sunfito akwai yiyuwar kasamu daya daga cikin yan'uwanka yan jarida kasamu wasu muhimman bayanai agareahi.

Amma da zummar kai kanka kayi taka tsan-tsan, wajen daukar bayanai Ina nufin ID card.

---- Idan kuma Allah yasa kasamu shiga wannan waje na taro,to akwai buqatar  kanatsu sosai, wajen dauko wannan rahoton.

Abu,  muhimmi acikin wannan aiki shi ne.
Kayan aiki in gan-tattu.

Wadanda sunkayi dai dai da zamani.

Saboda go gayya da sauran yan jaridu na duniya.
Musamman qashen da sukaci gaba.

Dawannan zan taqaita saboda yanayin lokaci.

Ina fatar Allah yasa muyi muwafaqa acikin wannan aikin.
Kuma yan'uwa se adanyi hakuri da yar tsarabar da nariko maku.

Ban saniba ko akwai me tambaya?

TAMBAYA

Assalam mlm yanzu idan inason. Nadar sauti Kuma inason inbayya Abunda akeyi acikin sauting musamman irin Wakar da kukesawa a wajen hada rahoto ko Kuma Muzaharar da ABUBAKAR KUDAN yasaka a Cikin Rahoton Muzaharar Daya dauka yazanyi Kennan??

2_Sannan yanzu Wakilin Ma'asumah yanada cancantar dauko rahoto saboda yanada I'd card Nashi??
Kamar yadda kukeyi??

AMSA:-


Na'am!!

Malan mas'udu naga tambayarka.

Babu shakka wannan abu ne me matukar wahala, wanda gaskiya duk bayanin da zamuyi anan bazai gamsar ba.

Sbd shi wannan aikin yana buqatar Gwaji!!
Wato practicall .

Alokacin da mukayi taron Shafin Ma'asumah na Karawa Juna sani A garin Kano ,duk wanda ya halarci zaman da mukayi,yaji irin yadda zaiyi ya hada rahoto.

Tambayarka ta 2

Sosai kuwa, wakilin Ma'asumah aduk inda yake zai iya shiga cikin jerin  yan jarida.
Yaje yayi aiki yadda yakkamata,sbd ya mallaki ID card nashi.


Batare da yayi amfani da manyan na kurorin nadiyar sauti ba..

Wannan 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post