Ma'asumah Nigeria News Update!
Na Sheikh Zakzaky
To ina Baku labarin daidai farkon Al'ummar da ta fara fanɗarewa itace Al'ummar da aka aika mata da Nuhu (As) wanda Annabi Nuhu ya kira su, yake Cewa: Ya Mutane na ku bautawa Allah baku da wani Ubangiji inba shi ba, suka ce a'a wannan kai dai kawai ƙire kake yi, mu tunda muke bamu taɓa jin labarin Cewa Allah ɗaya ake bautawa ba, Har ma dattawansu suka ce, karku ƙyale 'Wud' suna da wani Ubangiji suna ce masa wai 'Wud' sunyi shi ne, sassaƙa shi suke yi a tsufan Mutum, 'Wa ƙalu la tazarunna wuddan wala suwa' an, Wala yagutha wa ya'uƙa wa nasra, sunayen gumakansu, suna ce musu karku yadda ku bar wud Ubangiji da aka sani tun farko, karku bar suwa, kar ku bar Ya'uƙa, Yagus, karku bar nasra.
To Nuhu yayi ta kira, ya shekara cikinsu duba ba hamsin (950) yana kira, amma kaɗan su kai Imani daga cikinsu, sannan Nuhu (As) yai Addu'a yace Ya Rabbi waɗannan mutane baza su taɓa Imani ba, kuma in ka bar su, baza su haifi kowa ba sai fajiri mai yawan kafirci, Ya Rabbi karka ƙyale ko ɗaya daga cikinsu da rai, Allah ya amshi Addu'arsa, ya aiko masu da ruwan ɗufana.
Kafin nan Allah ya umarce shi da yin jirgi wanda, da ba'a san jirgi ba (kafin nan) kuma da can ruwa baya ɗaukan jirgi, ba'a san shi ba Sam, ba ma zai yiwu ya ɗauki jirgin ba, tunda bayan ruwan jirgin Annabi Nuhu (As) ne Allah ya hore ma Ɗan Adam jirgi ya ƙyale shi don ya zama aya, don haka duk nauyin da ake zuba ma jirgi sai ya ɗauka saboda horewa ne na Allah, Horewan Allah ne, inba don Allah ya hore ba, lalle ai jirgi bazai iya ahau kan ɗororuwa abu ya zauna ba, duk wani abu na horewar Allah mutum zai iya ganewa, sai dai in ya zama butulu akan cewa, wasu lallai ba wani dalili bane illa kawai horewar Allah ne, don randa Allah yaso ya nitsar da jirgi ya akan zama ya nutse ba wani dalili, sai aga cewa ai ba aga dalili ba,
Kunsan labarin wani jirgi wanda ana yawan faɗan shi, har yanzu ana nan anata 'research' har ma anyi rubuce rubuce ba kaɗan ba akan wani jirgi mai suna TITANIC wanda ya tashi daga Turai ya tafi Amerika, daga London ya tashi gabar ruwan na Britain Amerika, ance ainihin da wasu ke shiga ance akwai wata mata (ni wannan ƙissa Naji bansan ko dagaske bane) ance amma akwai wata mata da taji Ɗan tsoron shiga, sai wani yace mata wai ko Allah ma bazai iya nutsar da wannan jirgin ba, sai ta shiga, to ko yana cikin tafiya kamar yadda sun ce ainihin ƙanƙara ne ya tsaga ƙasansa, ya tsaga ƙasan sai ruwa na shigowa, kuma suna da Ƴan kwale kwale na ɗiban mutane wanda bai fi ya ɗauki ɗaya bisa uku na mutanen da ke cikin jirgin ba, ko ɗaya bisa huɗu na mutanen dake cikin jirgin.
Saboda haka tun ruwan na shigowa a hankali a hankali, jirgi na Ɗan nutsewa a hankali a hankali, duk suka taru a sama suna jira, to sai suka ce, yadda za'ayi mata da yara su, su shiga kwale kwalen, ya kamata dama a ƙa'ida akan samu escape boat (kwale kwalen tsira) da yawa wanda zasu iya kwashe mutane abar kaya su nutse, to Amma a wannan sai ya zama kwale kwalen basu wadatar ba, sai suka ɗibi mata da yara, Amma a cikin matan ma akwai waɗanda suka ƙi yarda su shiga, suka ce sai dai su mutu da Mazajen su.
To suna tada wanda suka shiga kwale kwalen da wanda suke jirgi, anata Cewa toh sai anjima, suna nutsewa suna nutsewa aka ce kamar ƙarfe biyu da kwata na dare aka dena ganin dogayen fitilun da ke saman jirgin, shigen irin fitilun da akan sa na kan titi ɗinnan, an saka su manya manya, suna haske a saman jirgin to anga nutsewar su, kamar ƙarfe biyu biyu da kwata na dare suka nutse, don haka tun ana sai anjima wane, sai anjima wane, yana nutsewa duk gaba ɗaya suka nutse, har yanzu ana ta bincike na inda ya nutse da ɓuraguzansa da ake ta cirowa, wanda yake kawai muna iya cewa kawai wala alla wannan mai mugun maganar ya halaka su da mummunar maganarsa, cewa ko Allah bazai iya nutsar da jirgin ba, Allah ko ya nutsar dashi.
Koda yake Allah Ta'ala yana da dauriya, akan mashi fiye da haka kuma ya yafe,
Amma wani lokaci yakan faru haka nan, akwai mutane da dama da su kai ma Allah wannan takakka suka gamu da gamuwansu, akwai wani da ake ban labari (ina ga ma Alhaji Ɗanlami ne) ma ke ban labarin, waɗansu zasu yi bori ne sai ga hadari, zasu yi bikin bori, sai yace ai ko Allah bai isa ya hana wannan bikin ba, toh sai nan take tsawa tazo Dam! Ta tsaga shi biyu shi kaɗai kuma, irin wannan.
To wato ina batun dai jirgin Annabi Nuhu ne, Cewa shi ne farkon jirgi, don da babu shi ba wai don Ɗan Adam bai san yadda ake yin jirgi ba, sai domin dama ba zai yiwu jirgi ya ɗauki mutum ba, amma wannan lokaci bisa Wahayin Allah ya gaya ma Nuhu yadda zai sassaƙa jirgi, ya sassaƙa kuma su ma sai ya Zama abun dariya wajen mutane, don yana gaya musu Cewa za'ayi ruwan da zai shafe komai, ba wanda zai tsira sai wanda ya shiga wannan jirgin, su kuma basu san jirgi ba a lokacin, saboda haka abinda zasu ce yana yin gidan katako, to yanzu wannan ne za'a shiga? Wannan gidan naka na katakon ne za'a shiga à tsira ? Wai kuji abinda Nuhu yake cewa, wai ruwa zai bullo wai zai Mamaye ko'ina ba wanda zai tsira sai wanda ya shiga wannan gidan na katako da yake yi, sai a fashe da dariya.
Har ma awani lokaci wasu suna gidan waina ana tuyar waina ana basu burodi, (irin tanderu ɗin nan babba wanda ake gasa burodi, shigen wanda akan masa kamar tsariya a tura itatuwa masu yawan gaske, sama kuma asa wainar da ake toyawa ko gurasa) to sai wasu ma suna wurin suna saye, da yake an zo wasu suna sayen gurasan da zasu ci, wai ana Tattaunawa ana cewa wai kaji Nuhu wai ruwa zai bullo, to ta ina zai bullo? Wai zai mamaye ko'ina, to anan dai take acikin tsakiyar tandan wainar inda wuta ke fitowa, sai Allah ya tsago da ruwa kamar bututun famfo ya tashi sama suka ce, Mene zamu gani haka? To farkon ruwan kenan.
Daga nan kawai sai ruwan kawai ta ko'ina, sai zubawa a guje, suka je mai hawa tudu ya hau, mai hawa gida ya hau, tun ana hawa bene hawa na ɗaya hawa na biyu, wani ya hau har gida ya shanye, wasu su hau itatuwa itacen ruwa ya shanye, wasu suka hau kan tsaunuka duwatsu masu nisa, har na ƙarshe duwatsun duk ruwa ya shanye su ka-ka-kaf kowa ya halaka in banda Waɗanda basu ke cikin jirgin Nuhu, kuma kaɗan su kai Imani dashi wanda suka tsira.
Cikin waɗanda basu tsiran ba har da Ɗan Nuhu na cikinsa, wanda yace, ya ɗana zo ka hau tare damu, yace a'a zan hau wancan dutsen ne zai kare ni, Yace ba abinda ke karewa daga Allah Yau in banda wannan inba Rahamar Allah ba, amma shi Nuhu ance ya kasance bai san Ɗan Kafiri ne ba. Don haka ne ma Tabbatan Shi Nuhu bai sani ba Shine bayan da ruwa ya shanye komai, komai ya halaka, jirgi ya tabbata akan tsaunin Judi sai Nuhu (As) yayi Addu'a yace Ya Rabbi, ɗana yana daga cikin tsatsona Kuma Alƙawarinka Gaskiya ne, ya kuma za'ayi ace ainihin kuma yanzun kowa ya halaka sai wanda yake cikin jirgin ruwa na kuma ya zama ɗana ba shi aciki? Sannan Allah Ta'ala Ya gaya mashi cewa, shi ai bashi cikin Iyalinka, shi ɓata gari ne, shi bai yi aikin kirki ba, 'Innahu Laisa Min Ahlik' Innahu Amalun Gairu Salih' ana cewa ba halinka ake nufi, yawwa Ma'anarsa wato bashi acikin Addininka shi fajiri ne, to sannan ran nan Nuhu yasan ɗansa bashi tare dashi.
Ma'asumah Nigeria News Update
MNU034 SOKOTO
