SHAWARA ZUWA GA YAN MEDIA, NA HARKA ISLAMIYYA! DAN ALLAH KAYI SHARE DOMIN SAKON YAJE INDA AKESO YAJE!!!

1— A yayin da ake fuskantar cutarwa daga azzalumai, akwai bukatar kowane dan Media ya fahimci aikinsa yadda ya kamata, ya gane cewa Harka da ma dukkan yan uwa sun dogara ga shi ne wajen samar da abin da zai zama hujja a kan cewa tabbas an zalunci yan uwa ne an cutar da su. Don haka ko da kowane dan uwa zai shiga cikin rudewa ko chaji a yayin Waki'a ko kafinta, kai dan Media ya kamata ya zama baka dauki ko da Chajin ba.

2— Abin da ake bukata daga gare ka shine ka samar da hakikanin hotuna da video masu motsi na abin da ya faru (ko yake faruwa), tare da lura sosai wajen zaban me ya kamata ka yada kai tsaye ga duniya, da kuma me ya kamata ka adana ga kanka, ko ka turawa wani amintacce a kebe ya adana, ko da wani abu zai same ka.

3— Za ka natsu ne sosai, ba ruwanka da slogans, ba ruwanka da magana ko sasancin da ake yi, aikinka shine ka dauki abin a yadda ya kamata, kuma ya zama ka natsu ta yadda in hotuna ne za ka samar da masu kyau da za su fitar da sako mai ma'ana, in video ne ka dauki video din a natse ya hanyar kwantar da wayarka (ba a tsaye ba), ta yadda zai zama ko masu daukan Video din gidajen TV sai haka.

4— Ka lura sosai ya zama ka yi aikin ba tare da an cimmaka ba, kuma ka dage wajen kubutar da abin da ka dauka, face in Allah ya nufe ka da rabauta, ta Shahada ko kamu. Za ka iya gane muhimmancin aikin da kake yi idan ka tuna da cewa Waki'ar Zariya gaba dayanta (ta Husainiyya), wani dan uwa ne shi kadai ya natsu ya dauki komai da ya faru tun daga zuwan sojojin, bude wuta, killace yan uwa a Husainiyya suna Sallah, wasu ana musu magani, zuwan Elrufai yai magana da sojojin, tafiyarsa har zuwa dare zuwa safiyar Lahadi. Kuma ya yi iyakan kokarinsa da taimakon Allah wajen kubutar da Videos din, wanda ya zama shi ake yadawa a matsayin kare kai har yanzu.

5— In an samu dama, (musamman wadanda suke da kayan aiki/Camera) su yi kokarin daukar hoton motar maharan, lambarta da rubutun jikinta, da fuskokin masu kawo harin, da suna da lambar rigunansu, ya zama sun yada, duniya ta kalli fuskokin miyagun jami'an tsaron da ke kashe yan kasarsu marasa dauke da makami saboda tsabar zalunci. Amma ya zama da luran gaske da wayewa wajen aikin (hakan zai yiwu ga masu Camera me 'zooming' sosai daga nesa).

6— A yi kokarin kiyaye mutuncin jikkunan Shahidai, musamman yan uwa mata. Kar ya zama a kokarin nuna zalunci da aka musu a bayyana tsiraicinsu. A kiyaye matuka gwargwadon yadda zai yiwu, tare da bayyana zaluncin. 

Allah Ya mana Jagora. Ya mana maganin azzalumai.

9/9/19.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post