Tuhume Tuhumen Da Amurka Da Saudiya Ke Yiwa Iran Kan Harin Aramco Ya Daɗa Fitowa Da Karfin Iran a Fili. Manjo Janar Husaini Salami (IRGC)
Yanzu muna iya fadar cewar "Amurka ta fitar da rai kan maganar kai wa Iran harin soja,ta koma yakin kame kame da tuhume tuhume da farfaganda.
Yanzu firgicin Amurka da kawanta kan Iran ya kai cewar 'duk abin da ya samesu to Iran ce tayi musu. Kai, ta kai ma ko hatsari aka yi saboda rudewa sai Amurka ta tuhumi Iran.
Ni ban san cewar ashe Iran ta zama hamshakiyar kasa mai karfi irin haka ba,ta yadda ko menene ya faru ga Amurka da kawayenta to Iran ce, Inji Janar Salami.
-
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya ce bayan Amurka ta zargi Iran da hannu a hare-hare na baya-bayan nan wanda Yemen ta kai kan matatun man Saudiyya. Sai kuma aka fara jin wasu karin tuhume tuhumen suna biyo wa baya,ashe nan gaba kadan ko mota ce ta fadi zasu iya tuhumar Iran da kayar da ita,domin basa jin kunyan yin karya
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sami irin wannan karfin wanda makiya suke da shi na sanya Iran a zargi a kan kowane irin lamarinsu in ji Manjo Janar Hossein Salami a lokacin da yake ganawa da wasu sojojinsa a lardin Arewa maso Gabashin Iran.
-
Mun bar makiyanmu a cikin duhu, ba tare da wani zaɓi a fagen fama ba, saboda Iran ta rufe dukkan hanyoyin ta'addanci,kuma gashi su ba zasu iya zabar yin gaba da gaba da mu ba,sai suka zabi yakin farfagandar Rediyo da Talbijin,in ji kwamandan rundunar IRGC.
Ya kara da cewa, rundunar sojan Iran tana kare iyakokinƙasarta sosai-da-sosai kuma tana yin taka tsantsan don ganin cewa babu wata damuwa ko barazana daga abokan gaba.
Har ila yau Janar Salami ya yi karin haske game da shirin da IRGC keda shi na ganin an warware matsalolin tattalin arzikin cikin gida da inganta jin dadin jama'ar Iran, yana mai cewa irin wannan nauyi yanzu shine ya hau kan IRGC,domin wannan ma tamkar yakin ne,amma na tattalin arziki.
-
Nasir Isa Ali
Tags:
Labaran Duniya