Wadanda wannan tsari na CBN zai fi shafa su ne masu kasuwanci, musamman irin na Kwari ko na Singa a Kano. Su ne suke daukan kudi tsuransa suna kaiwa banki kullu-yaumin. Hanyar magance matsalar kawai shi ne kowane shago ya samo abar nan da ake kira POS domin duk cinikin da za a yi maka da ya ke da kudi da yawa to a yi amfani da ATM wajen turawa.
Shi tsarin dama an yi shi ne domin a hana hada-hada da ruwan kudi a koma “cashless”. Ba wannan gwamnati ce ta fara yunkurin yinsa ba, tun shugabannin baya ake so a yi. Ita gwamnatin nan kun bata dama ne wajen dabbaka duk wani rashin imani da zai wulakanta rayuwar talakawa tun da kuka goya mata a baya a cire “subsidy”. Aka ce ku fito zanga-zanga kuka tsaya wai ku kuna goyon baya! Aka yi muku karyar wai ana kashe kudin kasa. To yanzu da aka dena kashe kudin kasar amfana kuke da shi? Sai ma tatsa da ake daga jikinku.
Tun a lokacin da kungiyar kwadago ta ce a tafi yajin aiki kuka ce ku ba zaku yi ba saboda Maigaskiya ne a kan mulki shi kuma yake gwada muku irin gaskiyarsa. Haka za a yi ta zuwa da tsare-tsaren da kowa sai ya ji a jikinsa amma ban da su. Idan an hana fita da dollar to su ban da su. Idan an kasa biyan albashi su kuma su sayi motocin miliyan hamsin-hamsin. Daga jikinku kuma za a tatsi duk wani kudi da za a watso muku na yin layin dogo da biyan albashin da har yanzu an kasa yi.
©ALIYU DAHIRU ALIYU