SHIN DUTSEN HAJARUL ASWAD DAGA ALJANNA YAKE??

✍️ Aliyu Dahiru Aliyu

Alqur'ani bai zo da aya ko daya akan dutsen "Hajarul Aswad" ba amma hadisai sun zo da yawa akansa. Daga cikin mafi shahara da zan yi bayani a kansa shi ne wanda ya ce dutsen Hajarul Aswad na daga duwatsun aljanna. Duk da wasu daga malamai sun raunana shi wannan hadisi, ni zan yi bayani ne bisa daukar ingancin hadisin amma da karin bayani akansa.

Labarai kala-kala akan wannan dutsen marasa tushe. Daga cikinsu har da wanda ya ce wai da dutsen fari ne daga baya zunuban mutane suka mayar da shi baki. Wani kuma ya ce ai Annabi Adamu ne ya taho da shi daga Aljanna. Irin wadannan labaran ba su da tushe ingantacce.

Dutsen "Hajarul Aswad", kamar yadda Sayyidi Umar ya fada, dutse ne kawai akan kansa da bai da wani tasiri na zahiri sai kawai don girman da Allah ya bashi. Mun sani cewa masallaci ba shi da banbancin da kowane gini sai don kawai shi yana da wata kima ta daban ba irin ta sauran gine-gine ba. Hakan bai dauke cewar gini ne ba kawai da tasirinsa ya ta'allaqa ne da girman da Allah ya bashi ba wai don daga wani guri aka dauko ginin ba.

Wasu daga masana Kimiyya suna ganin cewa dutse irin na "meteorite" ne kawai da ya fado daga sama. To amma wannan ba lalle ya zama gaskiya ba saboda binciken Kimiyya na gwaje-gwaje (experiments) sai bayan karni na 16 ya fara bayan zuwan Francis Bacon. A baya kimiyya ta dogara da Falsafa ne ba da gwaje-gwaje ba. Aristotle babba ne a "Biology" amma ta hanyar falsafa ba ta Kimiyya ba. Ibn Sina babba a "Medicine" ta hanyar falsafar Galen da Hippocrates ba ta gwaje-gwaje a dakin Kimiyya ba.

 To waye ya auna "Hajarul Aswad" a "laboratory"? Sannan tarihi ya nuna Yazid bn Mu'awiya ya rusa Ka'aba a zamanin yakinsa da Ibn Zubayr wanda har dutsen abin ya shafa. To waye yake da tabbas din da yawa daga bangaren dusten bai tafi ba? A ma barshi cewar zancen da masana Kimiyyar suke fada gaskiya ne to hakan bai ragewa dutsen kima ba. Kowa ya san ginin Ka'aba na kasa da bulo ne amma shin ya ragewa dakin kima? Abin da ake kula da shi shi ne kawai girman da Allah ya bawa gurin sai ya zama "sacred".

Sai dai kuma a nan zai zamo maganar daga aljanna aka daukoshi ta zo da shakku idan muka dauki maganar a zahirinta. Amma cewar dutsen yana daga duwatsun aljanna ba ya nufin cewa wai daga aljanna aka daukoshi. Manzon Allah ya ce tsakanin minbarinsa da dakinsa wani dausayi ne daga dausayoyin aljanna amma ba wanda ya taba zuwa gurin ya dawo ya ce ya shiga aljanna. Haka duk inda ake zikiri nan ma Manzon Allah ya ce dausayin aljanna ne, amma na tabbatar ba wanda ya taba zuwa gurin ya dawo ya ce daga aljanna yake.

Magana ce ake da ma'ana ba da harafi ba. Kowace magana ana fahimtarta da asalin ma'anarta ba da harufan da aka fadeta ba. Babu wanda ya taba zuwa ya ce dutsen Hajarul Aswad hannun daman Allah ne duk kuwa ga hadisi ya zo akan cewa dutsen "hannun Allah ne da yake gaisawa da bayinsa"! irin tunanin cewa dutsen daga aljanna ya fado shirmen tunani ne na "literalism".

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post