DOMIN KAI DA UWAR GIDA.
Yaku magidanta wannan filin naku ne,
Ku dai ku kasance da wannan shafin ako da yaushe......
Mai gida da uwar gida jiya dai mun dauko bayani akan sinadaran abincin da muke ci, duk da cewa zamu dan buda bayani kadan akan abinci mai sanya nishadi wato "Nashwaat" ana kiransa da (Starch) ana samun sa sosai a hatsi, da 'ya'yan bishiya, dankali da dangogin waken 'pea' kamar sweet pea, ba shakka wannan sinadari yakan tanadarwa jiki nishadin da yake nema.
Ataqaice za a iya cewa kuzarin da dan adam yake buqata wajen nishadodinsa yakan samu ne daga Fats, Starch ko in ansamu ragowar abinda jiki yake buqata na Proteins.
Kashi na ukun kuwa shine mai tsara nishadin mutum, wannan kuwa yakan samu ne ta wurin samun kyakkyawan markade abinci acikin dan adam, sinadarin yaqunshi Organic acid, Minaral, Vitamins da Ruwaye.
Ana samun wannan sinadarin acikin ganyanyakin da muke ci, da kuma 'ya'yan bishiya, shi kuwa Ruwayen da muke magana yakan taimaka ne wajen tsare ruwan dake jikin dan adam alokacin da yake asarar sa,
yakan tsarawa mutum zafin cikin jiki, tare da agaza masa wajen fitar da ruwan da bai da amfani, ta hanyar ji6i da fitsari akan sami wannan ruwayen aduk nau'o'i na abinci, masamman
'ya'yan itatuwa da ganyayyaki, akan kuma sameshi a ruwan sha.
To sai dai mugun ci yakan haifar da matsaloli da dama ta 6angaren kiwon lafiya, domin yakan jawo qiba, haka duk 6angarorin jiki yakan juya ya buqaci Fatawan da zai riqa taruwa aqarqashin fata, yawaita wani nau'in abinci yakan jawo.
*Cutar 6ataccen abinci, misali yawaita cin nama yakan haifar da cutar ga6o6i, ya raunatar da hanta da qoda, haka yawaita cin Fats da kayan zaqi yakan qara qiba hakan kuwa zai iya haifar da matsala a gudanar jinin mutum, hanyar gyara kawai mutum ya daidaita cin abincinsa, wanda ya hada duk
sinadarorin da ciki yake buqata ba tare da saka daya a gaba ba, misalin Carbohydrates, Fats, salts da Vitamins,
Zamu taqaita bayani akan su kafin mu fara hadawa magidanta irin magungunan da zasu
riqaci wadanda dama abincin sune ba a asibiti ko kasuwa zasu sayo ba.
Protein kamar yadda muka nuna a baya cewa yana gina jiki da ha66akashi, to qarancin sa yakan haifar da matsaloli na hana ha66akar jikin da sakewar ga6o6i, ana samun wannan sinadarin a nau'o'in nama, da kifi, haka qwai, nono da duk abinda ake sana'antawa dashi, da irin su wake da dangoginsa da adas(letils), duk wani jiki mai nauyin Kg 1, yana buqatar gram daya na Protein a kullum, domin sanin wanda yafi atsakanin Protein na jikin dabba dana tsirrai dole sai mun koma ga wanda yafi qarko gwargwadon Amino acid, zamu ga cewa qwai yana da kashi 100%, nama 83%, madarar shanu 80%, kifi 70%, wake 73%, wannan ta 6angaren qarko ne gwargwadon yadda suka
qunshi sinadarin Amino acid, zamu ga na 6angaren dabba yafi na tsiro.
To amma kuskuren da ake samu shine, wasu sukan yawaita cin nama basu san hakan kan na haifar da qiba ba, suna zaton yafi qara lafiyar jiki da ta shimfida, gaskiya cinsa ma da rabin kilo a rana na
(nama) zai iya haifar da matsala, domin duk yadda aka raba nama da kitse dole yana nan acikinsa, manazarta sun gano cewa cutar kansar hanjin qarshe 'Coloncancer' tafi cafkar masu yawaita cin nama sama da buqata, to amma fa in abincin da muke ci babu Protein din ana iya kamuwa da cutar
qarancin
jini 'Anemia' da hauhawar hanta, kumburin qafa, ramar jiki wace take gamawa da mutum, rauni wurin saduwa da sauran ga6o6in jiki.
Idan aka lura da kyau za a fahimci cewa, jikin dan adam yana buqatar nau'o'in abinci, domin kaucewa kamuwa da wasu cututtuka, ya kamata mutum yabi tsarin muslunci wato tsakaitawa cikin komai, duk wasu nau'o'in abinci da mutum yake gani suna da aikinsu, bawai Ubangiji (SWT) ya
halicce su bane mutum ya za6i daya ya yi shirga saboda wadata ko rashi, a'a, zai riqa cancanjawa ne saboda lafiyars a da ta iyalinsa gaba Daya, harma da lafiyar shimfidarsa wace don ita muke wannan bayanin.
Tunda muna da niyyar kawo nau'o'in abinci, wadanda munsan tabbas suna taimakawa
magidanta wajen biyan buqatun shimfida, dole kuma mu bayyana musu abubuwan da wadannan nau'o'i na abincin suka qunsa, galibi qasashen nan namu masu tasowa, sukan dogara ne akan nau'in abincin da yaqunshi sinadarin Carbohydrate, kodayake wannan sinadarin yayi fice ne da kayan zaqi da Starch, to amma haduwarsa tabbas daga Hydrogen ne Oxygen da Carbon.
Ko ya akayi dai dole abincin da muke ci yaqunshi kashi 50% na Starch a abincin da mutum zai ci arana, wannan sinadarin akan tattaro shine daga nau'o'in abinda mutum zai ci, sai dai anfi samunsa a alkama da dangoginsa, masara, makaroni, shinkafa, bredi, zuma, sukari da sauran kayan zaqi.
Akan sami tsakaitaccen sa a 'ya'yan bishiya, sai dai yafi yawa a dabino,(kalli hikimar da tasa Annabi ya umurci mai azumi da cin danyensa wajen bude baki), inabi, ayaba, mangwaro, ruman, abarba, da sauransu.
Akan sameshi a ganyayyaki amma yafi yawa a dankalin gida da na turawa, haka sauran dangogin wake da nono ko abinda akayi shi dashi, amma gaskiya kusan ba starch a jan nama(na dabbobi)da fari(na tsuntsaye da kifaye).
Wannan sinadarin na Starch da aka tatso shi daga abincin mu yakan narke gabadaya sai hanji ya
tsotsoshi, sai dai shi kansa hanjin yana da iyakar da zai iya tsotsa, don bai da qarfin da zai iya tsotson sukari sama da gram 120 a sa'a guda, don haka diban abincin da yake da Starch sama da wannan, iyaka yakan hana hanji tsotse shi gabadaya, to sai ciki ya kumbura, sai tusa koma zawayi a
wasu lokutan wannan yasa wasu suke fama da wannan matsalar in suka ci wani nau'in abinci.
Sukari kuwa bayan tsotse shi sai hanta ta adana kashi 5% a sifar sinadarin Glycogen, ta juya kashi 30% 40% zuwa sifar Fats, sauran sai su je 6angarorin jiki don amfana dasu, alokacin azumi ko yunwa sai hanta ta juya wanda ta adana din nan na Glycogen zuwa sukari, kamar yadda zata juya Fats da Protein zuwa sukarin, domin qoqarin tare gwargwadon da ake buqata na sukari acikin jini, kuma don sauran jiki ya amfana.
Ba shakka abincin dayake qunshe da sinadarin Fat, yana da sauqin samu a kasuwa, kuma mutane sunfi sonsa, don yafi saurin kauda yunwa, duk da cewa bai dadewa zai narke, to amma fa shine ginshiqin farko dayake maida mutum tulele, domin nan da nan zaka ga mutum ya nemi qarin wani bayan ya cinye na farko.
Ba shakka wadanda suke fama da cutar qiba sunfi kowa son irin wannan nau'o'in abincin, kuma ba sa yi masa da wasa, masamman shinkafa, makaroni, bredi da kayan zaqi.
Saboda mahimmancin sinadarin Fat din nan yakamata muta6oshi, domin shima wani ginshiqi ne mai mahimmanci na kuzari, samun gram daya nasa yakan ba jiki madaran zafi(thermochemical calorie), alhali Carbohydrate yakan iya bada 4 ne kawai, sai muyi qoqarin daddale wannan bayanin a darasi na gaba insha Allah.
Sinadarin Fat dai yakanyi aikine amatsayin dan tsakiya, wato mai taimakawa wajen tsotso Vitamins dake cikin Fats din, misali vitamin A, Vitamin D da Vitamin E, wanda wannan E din sananne ne gareku, masamman mahimmancinsa ta wajen taimakawa masu neman haihuwa.
Adalilinsa ne ma zamu yi qoqarin kawo sauran kashe-kashen Vitamins din, wannan sinadari na Fat, yana dauke ne da wasu acids wadanda 6angarorin jiki suke buqata, masamman 6angaren qwanyin haihuwa, tabbas qauracewa wannan sinadarin yakan kawo bushewar fata, da sal6ewarta wace galibi takan fara da kan ga6o6ine irinsu gwiwa, daga nan sai ta bi sauran jiki.
Ba wannan kadai ba, gujewa wannan sinadarin kacokan zata iya haifar da zuban suma, lalacewar qwanyin haihuwa da yawan buqatar shan ruwa kodayaushe, ko kuma cutar matsarmama, don haka
ne likitoci suke bada shawara da a riqa dan qara wannan sinadarin a abinci amma cikin lura, karya wuce kashi 15% a abincin kowace rana.
Fats dai kan shiga abincin mune ta wajen man shanu, butter, kakidi, fatar kaza (shiyasa ake hana wasu ci), nono da duk abinda akayi dashi, amma bashi da yawa a ganyayyaki, ko a dabbobi anfi samu a na rago sama da na sa, sannan kadanne qwarai a qirjin kaji in ancire fatar (shiyasa ake bawa marasa lafiya shawarar cire fatar qirjin kaza kafin su ci), bashi da yawa a zuciya da qoda.
Cutar daskarewar magudanan jini wato(Arterioslerosises) kan samu saboda dibar wannan sinadarin sama da qima, matsalar mu itace duk lokacin da muka sami abinda ranmu yake so to sai muyi masa cin qoshi, ba tareda sanin cewa duk abincin da muke ci magunguna bane, kuma duk lokacin da mutum yayi overdose zai gayawa jikinsa.
Wannan yasa muka kawo sinadarin Cholesterol, abune mai mahimmancin gaske wajen sanya qwaqwalwa nishadi, da ha66aka aikinta, yakan taimaka wajen samun lafiyayyen harmones din da
jiki yake buqata musamman ma na 6angaren saduwa.
Hantar dayan mu ita tafi bada kaso mai girma na sinadarin Cholesterol, takan fitar da kashi 80%
daga nan asami 20% acikin sauran abincinmu, to in wannan sinadari ya wuce Milligram 300 acikin jini ya zama matsala, domin ana buqatar mutum ya sami qasa da milligram 200 ne a abincin kowace rana, idan wannan sinadari ya hauhawa zai daskare a magudanan jini, ya hana jiki samun lafiyayyen jini mai cike da Oxygen, kenan akwai yuwuwar kamuwa da cutar bugun zuciya(Heart attack).
Zai jya hana jini zuwa matsayansa wurin qwaqwalwa, hakan zai iya haifar da daukewar aikinta wato(Cerebral stroke).
Mai yiwuwa mafita anan ta zama hana hanta fitar da gwargwado mai girma na wannan sinadarin ta wajen rage cin abincin da yake da gamsasshen sinadarin Fats, da wanda yake dauke da na Cholesterol din, an dai fi samun cikakken Fats din a nau'o'in abincin da muka fadi a sama sai kuma manja da man farin kwakwa, ga dai irin ta nan muna ganin masu son qarin ruwan maniyyi suna dibar ruwan kwakwan ba adadi ba tareda neman shawarar likita ba.
Ba ko shakka wasu abubuwan mukan sha su ko muci domin samun lafiyayyen aiki a shimfida, kuma zahirin gaskiya muna samun biyan bukata, amma shin muna da wata masaniya cewa babu wata cuta kuma da take taruwa mana a wasu sassa na jiki? Abin ban haushi ma, wasu sauyoyin itatuwa suke dibgawa aciki, don kawai suga miqewar mazakuta batareda sanin illar irin wadannan magunguna ba, nasihar qarshe itace, kowani nau'in abinci muka saka a gaba, mu guji yi masa cin Allah kadai zai raba mu.
Dole dai aqarshe muba magidanta haquri da cewa, magungunan da muke sa ran kawo muku abincin ku ne da dama kuke ci, to amma zamu fara gaya muku illolinsu da yadda ake aiki dasu tukun kafin mu kawo, kuma kada mutum ya saka abinci daya agaba yayi ta masga domin neman biyan wata buqatar.
Mu hadu a fitowa ta gaba
Haruna ne ya rubuta
Tags:
Taskar Ma'aurata