SAKONIN SOYAYYA(FARIN CIKIN MASOYA)

SAKONNIN SOYAYYA.
{FARIN-CIKIN MASOYA.}.

{ Sadaukarwa Ga Mata Da Maza, Samari Da
Ma'aurata.}
KECE RAYUWATA.
Zan kasance cikin son ki har abada. Kalaman
bakina sun gaza wajen furta adadin yadda
zuciya take 'kaunar ki. Kin zamo tamkar
numfashin da nake sha'ka. Ke ce rayuwata, ina
son ki. ban san halin da zan shiga ba a lokacin
da na rasa ki. Ke ce abar bege na cikin safiya
da maraice. Ki Huta Lafiya.
TAURARON ZUCIYATA.
Shau'ki mafi tsuma zuciya da nishad'i mafi
'karfin kore damuwar zuciyata basu kasance a
tare da ni ba sai bayan da na had'u da kai. Kai
ne ka zamo tauraron da hasken sa yayi
sanadiyar raba zuciyata da ba'kin duhun da ta
dad'e a ciki. Had'uwa da kai ya kawo canji mai
yawa a cikin rayuwata. Ka huta lafiya. Ina Son
Ka.
KE CE A ZAHIRI KUMA KE CE A CIKIN BACCINA.
Lokutan yin baccina sun kasance daga cikin
lokuta mafi soyuwa a cikin zuciyata saboda ke
ce kika zamanto cikin 'kawata baccina a
dukkan lokacin da na rintse idanuwana, kina
bayyana cikin mafarkina a kowane dare na kan
gan ki cikin shiga irin ta amare, tabbas ina
fatan mafarkina ya zamo gaskiya na zama na
ki kema ki zamo mallakina. Ina Son Ki.
KA ZAMO WANI 'BANGARE NA RAYUWATA.
Burin idaniyata a kullum baya wuce na ganin
ka. Aikin 'kwa'kwalwata cikin kowa ce da'ki'ka
shi ne tinanin ka. Da son ka nake kwana da
son ka nake tashi, tare da shi nake fatan
mutuwa manne cikin 'kirjina. Siffar ka na yi min
gizo cikin duniyar baccina a kowace rana. Ina
son ka masoyina.
A RANA IRIN TA YAU.
Ina son na sanar da ke cewa dukkan wani
motsinki kina yin shi ne a tare da ni domin
kuwa tini ruhikan mu suka dun'kule suka zama
abu d'aya gangar jikin mu ce kawai suka
banbanta da juna. Ina tare da ke zan kuma ci-
gaba da kasancewa a tare da ke cikin dare har
rana. Ina Son Ki.
KA AMINTA DA ZANCE NA DAGA ZUCIYA NE BA
DAGA BAKI BA.
Ina fatan baka daga cikin masu yin tinanin
cewa mace ba zata iya bayyana wa namiji tana
son shi ba? A yau nake son bayyana maka
wani sirri da ya dad'e 'kunshe a cikin zuciyata,
na kamu da son ka ba tun jiya ba balle yau.
Kai ne saurayi na farko da a karon farko ya
sace zuciyata cikin gaggawa, da tinaninka
nake kwana da kuma shi nake tashi. Tabbas
kai ne wanda zuciyata ta dad'e tana nema
domin samun nutsuwarta. Ina son ka masoyina
tare da fatan kasancewa a tare da kai har
abada. Ka huta lafiya.
INA SON KI FIYE DA YADDA NAKE SON KAI NA.
Ko kin jiyo abun da wasu masana SO suke
cewa kuwa? abun da suka ce shi ne, SO shi ne
kasantuwa cikin tinanin wani fiye da yadda
kake tinanin kan ka a koda yaushe kuma cikin
kowane lokaci da kuma yanayi, tabbas wannan
batu yayi dai-dai da yanayin da nake ji a kan
ki. Ina son ki fiye da yadda na ke son kaina. Ki
huta lafiya.
INA SON KA SABODA HALAYYARKA.
Ina kwana na tashi cikin tinanin ka. A dukkan
lokacin da nake cikin damuwa tuno da
tsararrun kalaman ka cikin muryarka mai dad'i
shi ne taimakon gaggawa da yake gusar mini
da damuwa, ina son ka saboda halin ka, amma
shin ni saboda me kake so na, kyau ne ko
kuma mene ne ya ja ra'ayinka a kai na?
KE KYAKKYAWA CE.
Kin kawo haske a cikin rayuwata, kin wadata
zuciyata da farin-ciki, kin kore dikan wata
damuwa daga cikin zuciyata da makami mafi
kaifi wato murmushin ki, zan so na kasance
cikin kallon fuskar ki a dukkan lokacin da kike
yin dariya, tabbas ke kyakkyawa ce, ina godiya
a bisa kulawar da kike ba ni, ina son ki saboda
halin ki. Samuwar ki a cikin rayuwata hakan ya
nuna ni a matsayin d'an baiwa. Ina Son Ki
karda ki manta da hakan.
NA YI FARIN-CIKI DA KASANTUWA TA A TARE
DA KAI.
Sau da yawa zuciyoyin mutane da dama na
shan wahala da shiga matsananciyar damuwa
a lokacin da suke tsaka da neman soyayyar
gaskiya daga wajen wad'anda suke so, ita
kuma soyayya ta gaskiya ana samun ta ne a
wajen wanda ya nuna maka 'kauna, a saboda
haka nake godewa Allah da ya had'a ni da kai
kyakkyawan saurayi mai kamala. Ina son ka.
SAMUN KAMAR KI ZAI ZAMO ABU MAI
WAHALA.
Ina tafe cikin tinanin ki kunnuwana suka jiyo
min abun da ya sosa raina jin cewa da akwai
sauran mata masu kyawun fasali da iya ado
irin na ki a cikin wannan duniya, sai dai ni na
tabbata ba za a ta'ba samun kamar ki ba a
cikin duniyarmu ta mutane, ina fatan ki
kasance cikin bani gudunmawar inganta
soyayyarmu domin cimma wa muradin zuciyar
mu. Na tanadi dukkan wata kulawa domin ki.
Fatana a cikin dare ko rana ki kasance mai tina
cewa, Ina Son Ki.
ZAN KASANCE MAI BAKA KULAWA MASOYINA.
Dama a ce sauran masoya na duniya za su yi
kwaikwayon salon soyayyarka tabbas da
yawan samun matsaloli a soyayya sun ragu.
Ka iya soyayya masoyina, zan kasance mai
baka kulawa da kuma kaucewa dukkan abun
da zai sanya ka a damuwa. Ina son ka ina
kuma kwana cikin tinanin ka. Ka huta lafiya.
INA SON KI RIK`E CEWA.
So abu ne da yake da matu'kar hatsari, saboda
haka akwai bu'katar ki yi duba na tsanaki a
lokacin da kike 'ko'karin za'bar saurayi na
gaskiya wanda zai tafiyar da rayuwar ki cikin
girmamawa da kulawa, amma a lokacin da kika
yi za'ben tumun dare tabbas zaki kasance cikin
da'na'sani da yin nadama na tsawan rayuwa.
Kasantuwa cikin rayuwa mai inganci cikin
soyayya ta gaskiya hakan na nufin ki za'bi
mutumin da hankalin ki ya kwanta da shi.
Wannan shawara ce a matsayina na masoyin
ki. Fatana a kullum ki fahimci cewa, Ina Son Ki.
NI NA TABBATAR DA NA YI DACE.
A dukkan dare zuciyata na rad'a min cewa, So
ba kawai yana nufin samun abokin rayuwa
bane ba, sannan kuma ba yana nufin 'kulla
zazzafar soyayya a karon farko ne ba, a'a SO
yana nufin samun ingantacciyar kulawa daga
wajen saurayi kyakkyawa irin ka, SO na nufin
gina katangar soyayya mai 'kwarin da zata
d'auki tsawon lokacin da ya kai a busa 'kaho a
doron 'kasa. Ina Son Ka.
INA FATAN SAMUN KULAWA DAGA WAJEN KI.
So na iya sawa mutum ya kai kansa wajen da
zuciyarsa zata gaza samun kulawar da ta dace
da shi, hakan na nufin ya kasance cikin 'kunci
da damuwa. Ina fatan zaki kasance cikin bawa
furannin soyayyar da nake yi miki tsaftataccen
ruwa domin ganin ingantuwar soyayyar mu
cikin bawa juna kulawa. Ina Son Ki, farin-cikin
raina.
ZAI YI WAHALA FITAR SON KA DAGA CIKIN
ZUCIYATA.
A lokaci d'aya So kan iya shiga cikin zuciya har
ya samu gurbin zama, amma fitar da shi daga
cikin zuciya ka iya d'aukar mutum tsawan
rayuwa ba tare da ya cimma wa hakan ba, ina
son ka masoyina zai yi wahala fitar son ka
daga cikin zuciyata. Ina fatan zan kasance
cikin zuciyarka kamar yadda ka kasance cikin
tawa zuciyar a safiya da maraice?. Ina Son Ka.
KIN YI MIN SATA.
Tawagar jami'an tsaro na nan tafe a hanyar su
ta zuwa kama ki a sakamakon sace min zuciya
da kika yi, kika kuma yi garkuwa da farin-ciki
na, kika kasance ri'ke da linzamin sarrafa
tinanina. A nan nake cewa mu had'u a kotun
masoya domin ki kare kan ki. Hmm! Ina Son Ki,
Masoyiyata.
INA TINANIN RANAR DA ZATA ZO A CE NA
RASAKA A CIKIN TA.
Ina son ka masoyina, ina kwana zuciya cike da
tinanin ka. Na aminta da cewar masu cewa Shi
so tamkar ya'ki ne wanda fara shi yake da
sau'ki amma tsayawarsa ya zamo abu mai
wahala. Ina tinanin ranar da zata zo a ce na
rasa ka a cikin ta, wannan rana zata kasance
rana mafi duhu da 'kuntata a gare ni. Ina son
Ka.
SAMUWAR FARIN-CIKIN KI SHI NE BURINA.
Dukkan abun da na baki masoyiyata na
dangane da lokaci da kuma kulawa ba wai ina
tsammanin samun kwatankwacin shi daga
wajen ki bane ba domin yin hakan abu ne da ya
zama dole a kaina. A kullum burina ki kasance
cikin farin-ciki da annushuwa. Ina son ki abar
begena.
MU KASANCE TARE CIKIN SON JUNA SHI NE
MURADI NA.
Kasantuwar ka masoyi a gare ni ya wadata
zuciyata da farin-ciki. Samuwar farin-ciki a
gare ni cikin soyayyar mu ba abu ne da ganin
'karshen sa zai yi sau'ki ba, saboda ita
soyayya ta gaskiya aba ce da bata ta'ba
gogewa daga cikin zuciyoyin masoyan biyu.
Ina fatan zaka ci-gaba da so na kamar yadda
nake son ka har abada. Ka huta lafiya.
BURIN ZUCIYATA SHI NE KI ZAMO MATATA.
Na kan shafe dare cikin yin addu'ar dacewa da
samun wani kaso daga cikin kulawar ki
masoyiyata, So ya kasance a cikin zuciya ne
ita kuma kulawa bayyane take a saman
fuskokin mu, zan kasance cikin farin-ciki na
tsawon rayuwa a dukkan lokacin da aka ce na
mallake ki a matsayin matata, ina son ki, ina
kuma 'kaunar ki, zan ci-gaba da son ki har
abada.
BANI DA GWANIN DA YA ZARCE KA.
Ina son ka kuma ba zan daina son ka ba har
zuwa lokacin da zuciyata zata daina bugawa.
kai ne a cikin zuciyata a dukkan inda na shiga
a fad'in duniya, babu wanda zai iya maye
gurbin ka a cikin ta a lokacin da na rasaka
saboda haka nake fatan Allah ya bar mu tare
har abada. Ka huta lafiya.
KO KIN SAN CEWA AKWAI WANI SIRRI NA
MASOYA A JIKIN FURANNI?.
A lokacin da kika kai ganin ki ga tarun furanni
dake shinfid'e cikin lambun masoya zaki tarar
da banbanci mai yawa dake tsakanin su ta
fuskar launi, amma abun mamaki a gare su shi
ne duk 'kamshin su ya kasance guda d'aya ne,
wannan ba komai bane face wani sirri na
daban a soyayya. Son ki ya mamaye zuciyata
fiye da yadda fuskata zata iya bayyanar da
hakan a zahiri. Ina Son Ki masoyiyata.
MIJINA FARIN-CIKIN ZUCIYATA.
Ina fatan kana nan cikin walwala da jin dad'i
mijina na kaina? Na kan shiga cikin kewarka a
dukkan lokacin da ka yi nesa da ni. Tabbas
son ka ya mamaye zuciyata hakan ya sanya
bana yin wata walwala da sukuni face muna a
tare da juna. Ina son ka hasken idaniyata. Ina
yi maka Fatan nasara da dawowar ka gida
lafiya.
INA SON KI MATATA.
A yanzu haka son ki ya motsa a cikin zuciyata.
Tabbas na 'kara aminta da cewa soyayya bata
tsufa, saboda shi so bawai yana samuwa ne
daga duniyar tinanin mu da ta kasance cikin
irga shekarun mu ba, yana samuwa ne a cikin
zuciyoyin mu da suka kasance cikin bijirewa
irga adadin shekarun na mu a duniya. A
saboda haka nake cewa ina son ki matata, ki
kula min da kan ki har zuwa lokacin da zan
dawo gida. Ki huta lafiya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post