MARTANI GA JARIDAR DAILY TRUST AKAN WASU KARAIRAYI DATAYI KAN DAURA, DA KUMA SAKON KAR TAKWANA GA WASU MASU KARANCIN TUNANI A CIKIN MUTANEN DAURA.


✍️ Musa Ibrahim Daura
29-9-2019.


A Jiya ne 28-9-2019 jaridar nan ta turanci mai fitowa a kowace rana mai suna Daily trust ta ruwaito wani labari mai taken FOR THE SAKE OF PRESIDENT BUHARI, wato ma'ana Don kyautatawa shugaba Buhari.

Labarin ya kumshi karya da gaskiya, wannan ne yasa naga ya dace in mayar da murtani ga jaridar, duk da bada Hausa tayi rubutun ba, amma na zabi inyi martanina da Hausa domin zaifi gamsar dani yakuma gamsar da masu karatu.

A cikin labaran data ruwaito na gaskiya sun kumshi WASU aiyuka data lissafo cewa anyiwa Daura da kuma Wanda ake kan hanyar yimana, tabbas mun samu wannan dama a wannan mulki, to amma kada jaridar ta manta mu mutanen Daura mun cancanci fiye da abin data lissafa kasantuwar shugaba buhari Dan' mune, kuma shi da' nagari kullum kokari yake yaga ya sakawa mahaifansa da kyakkyawan sakamako. Bayan haka gwagwarmayar siyasar da mutanen Daura suka sha tare da dandana bakin cikin shekara goma sha biyu, ana mana azaba, saboda mun kasance yan'adawa, babu wani aiki daya tal da za'a nuna a tsawon shekara goma sha shidda da PDP tayi tana mulki Wanda mutanen Daura suka karu dashi daga gwamnatin tarayya. BABU SHI.

Saboda haka ko bisa wannan dalili yakamata shugaba buhari ya shafe mana wancan bakin cikin da takaici, kuma alhamdulillahi muna godiya da alkhairan da muka samu a wannan gwamnti da mutanen Daura suka bauta wajen ganin tabbatuwar ta. Muna kuma neman kari idan zai samu. A HANNU DAYA KUMA

KARYAR DAKUKA TAFKA.

Na farko dai a najeriya muna da ministiri a kalla guda ashirin da hudu ko da Biyar, amma a cikin karyar da kukayi kunce kusan babu ministirin da batayi aiki a garin Daura ba, Wanda idan da gaskiya ne a kalla zaku zana aiyuka ashirin na ministiri daban daban, amma kun lissafa aiyukan da basufi na ministiri biyar ba, saboda haka wannan magana tun daga nan, tazama KARYA.

Sannan a wata karyar ta daban kunce kusan duk inda aka duba a Daura za'aga Manyan motocin kamfanoni na aiyuka guri guri da kuma yadi yadi na masu aiki wadanda ke gudanar da aiyukan da akeyi, to amma sai kuka kasa fadin unguwannin da wadannan kayan aiki da kuma yadin masu aikin suke, Wanda kuma a zahiri babu, idan ma akwai bazai wuce daya ba Wanda aka fara wani aiki kwanan nan. DON HAKA WANNAN MA KARYACE.

Kunyi bayanin cewa an gama aikin sabke Dam kuma har yana ba Daura ruwan sha Lita  miliyan daya a kullum, a ina ne akayi (connecting) hada ruwan, kuma daga ina aka jawo pipe din? Kamata yayi Ku fadi inda TANKIN RUWAN YAKE, SABODA HAKA WANNAN ZANCEN MA KARYA CE KUKA SABKE WA DAURA.

Haka kuma kunce an Gina Santa ta NDE Wadda taci zunzurutun kudi naira milyan tamanin da hudu(#84,000,000) har ma ta yaye dalibai na farko mutum Dari, shima kun kasa fadin inda aka Gina santar kamar yadda kuka fadi ta zango road, ITAMA WANNAN SANTA DA KUKA FADI KARYA CE BABU ITA.

Kunce a farkon mulkin wannan na buhari, an Gina hanyoyin ruwa(drainages) an kammala, masu tsawon kilomita 21, wannan ma karya ne, domin aikin da akayi na hanyar ruwa bai wuce kilomita biyar ba ya zuwa yanzu. DON HAKA NAN MA KUNYI KARYA.

Kunce yanzu haka ana nan anayin wani aiki na hanyar ruwa da tituna na kolomita arba'in a cikin garin Daura, shima Baku fadi guraren aikinba, mu kuma mutanen Daura bamuga inda akeyin aikin da yakai haka ba, Don haka shima wannan labarin kamzon kurege ne.

Kunce ana kan aikin titi Wanda zai zagaye Daura (Ring road) na tsawon kilo mita tamanin 80 - 90km. WANNAN ZANCE SHIMA SHACI FADI NE BABU SHI BABU ALAMARSA.

Haka nan maganar tagwayen hanya daga katsina zuwa Daura, dakuma maganar titin jirgin kasa duk labarine, babu su babu alamarsu a zuwa yanzu da muke wannan magana.

A taikaice dai labarinku kashi siitin cikin Dari duk zuki ta malle ce, inji yara! Saboda haka masu karatu yakamata Ku dauki izina daga nan, Ku daina gaskata duk labarin da kuka gani a jarida ko kuma a Facebook, matukar Baku da gamsashiyar shaida akan lamarin.

SAKON KARTA KWANA GA MASU KARANCIN TUNANI NA CIKIN DAURA.

Wasu daga cikin mutanen Daura, manya da kanana masu karancin tunani kullum.suna ihu wasu na zage-zage cewa mi akayi musu, basuga komai ba, to kunji dai yadda wasu na waje suke kallon Garinku, suna ganin babu inda aka fifita akewa aiki kamar Daura. SABODA HAKA WASU NA ZARGINSA (SHUGABAN KASA)YANA KYAUTATA MUKU, KU KUMA KUNA SUKARSA DA ZARGINSA CEWA BAYA MUKU KOMAI. To hausawa dai na cewa KADA ALLAH YA KAWO RANAR YABO.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post