SAI WASU SUN SADAUKAR ZA'A CECI WASU
Ma'asumah Nigeria News Update,
Sadaukarwa Ce Mafitar mu Na Sheikh Zakzaky
Wannan karin Magana ne, hikima ce ta mutane, abinda hakan ke nufi shine, sai wasu sun sadaukar da kansu domin ceton wasu, sannan za'a iya ceton wasu ɗin, kuma wannan Shine ainihin koyarwar Addini, shine koyarwar Sadaukarwar Annabi Ibrahim (As) wannan kuma shine Sadaukarwar Imam Hussein (wanda bada jimawa ba zamu shiga lokacin jajen na Ashura) wanda shi ya bada ransa,
Kuma à '' version'' ɗin kiristoci, shine Sadaukarwar da Isah Almasihu yayi, Shiyasa ma Addininsa ya wanzu, in ba haka ba da an manta anyi shi, amma sai ya zama ya sadaukar da ransa, Sadaukar da ransa shi ya wanzar da Da'awarsa, mu ma haka muke gani, Imam Hussein yayi kama da Isa ta wannan Sadaukarwar, muna Cewa shiya ceci Musulunci da jininsa, wanda mutane basu ganewa sai anyi musu bayani cewa lalle shi ya ceci Addinin nan, domin da ba don shi ba, da ba Addinin,
Yanzu ma dai akwai wani irin Addini da ake dashi wanda yake, zamu iya kiransa kamar makami na mulki, instrument na samun matsayi, wannan daban, shi kuma Addinin Allah tsantsa shine Imam Hussein (As) ya bada ransa wajen cetonsa, domin da ba don haka ba, za'a ɗauka da sarauta da Addini abu ɗaya ne, amma sai shi bai bi sarautar ba, ya tsaya kan Addinin, cewa ashe ba abu ɗaya bane.
Na'am wani lokaci Addini da sarauta suna iya tafiya tare, amma in sun rabu Addini za muyi, amma in suka gwamu a mutum ɗaya Masha Allah, yanzu dai mun san sun rabu, sarauta da Addini abubuwa daban daban ne, ko da ko sarautar anyi ta da sunan Addini.
Wannan Sadaukarwa ce da muke tunawa a lokacin Sallar Layya, to har Wala Yau mu kuma yau Asabar da ma gobe Lahadi akwai wani abin tarihi daya cancanci duk su zama Idodi bayan idin Ghadeer bayan Sallah da muka yi shi kuma ranar 18 ga watan Zulhijja, wanda wannan Manzon Allah ya ɗaga hannun Magaji sa Yace "In Nine Shugabanka, to wannan ne Shugabanka bayana"
To kuma mutane suka samu fitinuwa akan cewa ya akayi shi wannan mutumin bai zama Shugaban ba bayan Annabi?? Ta nan suka kasa gane cewa akwai Shugabanci irin na Annabi, na Addinin Annabi, akwai kuma sarauta na mulkin duniya, don an raba, Shugabancin da Annabi yayi wanda ya ɗoru akan saƙon Addininsa, to shine Magajinsa yaci gaba Da, zaku ga akwai waɗansu hotuna an nuna wani ya ɗaga hannun ɗaya, Ɗaya ana nufin Annabi ne, ɗayan Ana nufin Ali ne, yace "Man Kuntu Maulahu, Fa haza Aliyun Maulahu, ma'ana wanda na zama nine Shugabansa to wannan Ali shine Shugabansa bayana,
To Ali ɗin shine ya zama Shugaba na Addinin da Annabi yazo dashi, amma kasantuwar anyi Shugabanni na siyasa, sai ya zama an bambanta, duk da wasu suna ganin shugaban siyasa Shine na Addinin, amma mu a wurin mu, Addinin da siyasar suna iya haɗuwa, kuma suna iya rabuwa, in sun haɗu Masha Allah, in sun rabu, Wanne zamu bi? Mu Addini Muke bi, saboda haka mu Ali Muje bi, saboda haka ranar da Annabi ya ayyana wannan ya zama ranar buki a wurin mu, har ma yafi Babbar Sallah muhimmamchi a wurin mu, domin shi ya nuna ina ake bi bayan Annabi, ina ne zaka bi ka samu Addini bayan Annabi? Don wannan Ali ɗin Shine Halifan Annabi a tafsirin Alƙur'ani, shi zai fassara maka littafi, kuma shine ya nuna Hikimar wanzar da saƙon Annabi har ya zuwa ƙarshe domin Limami bayan Limami, ba Ali kawai ya gabatar ba, Yace bayan Ali sai wane, bayan wane sai wane har zuwa Ƙiyamus Sa'a, kowane lokaci akwai Hujjar Allah adoron ƙasa, wanda yake ta nan ne Allah zai yanke wa Mutane hanzari, don akwai Hujjarsa a kowane zamani.
Ma'asumah Nigeria News Update
MNU034
Tags:
Jawaban Sheikh Zakzaky
