Shawarwari Ga Yan Media Musamman Wakilan Shafin Ma'asumah...(M.N.N.Updates)

Musa Hassan Shinkafi Daga dama tare da Mas'udu dan Masani Daga Hagu A taron karawa juna sani na shafin Ma'asumah a garin katsina

Daga Editer (MNU02)


______________________

ASSALAMU ALAIKUM WARA HAMATULLAH.


Ina farawa da gabatar da Uzuri ga Yan uwan aiki akan Rashin Zuwana Cikin Cikakken lokacin da akasa.

Hakan ya faru ne Saboda Zazzabi da nake dan fama dashi kwana biyu yanzu hakama Saida nasha Allura naiya kawo nan, akan wannan dalilin ne Zaadan samu Tawayar bayani daga gare ni, Insha Allah Zanyi magana akan Maudu'in  Muhimmancin Yin Rubutu Wanda bana Harka ba ga Yan uwa ko kuma Hasatan garemu Ma'akatan Wannan Shafi namu na Maasuma Nigeria News Updates.

Za'asamu Matayassara, Idan Allah (T) yakaimu wani karo ko bani ba Wasu daga cikin mu Sai su karasa wannan bayani Sanadiyyar Duk Malamai ne a tafiyar.

Awwalan dai Yanzu Duk cikar mu Ma'aikatan Shafin Ma'asuma Nigeria News Updates, mun kambala Fahimtar Hanyoyin Isar da Sako, kuma Munsan Muhimmancin Isar da Sakon. 


Domin a Yanayin da ake Ciki Yanzu Social media ta Rinjayi kowane Nau'in Ababen Isarda Sako. Kama daga na Tv, Radio, News papers Duk Yanzu hasken Social Media Yana Neman Ya ragye tasirinsu Har Sai Sun hada ayukansu da ita kanta Social media din.

Zakuga Kowane gidan Redio da yake da Shahara yanzu a duniya Sai ya buda Shafi a Social media.

Haka Gida Televisions.

Haka Shima na News papers.


To Anan Inason Na nuna mana Banbanci tsakanin Mu Yan uwa Ma'abuta Addini da Sauran Mutane Wajen Kokarin Isar da Sako Sawa'un na Harkar Musulunci ne ko kuma Labari na Duniya.

Abu nafarko Yan uwa Musulmi Yan jarida da Sauran Yan Media Khadifinsu ko kuma nace Manufarsu a Harkar Isar da Sako Shine; Isar da Sakon Addinin Musulmi da Neman Yaddar Allah.

To acikin Duk Abinda akeyi domin Neman Yaddan Allah akwai Bukatar Gaskiya da Sadaukar da lokaci da Duk  wani Abin Amfani domin neman Yaddan Allah da Samun tsira a gobe .

 To Wannan yasa Yan uwa yan jaridu da Yan Media na Harkar Musulunci Suka Zarce Sauran Yan Jaridu na gama gari Ko kuma na Amawa.

Domin Yan media na Harka Musulunxi Suna Fadar gaskiyar Abinda yafaru ne Duk Inda Bukatar Hakan ya taso ko kuma Wani Al'amari ya Afku.

Sabanin Sauran Yan Jaridu na gama gari  Sunayi ne domin Neman Shahara a Duniya da kuma Abin Sawa a aljihu.

To Anan A daidai Wannan gabar Yakamata Nace .
Kenan Mu da Mukeyin Harkokjn Watsa labarai domin Allah. Yakamata yazan Mun Bude aikin mu yazan bai takaitu a Rahotannin Harka ba kadai.

Saboda Dalilai kamar Haka.........


 Domin Fahimtar Gaskiyar mu Yasa Mutanen dama da basu tare damu a Harkance Suke Yadda da Maganganun mu na Abinda yafaru Acikin Al"umma idan muka kawo batare da Shakka ba.


Ga Misali nan ga Jaridar Almizan Wasu basuyin Harka nan, wasuma Makiya ne Amma Sunayiwa Duk  Labarin da Sukaga  Almizan ta buga Maki dari bisa bisa dari . Su yadda dashi domin Sunsan Yan uwa basu karya suna fadar Gaskiyar Abinda ya faru ne.

Abu na biyu Kuma, Zamu ci Riba Biyu acikin Bude Aikin Mu na Harkar Isar da Sako yazama na Game gari ba Rahoton Harka kadai ba.

Wakilan shafin Ma'asumah a taron karawa juna sani na biyu a garin kano


Dayawa daga Cikin Wadanda Basu kula Shafi Idan Ya taikaita a Matsayin yana kawo Rahotonin Harkar Musulunci ko Shi'anci ne Wasu Ko Shearing bazasuyi ba. Idan ma labarin Harka ne Zakaji Sunce kai ae Wannan Shafin Na Yan kaza ne.


Amma Idan Muka bude Aikin namu Walihan Yazamana Muna kawo Rahoto na gama gari bisa ga gaskiya, da Amanar aikin Jarida Zaizama Sun bada Amana ga Shafin Suna Bibiyarsa yau da gobe ma Zakaga Har post din Harka din da Yazan basa karantawa acan baya sun fara karantawa daga nan Sai Sakon Harkar Musulunci da Da'awa Sufara Shiga Sannu a Hankali.


Sai kaga Sako ya Isa Inda ake bukatarsa.

Sannan Yakamata Dan uwa Dan Jarida ko Dan media Yakasance Mai Inganta Kalmominsa na Rubutu da kula da Kanun labarai da Zai Jawo Hankalin Masu Karatu.

Sannan Idan Son Samu ne.

Yazaman A lokacin Fitar da Rubuce Rubuce na Waki'o'e A rika amfani da Kalmomin da Al'umma gari Suke Fahimta Wajen Isar da Sakon Abinda Yake Faruwa kaitsaye daga Bagieren da Waki'a Din take faruwa.

MISALI ANAN.

*Idan Muka Fitar da Head line akan cewa "JIMI'AN TSARO SUN SHAHADANTAR DA YAN UWA MUSULMI ALMAJIRAN MALAM ZAKZAKY BIYAR WAJEN MUZAHARAN ASHURA DA AKAYI JIYA AGARIN BAUCHI" wannan Head line na Yan uwa kuma Su kadai Zasu yadda da cewa Shahada Sukayi Har Suyi Shearin ko kuma Su tsaya subude link din shafin Su karanta, ko kuma Wasu daidaiku Masu Ilmi akan hakan, kuma a wannan Head line din An bayarda Wasu Mutane da dama daga cikin Al'ummar Yan uwa kristoci da Sauran wani bangare na Addinai daban daban Masu tausaya mana. Amma Abinda Yakama yazama Shine "JAMI"AN TSARO SUN KASHE YAN UWA MUSLMI ALMAJIRAN MALAM ZAKZAKY BIYAR JIYA A WAJEN MUZAHARAN ASHURA A BAUCHI" Anan ko krista ko dan Izala ko dan darika kai ko wanda Baida Addini Yasan Kisa akayi kuma kisa ba bisa hakki ba, akan kowace Irin doka Zalunci ne.

Sannan Wajen Rubutun  Kalmar Waki'a Musamman a "Headline" Domin Waki'a kalmace tamu ta Yan uwa Baikamata a Shafi na Al'umma na kowa da kowa ba, A rika Afani da kalmar waki'a Wajen Rubutu Musamman axikin Shafin da Ake Son Yasamu Karbuwa kowa da kowa, Misali: "YANZU HAKA ANA WAKI'A A GARIN KADUNA WAJEN MUZAHARAN MAULUDI " kaga wannan dan uwa kadai Zai Fahimceka ko wani na kusa da Yan Yan uwa da Suka Saba Jin kalmar Waki'a Yau da gobe amma Idan kace "JAMI"AN TSARON YAN SANDA/SOJOJI SUN AFKAWA ALMAJIRAN MALAM ZAKZAKY MASU ZANGA ZANGAR LUMANA TA MAULUDI" kaga wannan ko krista ko ma wani kalar yare ne, idan yana iya karanta Hausa yasan mi kake nufi.


Sannan Yakamata  arika yin ruubuce Rubuce Na Nishadartar da Al'umma Domin Shima Yana Jawo Hankalin Mutane dadaman gaske Wajen Bada Kulawa ga Shafi Sa6anin Idan Muka Nace akan Da'awa dare da Rana. Amma Rahotannin na Nishadantarwa nan Ma Za'a kama Wasu Shafin Cikin Sauki Zasu karanta Har post, na Da'awar.

Wakilan shafin Ma'asumah wajen taron karawa juna sani agarin katsina Karo na farko



A karshe Abinda Yafi Gayar Muhimmanci Shafin Shine Jawaban Syed Zakzaky na Daidai Da Lokaci. Su Syed (H) Sun Riga Sun kambala Bayani Akan Kowane Irin Al'amuran yau da gobe dama Kulum Musamman Makomar Wannan Al'umma da Muke Ciki.

To shima Yazan koda Ba kulum ba Yazan Ana tunatar Al'umma akan Wannan jawabbai na Jagora (H).

Misali; Kamar Yanzu lokaxin Mulkin Buhari da Yadda Talakkawa Suke Shan Matsin Lamba ta hanyar Cire Tallafin Kaya ln da Ake Shigowa dasu (VART) da kuma Hana Shigo da Shinkafi.

Akwai Jawabin Jagora da yayi Tun lokacin Obasanjo Inda Yake Cewa "Duk Azzalumin da Yayi Mulki a kasar nan Ya sauka Wani yazo Sai Ance gara Wancan da Yawuce da Wannan"

kuma kama Case Din Boko Haram Da yake neman yadawo Sabo Hul a Next Nevel din Shima Jagora Sunyi ta Magana akansa.

Haka na Barayin Shanu.

Duk wannan yanada gayar Muhimmanci acikin Ayukan Mu.

Sannan Akwai bukatar Dan jarida ko media na Harka Yakasance Mutumen mutanen gari amawa.

Da irin dukkanin Maanar waye.

Kuma ba kowane Bagire ne ake bukatar dan uwa dan media yakasance Ya nuna kasan ba.

Saboda yanayin aikinsa.


To Akarshe dai kada na cika ku da surutu Sosai.

Anan Ina bamu Shawara akan Cigaba da kawo Rahotanni na gamari domin Bunkasa shafin mu na Maasuma ya tashi daga na Yan uwa Shia zuwa ga Dukan Al'umma All over the globe✋✋✋

nagode

______________________
Tambaya??

TAYAYA ZAN DAUKI RAHOTO DA AMAWA??
____

Amsa:-
Shi daukar Rahoto ga Amawa Rubutun yanada yawa Sosai amma gashi a taikace.

Zaizama Rahoto biyu kamar yadda nayi magana abaya.

*Rahoton Harka

*Da Rahoto na gama gari.


To kuma kowane da yadda ake Kokarin hada Rahotonsa batare da Anjefa Sours na Labari Cikin Hatsari ba.

Kuma Shi dan media yayi aikinshi cikin Nasara batare da matsala ba.


Misali

Mataki na farko Idan Dan uwa dan Media yasamu labarin Faruwa wani Incident.

Yayi kokari ya Isa wurin da Abin ke faruwa 

Idan wannan damar ta wuce sai aje mataki na biyu.

Shine ta hanyar Sours of Genuine News.
Wanda ya gani da idonsa ta hanyar yin magana dashi fuska da Fuska baka da baka.

Ko kuma ta hanyar magana dashi a waya

To anan.

Akwai Adalci da kare Rayuwar Sours Na labarin bayan kambala firi.

Yanada Zabi na ka tambayeshi yanaso a fadi Sunansa a bayanin ko baida bukata.

Domin kada kajefa rayuwarsa cikin hatsari.

Amma ajiye Record na Zantawarka dashi domin gudun abinda ka iya tafiya yadawo...
_________________

Wannan Jawabin Musa Hassan Shinkafi NE a jawabinsa da yayi a dakin karatu  Na Wakilan Shafin *Ma'asumah Nigeria News updated* Ranar Laraba Talata 17 ga watan Sep.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post