DOMIN KAI DA UWAR GIDA PART 1

DOMIN KAI DA UWAR GIDA 


YA KAI MAI GIDA SHIGO DAGA CIKI KA JIYA... 
WANNAN MAUDU'IN NAKU NE.. 


Ku dai ku kasance da wannan shafin mai Albarka. 

Aduk 6angaren da muka dauka mukan danyi qoqarin ta6a wasu abubuwane kawai da muka san zasu iya amfanarwa, sauran kuma mutattara mu barwa mai karatu ya qara bincike,


Amma yau zamu farane da bayanin Dr Gaylord Heuzer a littafinsa na (Algaza'u yusni'ul Mu'jizaat)inda yake cewa:- Haqiqa abinci yana taka rawa wajen tabbatarwa maza da mata lafiyarsu ta6angaren saduwa, saboda haka ne ya zama wajibi ayi bincike ta wannan 6angaren.
Ba shakka rauni wurin saduwa yakan baqantawa ma'aurata rai wani lokaci yakai ga saki ko juya wa juna baya, alhali abincin da muke ci zai iyayin maganin wannan matsalar matuqar anyi amfani dashi ta fuskar da ta dace, sai sha'awar mutum ta dawo kuma yasa mijin yaji dadin saduwa.
Yace "Zahiri Vitamin B yana qara kwadayi da samun qarfi wurin saduwa sama da sauran kashekashen abinci, adon haka ne ya zama dole akan wadanda suke da rauni, da su mai da hankali wajen neman wannan nau'in na Vitamin B.
Bulgariyawa sukan dauki kindirmo amatsayin abincinsu, shi yasa kusan kowa yasan sukan tsufa tare da qarfin su na saduwa.
 Da yawa wasu Harmones din suna 6oye ne acikin proteins, shima kenan dole mai rauni ya nema,
masamman Protein din da aka samu daga dabbobi, shikam yafi saurin bada abinda ake nema sama da wanda aka samu daga 'ya'yan bishiyoyi ko ganyayyaki.

       Vitamin A

yakan taimaka wa ma6u6ugan ruwan namiji da kuma marainansa, kuma yakan tsarawa mace al'adarta, da haka ya wajaba a riqa samun sa sosai ta hanyar ganyayyaki, 'ya'yan bishiya ko juice din gida ba na kanti ba.
Matan da suke fama da matsala, wadanda basa sha'awar saduwa, sannan al'adarsu ta rikice musu, wani lokaci takan hada musu har da ciwon kai, kenan suna matuqar buqatar Vitamin C, qarancinsa yana iya qara kwararan jini.
          

       VITAMIN E


kuwa, shi ake kira na ya6anya, ba a ganin tasirin sa sai in anyi amfani dashi da dan dama, ya kan yi maganin cutar rashin haihuwa ta 6angaren maza, domin yakan magance tsinkewar maniyi.
Mace kuwa yakan yi mata maganin radadin haihuwa, ya kanyi kuma maganin saurin kawowa,
akan sameshi ne a alkama, ko man alkama, ko latas, da sauran korayen ganyayyaki, akan sameshi ma asauran hatsin da ba a surfe ba, don galibi ana fitar dashi a surfe ko a wajen tankade.
         Dr. Lord yaci gaba da cewa ana samun rauni ne wajen saduwa adalilin qarancin kyakkyawan abinci,
amma ba tsufa ba, wasu ma suna ganin qarfin da maza suke dashi a shimfida dalili ne na lafiyar jikinsu, 
Abinci yakan taimaka ga lafiyar jiki, da cigabansa, yakan mayar wa mutum kuma abinda ya rasa alokutan aiki, kenan za a iya kasa abincin zuwa gida 3.



Akwai mai gina jiki, wanda yake taimakawa ha6akar jiki, da mayar wa mutum abinda ya rasa,
wannan kuwa yana qunshene a Proteins, Vitamins da Salts.
            Wannan Protein din yakan kasu zuwa gida 2, gwargwadon yadda aka samo shi, akwai na jikin dabba, kamar nama da kashe-kashensa, qwai, madarar shanu da abubuwan da aka cira daga cikinta, akwai kuma Protein na tsirrai, kamar dai waken fatauci, farin wake, da wanda ake kira pea, da adas(lentils), alkama, da shinkafa, sha'ir, da sauransu, abubuwan da suke qara jin dadi sun hada da 'ya'yan bishiya, dankalin turawa, sukan qara nishadin jiki, su qarfafa hanta wajen yin aikin da ya dace, wannan kuwa idan an sami ragowar abinda jiki yake buqata ne sai ya mai dashi sifar(Glycogen)wanda zai yi amfani dashi wajen juya shi zuwa sukari ayayin jin yunwa ko azumi.
  Abinda yasa na dauko wannan bayanin don mutum yasan irin abubuwan da zasu yi daidai da lafiyar jikinsa, wani hadin ko kana da rauni wurin saduwa kuskurene ka hada shi, masamman masu fama da cutar sukari, wadannan da yawa sukan sha wahala wajen bin qa'idoji, a zahirin gaskiya basu da buqatar kwatanta wasu abubuwa da yawa daga cikin nau'o'in abincin da zamu fadi,  in mutum bashi da lafiya kuma yana da likita, zan bada shawara kan cewa ya tuntu6i likitansa kan irin abincin da yake so yaci, don kaucewa karo da nau'in abincin da baiyi dai-dai da lafiyarsa ba.

da yawa masu fama da cututtuka sukan sha wahala saboda raina shawarwarin likitocinsu.



Zamu dakata a anan sai a fitowa ta gaba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post