JAMI'AN YAN SANDA NA SHIRIN YIN KISA.

JAMI'AN YAN SANDA NA SHIRIN YIN KISAN KIYASHI A KAN 'YAN UWA MUSULMI A RANAR TALATA .

Ranar Talata mai zuwa 10/9/2019, ta yi daidai da ranar 10 ga Almuharram 1441H a mafi yawan kasashen Duniya. Ko da yake rannan a kirgen Musulmin Nijeriya ta yiwu 11 ga wata ne, amma don ya zama an dace da al'ummar Duniya, yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky za su gabatar da taruka da Muzaharorin Juyayin Ashura ne a ranar Talata din a dukkan birni da kauyukan Nijeriya kamar yadda suka saba gabatarwa fiye da shekaru 25 da suka gabata.

Kamar yadda a watan Afrilun 2017, gidan rediyon DW Hausa ya fitar da wani rahoto mai dauke da bayanin Yariman Kasar Saudiyya, Muhammad Bin Salman da yake tabbatar da cewa su (Saudiyya) ne suka ba da kwangilar kawo karshen Shi'a, abin da ya kira tasirin Iran a Africa, musamman a Nijeriya, inda ya nuna karara cewa su suka sa aka dirarwa Shaikh Zakzaky ake kuma tsare da shi tare da kokarin ganin bayansa da da'awarsa.

Juyayin Ashura wanda mafi yawan al'ummar Musulmi, musamman mabiya Mazhabar Ahlulbait (AS) da kuma 'Yan Darikun Sufaye da ma Wasu Ahlussunah na gaskiya suke gabatarwa a duk shekara don taya jaje ga Manzon Allah (S) akan kashe jikokinsa da sahabbansa mutum 72 da rundunar Yazidu Dan Mu'awiyya suka yi a Karbala, yana daga abubuwan da Gidan Sarautan Wahabiyanci na Saudiyya basu son wanzuwarsa, don haka suke fitar da miliyoyin Daloli a duk shekara don a ga an dakile yiwuwar Juyayin a kowane yanki a fadin Duniya.

Da yake sun samu wawaye, dolaye, sakarkaru, shahashun mutane, wanda gumma dabbobi da su a Nijeriya, sun yarda musu su basu kudi, su biya su, su kashe musu yan Kasar su da karfi da yaji. A bana ma, Gwamnatin Mohammadu Buhari na da shirin afkawa Muzahararori da tarukan Ashura a dukkan garuruwan da za su gudana a fadin Nijeriya.

Gwamnati na kokarin yin Ta'addanci a kan 'yan uwa Musulmi ne ta hannun babban shugaban rundunar yan sanda na kasa, Mohammadu Adamu. Abin mamaki, yadda yake amsa sunan Muhammad ya nuna kamar shi Musulmi ne, amma dai ya yarda zai kashe kuma zai ba da umurnin a kashe al'ummar Musulmi masu taya Manzon Musulunci jaje a wannan tsakanin. Ga dukkan alamu bai yi imani da ayar Allah ta cikin Alkur'ani da ke cewa: "Kuma wanda ya kashe Mumini da gangan, sakamakonsa wutan Jahannama ne, zai daumawa a cikinta, kuma Allah Ya yi fushi da shi, kuma ya tanada masa azaba mai radadi."

Abin takaici ne sosai, a yayin da kullum mahara da yan bindiga kan shiga garuruwan Musulmi su dirar musu, su kashe su, su kona dukiyarsu, su sace su, su ma matansu fyade da cin mutunci kala-kala, jami'an tsaron Nijeriya ba kawai yan sanda ba, har Sojoji sun kasa yin komai a kan wannan, amma kullum mafarkinsu shine za su gama ne da wasu mutane da suka ce za su yi Musulunci ne a irin fahimtar da suka masa, wanda cikinsa babu taba dukiya ko ran kowa, face ma taimakon al'umma da nuna musu tauyasawa ta hanyar basu gudummawar abinci, kudi, gyaran muhalli da kyautar jini a asibitoci akai-akai.

Amma daga mummunan shirin da jami'an tsaron Nijeriya suke yi akwai cewa za su yi amfani da Muzaharorin Ashura, a yayin da ake yi, su bayyana karara su bude wuta a kan masu Muzaharar, su kashe na kashewa, su kama na kamawa, sannan daga nan su fara bi suna kokarin kama wadanda suke kira manya ko shugabannin Harkar Musulunci wanda sun ta kokarin su kama su kafin yanzu, ya gagara saboda gudun yadda al'umma za su zarge su da ta da zaune tsaye. Suna nufin daga nan za kuma su samu damar nuna cewa ana rikici ne da Shi'a, sai su fara kokarin rushe muhallan tarurrukan Shi'a din. Ba mu a karya bane ko hasashe, haka suka tsara, kuma ya kamata al'umma su sani, in har suka ga hakan, to su sani cewa dama an shirya bin matakan ne ake aiwatarwa yanzu.

Ya kamata Gwamnatin Nijeriya ta yi nazari, ta san cewa ba za ta samu goyon bayan al'ummar Nijeriya, musamman ma Musulmi da wadanda ba Musulmi ba da yunkurinta na kashe 'yan uwa Musulmi ko kama su ko rushe muhallan taruka da ibadunsu. Domin kuwa sam Shi'a ko Harkar Musulunci bashi daga matsalar al'ummar Kasar nan, ba Harkar Musulunci ke kashe su da sunan Boko Haram ko Barayin Shanu ko Masu garkuwa da mutane, ko yan ta'adda ba. Ba Harkar Musulunci ce taki samar musu da tsaro da kula da lafiya da dukiya da rayukansu ba. Ba Harkar Musulunci ce ta jawo musu tsadar rayuwa da tashin kayan masarufi da matsanancin talauci da rashin daɗin rayuwa ba. Ba ita ta rufe musu iyakoki kasa ta hana shigo musu da abinci amma ta bari ana shigo da makaman kashe su ba. Duk wadannan gwamnati ke yinsu, kuma al'umma na neman mafita daga gare su ne a wajen gwamnatin. Don haka ba abin da ya shafe su da Shi'a ko Harkar Musulunci.

Ya kamata ta sani, Shi'a din nan, ko kuma yan uwa Musulmi na Harkar Musulunci, bangare ne na al'ummar Nijeriya, duk wanda kuka kashe a cikinmu, shi dan uwa ne ga sauran al'ummar Kasar da dukkan fahimtunsu, ba daya daga cikinmu face da ne, ko dan uwa, kani ko wa, ko ba a ga sauran al'ummar Kasar nan. Don haka mu ba wasu mutane ne na daban ba, face bangaren al'ummar kasa. Kuma duk abin da ya same mu ya samu al'ummar Kasar, kuma da ku za su yi Allah wadai.

Muna addini ne na Musulunci a yadda muka fahimta, kuma wani dan mace bai isa ya hana mu aiwatar da Musulunci a matsayin addinin da Allah Mahaliccinmu ya yarje mana mu yi ba, kuma a bisa fahimtar da muka masa kan yadda aka saukar da shi da yadda aka bar mana amanarsa a wajen Ahlulbait (AS) za mu gabatar. Da yardar Allah, kamu, kisa ko dauri da rushe gidaje da duk nau'in cutarwa ba zai kawo karshen al'amarinmu ba, kamar yadda kashe Imam Husaini (AS) da datse kansa bai kawo karshen Ahlulbait da Mazhabar su ba tun shekaru kusan 1400 da suka wuce. Don haka in kun sa ba makawa za ku yi ta'addanci, ku yi mafi muninsa, InshaAllah sharri baya samun mumini. Kuma mutuwa a gare mu al'ada ce, Shahada kuwa karama ce a gare mu. Jarabawa kuwa ita ce gadon da Annabawa da A'imma (AS) suka bar mana.

— Saifullahi M Kabir
8/1/1441H - 8/9/2019

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post