Tare da Salisu Mika’il 07032202642
Kuskure wani abu ne da ya zama bangaren rayuwa. Zai yi wahala a ce ga wani mutum da bai taba aikata wani kuskure a rayuwarsa ba. Don haka ba wani bakon abu ba ne don ka aikata kuskure a lokacin da kake gudanar da harkokin rayuwarka. Bambancin da ke tsakanin mutane shi ne yadda suka ci gaba da gudanar da rayuwarsu bayan sun fahimci kuskuren nasu.
A lokacin da wani yake yanke kauna, ya rasa karsasi, zuciyarsa ta kuntata, ransa ya dugunzuma, natsuwa ta kaurace masa, ya rasa inda zai sa kansa. Wani kuma sai ya natsu, ya kwantar da hankalinsa, ya yi nazari sosai don ganin wane irin darasi mai amfani zai samu daga wannan kuskuren, kuma wace hanya zai bi don ganin ya fitar da kansa daga inda ya samu kansa a dalilin wannan kuskuren, kuma wace hanya zai bi don ganin ya kauce wa aukawa cikin wani kuskuren?
Wani yakan mayar da kuskure ya zamo tarnaki a gare shi. Ya rika tuna asara da rashin da ya yi a dalilin wannan kuskuren. Ya gaza mancewa da abubuwan da suka faru a baya, rayuwarsa kullum a hargitse ba natsuwa. Ya kasance kullum cikin zargi da tsangwamar kansa. Hakan ke sanya mummunan tunani ya yi tasiri a zuciya, ya haifar da mummunan yanayin da zai sa a rika kallon rayuwa a birkice, a jirkice, ta karkatacciyar mahanga.
Babbar ribar da mutum zai ci daga kuskuren da ya aikata shi ne, ya koyi darasi domin gyara da inganta rayuwarsa a gaba. Kuma ya yi kokarin nusar da mutane don su fahimci illolin da suke cikin aikata irin wannan kuskuren don kada su auka ciki. Gaskiyar magana a mafi yawancin lokuta kuskure yakan zamo mana alheri, domin mutane masu yawa nasarorin da suka samu a rayuwa suna da alaka ta kai tsaye da kura-kuran da suka aikata a baya ko kuma kura-kuran da wasu suka aikata.
Don haka duk lokacin da ka aikata wani kuskure, to dama ce ka samu ta kyautata rayuwarka, don ta samu inganci fiye da baya. Kada ka bari damuwa da bakin ciki su hana ka amfanuwa daga darussan da ya kamata ka samu daga wannan kuren. Idan ka bari hakan ya auku, to za ka yi asara biyu: Na farko dai ba za ka iya tariyo rayuwarka baya don ka goge wannan kuskuren ba. Na biyu kuma damar da ka samu ta koyon wani darasi mai amfani daga kuskuren don gyaran gaba za ta subuce maka.
Matukar kana numfashi, to kana da cikakkiyar damar da za ka gyara rayuwarka. Tuntube a lokacin da kake tafiya ba ya nufin tafiyar ta zo karshe. Nuni ne a gare ka cewa, wannan takun da ka yi akwai mishkila, don haka ka natsu ka daidaita don kada nan gaba ka kara karo da wani dutsen da zai iya fasa nama ko ya karya kashin yatsan kafar. Kada ka yarda tuntuben nan ya zamo shamaki tsakanin ka da muradanka. Maimakon haka ana so ka mayar da shi ya kasance tsani gare ka, wanda za ka taka don isa ga biyan bukatarka.
Kada ka sare, kada ka gajiya, kada ka rushe kyakkyawan fatan da kake da shi, don ka hadu da wani cikas a dalilin wani kuskure da ka aikata, maimakon haka, yi kokari ka sake jan damararka, ka kara kyautata niyyarka, ka fuskanci rayuwa bisa kyakkyawan zaton cewa alherin da ke jiranka a gaba mai tarin yawa ne, yawan da bai kamata ka bar shi ya kubuce maka don wani tarnaki yana neman dabaibaye ka ba.
Yi kokari ka kwance dabaibayin nan, ka kara gaba don riskar babban rabon da ke jiran ka. Ka tuna, mikewarka bayan faduwar da ake zaton ba za ka iya tashi ba, za ta yi matukar faranta ran masoyanka, kamar yadda kuma za ta yi matukar turmuza hancin makiyanka. Ka ga ke nan ko don ka faranta wa masoyanka rai, ya zama dole a kanka ka mance da abin da ya faru a baya ka fuskanci gaba.
Duk lokacin da ka fahimci ka yi kuskure, yi kokari ka gyara. Kada tunanin za a yi maka dariya ko za a ga gazawa da gajiyarka su sanya ka kafe a cikin tabo da lakar kuskuren. ‘Barnar da za ta auku gare ka sai ta fi muni a kan dariyar da kake zato da tsoron za a yi maka. Gujewa barna ba tsoro ba ne, jarumta ce. Don haka kada ka yi girman kai ko dagawa wajen dagewa a kan kuskure, don kawai takama da alfahari da tunanin kada a ce ka ba da maza. Duk wanda zai zuga ka, ka tabbata a kan kuskure, ba mai kaunar ka ba ne. In lamurra suka dagule, guduwa zai yi ya bar ka a cikin tsomomuwa. Sannan zai iya shiga cikin masu yi maka dariya ana zagin ka, bayan ya ingiza ka.
Mutumin da ya yi kuskure, ya fahimci kuskurensa, ya yi nadama, ya juyo don gyara, to ba karamin jarumi ba ne. Ya cancanta a yaba masa, a karfafa masa gwiwa, kuma a taimaka masa wajen ganin ya kyautata ayyukansa na gaba. Wannan zai sa ya samu kwanciyar hankali da natsuwar fuskantar kulen da ke gabansa. Sabanin abin da ke faruwa a yau, da zarar mutum ya aikata wani kuskure, sai a tsane shi, a kyamace shi, a guje shi, a rika tozarta shi. Bayan kuma dukkan mu ba mu fi karfin aikata irin wannan kuskuren, ko ma wanda ya fi shi muni ba. Hakan ke jawo a maimakon a tsamo mutum daga halaka, sai a dada tura shi cikin halakar. Maimakon a taimake shi sai a cutar da shi; maimakon a gyara shi, sai a bata shi; maimakon a shiryar da shi, sai a tabar da shi.
To, amma ko da a ce ka samu kanka a tsakanin irin wadannan jama’ar, kada ka bari wannan mummunan halin nasu ya kange ka daga manufarka ta son gyara kuskurenka. Mance da su ka fita sha’aninsu, ka mayar da hankalinka da tunaninka ga duk wani abu da ka san zai taimake ka gyara kuren. Ka kaurace wa irin wadannan mutanen in zai yiwu, ka kusanci wadanda za su tallafa ma da shawarwari na karfafa gwiwa, wadanda burinsu shi ne su ga ka gyara kurenka, kuma ba ka maimaita wani kuskuren ba.
Wani abu mai muhimmanci kuma shi ne, kada ka rika zaton girman kuskuren ba zai bari ka iya rayuwa mai amfani a gaba ba. Sam ba haka ba ne! Akwai wadanda suka aikata laifuka da kura-kurai masu girma da muni fiye da kai, amma da suka gane, suka yi nadama, suka tuba, suka kyautata ayyuka, sai aka mance da wancan kure da laifin na baya. Sabuwar rayuwar da suka gina wa kansu, sai ta zamo ruwa da sabulun wanke datti da kazantar rayuwar da suka gabatar a baya. Maimakon kallon su a matsayin masu laifi sai aka dawo ana masu kallon salihai managarta.
Don haka kada ka yanke kauna daga samun ingantacciyar rayuwa, don kawai wani kuskure da ka aikata, komai girma da munin kuskuren, domin ba kai ne na farkon aikata irin wannan kuren ba, kuma ba kai ne na karshe ba. Bambancin kawai ya ta’allaka ne a kan abin da mutum ya aikata bayan ya gane kuskuren.
An buga a ALMIZAN ta 1409
Tags:
Daga marubata
