SU MABIYA GIDAN ANNABI BASA YANKE KAUNA GA NASARA
"Shiyasa su mabiya gidan Annabi basa fidda rai basa yanke kauna kullum suna sauraran nasara ne da taimako daga Allah (swt) saboda alkaqari ne na Allah a bakin Manzon Allah (S).
Amma Alhamdulillahi a wannan zamanin namu muna ganin haske mun fara ganin wannan Annabta ta tabbata.
To wannan kenan, Wannaan wanda muke bi dinnan, wanda muke taronnan saboda shi; shi wanda yazo mana ko ya shimfida mana ingatcciyar akida wacce da itace ake samun shiga Aljanna, da ita ce a tsallakewa da ita ce ake sanin Allah (Swt).
Ibni Abul hadid Al-mu'utazali yana cewa; Ba'a san Tauhidi hakikanin Tauhidi ba, (Na'am tauhidi shi ne
sanin Allah da kadaita shi, amma Filla fillar Tauhidi) wannan daga bakin Imam Ali aka sani, kamar ba Allah hakkokinsa, abinda ya koru daga gareshi da wanda ya wajaba ko ja'izi wannan daga bakin Imam Ali aka fara ji.
Dukkan Mazhabobin Tauhidi Na Ash'ariyya ne, na maturidiyya ne ko na ma wace makaranta ne to daga bakin Imamu Ali aka ji. Almajiransa ne sukayi rassu kowwa ya dauki makarantar da yake so, amma dai daga bakinsa aka fara ji, yace:- Da ace mutanan da ya rayu dasu sun san Tauhidi kammar yadda Imamu Ali ya sani, da sunyi bayani ko da anji daga garesu ko an rowaito amma ba a sani ba sai a gunsa. To yaushe zamu bar wannan mutum mu tafi ga wasu mutane".
- Shaikh Yaqoub Yahya Katsina, a wani bangare na jawabinsa Na Ghadeer da yayi a ranar Litinin 19,8,2019 dai-dai da 18,12,1440 a Markaz Katsina, Bin Yaqoub Katsina Ya rubuta.
id_el_Ghadeer
#FreeZakzaky
![]() |
Sheihk yakubu Yahaya katsina kenan alokacin dayake jawabin ghadde |

Tags:
Munasabobi