Turawa Abokkai da Yan uwa domin su amfana.![]() |
Mlm Yahayya Isa (Muslim) Shinkafi a dama Sai Comred Nazeer a hagu a wajen Taron karawa juna sani na Wakilan Shafin Ma'asumah. |
Inafarawa da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Ina neman tsarin Allah daga shedan jefaffe daga rahaman Allah,
Allah kayidadin tsira ga Annabi Muhammadu da iyalan gidansa tsalkaka
Allah gaba maulana sheikh ibrahim yakubu zakzaky lafiya Allah kadawomana dashi acikinmu Allah kacikamasa gurinsa na tabbatar addini a wananan kasa.
'Yan uwa musulmi maza da mata na wanga shafi mai albarka na ma'asuma assalamu alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu
Da farko inayima kowa barka da zuwa da fatan anyini cikin koshin lafiya?
FILM HANYACE TA ISAR DA SAKO KAI TSAYE ACIKI AL'UMMA
Dafarko minene film?
Shirinie na isar da sako ta hanyar yin labari dangane da faruwan wani abin ko ainahin sakon da ake so a isar
Film hanyace ta isar da sako kai tsayi acikin al'umma kuma yayima mai kallonsa tasiri batare da yanemi wani ko
Wataba don yayi mai karin bayani,
Idan kalura saboda tasirin film da kuma zamanai hanya kai tsaye ta isar da sako hatta da 'yan isiyasa sun anfani da film wajan isar da manufar da sukeda'ita siyasa
Saboda tasirin film da kuma zamanai hanya mai sauki ta isar da sako kai tsaye acikin al'umma
Hatta da masu tsaron kasa da akecema soja ko 'yan sanda ko dss suna anfani da film wajan isar da sakon da suke so su isar a cikin al'umma
Idan kunlura abinda a kayi mana a zariya bai yi tasiriba sai da suka hada film na karya sannan suka dauki nauyin yadashi acikin al'umma wanda kai dan uwa dakayi magana na cewa abinda yafaru zariya na cewa antarema shugaban sojoji hanya karyane, nan take sai mutun ya nunama film gashi mungani...tahaka film din yashiga al'umma kuma yayi tasiri
intakaice maka mutane basu gamsu da abunda akayimana a
Zariya zalunci neba sai da 'yan uwa suka fito da nasu film
Ina kawo wannanne dan 'yan uwa sugane cewa film hanyace ta isar da sako kai tsaye a cikin al'umma kuma sakon ya'isa.
AMFANIN FILM
Ana amfani da film wajen tallata kasuwanci, yan kasuwa da dama suna amfani da film wajen tallata hajojinsu domin ddomin domin dominuniyay tasan dasu.
Mai dan karamin kasuwanci cikin lokaci kan Kane zai iya zamowa babba mai fadi idan yana wallafasa al'ummah na gani.
ILMANTARWA
Film hanya ce da al'ummah kan sami ilimi cikin sauki daga gareta, ta hanyar amfani da film za'a iya aika ilmummukan da zai mutum ya gama rayuwan sa bai san su ba.misali idan muka dauki wa'azuzzukan malaman mu da ake sanyawa ta hanyar film yafi sauki mutum ya zauna yana kallo kuma yana fahimta tamkar kana wurin.
WATSA LABARAI KO ISAR DA SAKO
Idan mukayi duba da duk gidajen radion duniya manya-manya irin su BBC, VIA, CNN, FIR, dama sauran su duk suna watsa labaran su ta hanyar film ne.
Wannan ina kawo sune dan 'yan uwa sufahimta
kuma sutashi tsaye dan ganin sun isar da sakon wannan harka acikin sassan duniyar nan.
Mutum na farko da ya zama marubuci kuma dan film na farko shine wani Masani mai suna Tepsis of Iscaria. Tepsis of Iscaria mutum ne da ya fito daga garin Iscaria kuma mai ilimi sosai wanda a wannan lokacin matakinsa daidai yake da na professor a wannan zamanin da muke ciki yayi tunanin cewa ya kamata yayi amfani da iliminsa na yin abubuwa uku akan yanayin bautan gunki da akeyi a qasar Greek .
Na farko ,Mutane suna bautawa gunki a kowace shekara su kaiwa gunki abinci don neman tabarraki kuma gunkinnan bai taba amsa musuba. Tepsis ya rubuta labari akan gunkinsu da jama'a. Wannan shekarar da lokacin bauta yazo ,sai ya je ya buya a bayan qaton gunki. Da sufara bauta, sai tepsis ya amsa cewa, Ni Allanku na amsa muku. Bayan an kammala bauta, sai mutane sun kuma gida da faribciki. Tepsis ya cigaba da haka, yana fantaw wa masu bauta sannan yana farantawa marayu.
Malamai, masana addinin musulinci sun gano Allah ne ya farayin Director na film mala'iku ne sukafara zama masu yin film...
Mukoma tarihin Annabi Adamu (as) na abin da yafaru ga diyansa kabila da habila na kisan kai a tsakaninsu inda Daya yakashe Daya ya rasa yadda zaiyi da gawara sa. sai Allah yayi umurni da Mala'iku dasu Yi (Actions), sukatafo da siffar tsintsaye sukayi fada a tsakanin su hartakai da Daya ya binne Daya, daganan sai shi....
Ba sai na kawomaku tarihin anan ba saboda lokaci kowa yasan tarihin.....
Gaskiya yakamata muba wannan janibin fahimmaci na film
Yazamuyi muyi Firm ??
Shin Da farkoma Wanene Dan firm??
Dan Firm Shi ne:- Wanda yake Shiga cikin rigar wani daban labarin kuma ya kwaikwaiyeshi dai-dai halayen Wanda ke cikin labarin ta yadda masu kallon zasu rika tunanen ainahin gaskiya ce suke kallo .
Ana Samar da yanayin ne ta hanyar saka dan wasa dai-dai da inda yadace cikin labarin , da yin amfani da sutura da sauran abubuwan da ake bukata cikin labarin
SHIKA-SHIKAN DAN FIRM DOMIN ISAR DA SAKO MAI KYAU DA INGANCI, KWARA BIYAR NE (5).
1-Yanayin kirar jiki (carriage)
Shi yanayin kirar jiki Nada nasaba Da yanayin da ake bukata a cikin kudin Shirin wasar Wato (scriot) Idan labari yakawo cewa jarumi ko jarumar cikin wasan do go ne ko doguwa , fari ko Fara , baka ko baki kato ko siriri. Abinda akeso shi ne shi dan wasan ya zamo ya Nada yanayin shi Wanda ke cikin Labarin.
2-YANAYIN ZAMA (POSTURE)
Idan zaka dau photo ya ya kake zama , tsayawa , tsugunne? Duk kowane yanayi Nada na shi yadda ykmata yakasance , misali: idan macce da mijinta suna tattaunawa a cikin falo yaya yanayin zaman su zakasance ?? Tabbas zama zasuyi suna fuskantar junansu. Haka zalika idan akwai rigima ko ta shin hankali tsakanin su basuga ta zama ba a tsaye zamu gansu suna zarewa juna Ana daga murya Ana hantarar juna.
3-YANAYIN AMFANI DA SASSAN JIKI (GESTURE)
Kalmar Gesture na nufin yin amfani Da sassan jiki yayi magana batare da ya furta komai ba amma kuma a fahimci abunda yake fadi ko yake nufi ga Mai kallon sa.
Da akwai Sassan jiki da suke da muhimmanci a wannan bangaren Isar da sako
(A)- Fuska ita ke dauke Da dukkan ma'adinan da ake anfani dasu wajen isar da sako , alal misali:- idan kahadu da mutun sai ya turmushe fuska koda baice komai ba alamun fuskarsa ta nuna cewa yana fushi ne kaga dole ka kiyaye.
Idan kuma ka tarar Da fuskarshi da annashuwa kasan cewa yana cikin farin ciki bazaka ji darr na .
(B)-Ido Nada matukar amfani wajen Isar da sako misali:- idan wani yagamu da ibtila'I Mai tsanani koda bai bare baki yana kukaba do..
(C)- Baki da abubuwan cikinsa .
Idan aka baka labarin da yabaka mamaki me zakayi Keenan? Farko alamar mamaki shi ne bude baki Wanda idanu na taimakawa ta hanyar zare ido
(D) hannu Nada matukar amfani wajen kwatance . idan bakason mutun ya iso inda kake zaka iya dakatar dashi da tafin hannunka batare ba tare da nuna cewa ya dakata ba. Zaka iya nunawa da hannunka cewa mutun yabarma gida. Da yatsa zaka iya gargadi ko nunawa mutun ya matso kusa KO alamar a'a ...
Wata Sabuwa..
KAFIN MU FAHIMCI DUK ABUNDA MUKA TATTAUNA ACAN BAYA SAI MUN FAHIMCI MINENE WASAN DABE??
Wasan dabe shi ne shirin drama da akeyi a kebabbun wurare kuma a bainar jama'a kamar tamsiliyya da akeyi akowane gari na ashura.
Wassan dabe na zamowa ne ta hanyar Samar DA:-
1-labari
2-yan wasa
3-dandali (wajen wasar)
4-sutura
5-Kayan amfani
6:- Kwalliya
7-Haske da Sauransu
1-Labari:- Shi ne Abu na farko da suke samarwa soboda shine jadawalin da akebi anan da abunda yakunsa da duk abunda akeso agani, wane irin Dan wasa ake bukata , yadda aka Samar DA labarin domin Isar da sako a dandalin kaya sutura kayan kwalliya da sauransu.
2-Yan wasa:- Sai a duba cikin jadawalin labarin aga wane irin Dan wasa yakamata a tanada .
Labarin zai iya tanadi katon namiji baki gajere zai iya kawoshi a matsayin Mai kudi , a hakan za'abi a fidda duk launin Dan wasa Da labarin daya bukata .
3-Dandali:- Wajen gudanar da Shiri anan za"a duba yanayin dandali (wajen wasar) yadda labari yakawo sai a samar dashi ta hanyar fiddashi har yabayr da ma'ana don Isar DA sakon da ake bukata cikin labarin.
4-Sutura:-Sune rigunan da ake sakawa cikin shiri.
Kamar akowane fanni labari zai iya fitar da irin kayyayyakin da ake bukata da ake bukata a sanya a cikin shirin . Misali:- idan akace wane sarki ne Ko Mai kudi ne ko Dan fashi ko tallaka , Maga anan suturar data dace DA kowane Dan wasa za'a Sanya masa.
5-Kayan amfani (props)
Wadannan sune kayan daki kwano hoton bango ,abinci,ruwa,kayan alatu, da sauransu.
6- Kwalliya:- tanada amfani wajen fassara labari ,misali- kura ta tsaga fuskar wani mafarauchi dole ne muga ta yadda ya tsaga fuskar .KO kuma matar sarki Tasha ado iya ado dazai nunama masu kallo cewa wannan matar sarki ce ko matar Mai kudi .
7-haske:- shi ne Wanda ake bukata a haska domin fassara yanayi da kuma wuri acikin wasan danbe KO firm sai dai haske sun Dan banbanta da juna kamar yadda ko a kwan lantarki akwai fari akwai ja...
SHAWARA
Shawara ga 'yan Wakilan Shafin Ma'asumah..da yakamata suba wannan janibi mahimmaci dan sakon sayyid (h) ya kara shiga acikin al'umma...
Kuma kowa na iyayi a garinsu ba sai Muba
Ga misali nan ga 'yan malunfashi
.
Anan zan tsaya
Ina rokon Allah ya ganardamu abinda muke karantawa ya shiyardamu da shirin da keciki
Allah ya farantamana ya dawomana da jagoranmu a cikinmu sayyid (h)
Allah ya kara dafama
Masu hidima ga wanga shafi Mai albarka na Ma'asumah Nigeria News Updated
TAMBAYA;-
Mlm Yahayya idan inason indauki firm na comedy da muka shirya na shafin Ma'asumah dole sai da kyamara ko Kuma computer na gyaran Vedion kamar yadda Naga kunayi??
Amsa:-
@Dan masani uwayen tsokana, To agaskiya nasan kayi wannan tambayarne domin wasu sugani su anfana
Daukar vedio basai DA kyamara ba amma da kyamarar yafi haske, yanzu wayoyi hanyoyine mafi sauki na daukar comedy ta hanyar dauka ta gicce cikin natsuwa ba motsi to duk dauka guda (sin) Sai ka yanke wajen gyara sai kahadeshi sannan editing gyara ba dole sai DA computer ba, zakuji komai anan gaba......
Ngd
Wannan Itace karshen Darasin da Mlm Yahayya Isa (Muslim Shinkafi ya gabatar a dakin karatu Na Wakilan Shafin Ma'asumah Nigeria News Updated a ranar Jumu'a 19-Sept-2019...
Masha Allah da wannan bayini Allah ya saka da alkhairi
ReplyDelete