FACEBOOK SUN HANA DUBBAN MANHAJA AIKI A SHAFINSU

FACEBOOK SUN HAN DUBBAN MANHAJA AIKI A SHAFINSU. 

Hukumomi sun tuhumi Cambridge Analytica da amfani da bayanan sirrin domin samar da tallace-tallacen siyasa da suka yi kokarin sauya wa ra'ayinsu kan mutumin da ya fi dacewa su zaba ya jagoranci kasashensu.
A sanadiyyar badakkalar Cambridge Analytica, hukumar samar da daidaito a ciniki ta Amurka ta ci tarar Facebook dala biliyan 5 a watan Yuli.



Wannan ne mataki irinsa mafi girma da aka taba cin wani kamfani da ya taka dokar boye bayanan sirrin masu hulda da shi.
Badakkalar Cambridge Analytica - wadda ta shafi dubban miliyoyin mutane ya dagula wa Facebook lissafi matuka, kuma har yanzu yana fuskantar shari'a daga mutane da kamfanonin da abin ya shafa.



A kan haka ne ya dauki wadansu matakan yin gyara ga yadda ya ke aiki da kuma gyara barnar da batun yayi wa dangantakarsa da masu amfani da shafin sada zumuntarsa mai matukar farin jini.


Ana yada manhajar da ke dauke da sirrin mutane a Facebook
An ci tarar Facebook dala billiyan biyar
A bara Facebook ya kaddamar da wani bincike kan yadda a kan yi amfani da manhajoji wajen sarrafa bayanai daga shafin nasa.
Kuma ya fara da dakatar da manhajar wasu kamfanoni 400 ne, amma ya ce ba duka manhajojin ne suka kasance masu hadari ga masu amfani da Facebook din ba.


Kamfanin Facebook ya fuskanci matsanancin matsin lamba a shekarar 2018 bayan da aka bayyana cewa wani kamfani mai suna Cambridge Analytica ya yi amfani da bayanan mutane ba tare da izini ba.
Har yanzu Faceook ya ci gaba da gudanar da wannan binciken, kuma bai ajiye lokacin da zai kammala aikin ba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post