ME YA FARU A DAJIN KADUNA????

SOJOJI SUNYI NASARAR KWATO MUTUN BAKWAI A HANNUN MASU GARKUWA DA MUTANE

Rundunar soji ta shirin Operation WHIRL da ke a Dibijin ta daya dake a jihar Kaduna sun ta sanar da cewa ka da mutanen da aka yi garkuwa dasu su takwas a kauyen Labi dake a cikin karamar hukumar Chikun a cikin jihar ta Kaduna.
Jaridar Punch ta ruwaito a ranar Larabar data gabata cewa, mutanen da aka kubutar, ayi garkuwa dasu ne a lokacin suna kan hanyar su ne daga garin Ilorin dake a cikin jihar Kwara zuwa jihar Kano.
Wata majiya da bata bukatar a ambaci sunanta saboda ba’a bata izini ba ta bayyana cewa, bayan anyi garkuwa da mutanen an kuma jutsa dasu zuwa cikin wani Daji.
Majiyar ta ci gaba da cewa, bayan da aka samu bayanan sirri ne jami’an na sojin suka bazama suka dura ga maboyar nasu garkuwar, inda musayar wuta ta barke masu garkuwar suka suka ranta a na Kare dauke da raunuka suka kuma bar mutanen da sukuyi garkuwa dasu a sansanain nasu.
Jami’an sun saki nutanen da akayi garkuwar dasu suka kuma umarce su dasu ci gaba da tafiya inda zasu.
In za’a iya tunawa, wannan shine karo na biyu a cikin satuttukan da suka gabata da jami’an na Dibijin ta daya dake kaduna suka kwato wasu da akayi garkuwa dasu.
Bugu da kari, a satin makon da ya gabata, mutane bakwai harda yarinya yar shekara bakwai akayi garkuwa dasu a kan babbar hanyar Abuja zuwa jihar Kaduna a ranar Lahadin data wuce, inda suma jami’an shirin soji na ‘Operation Thunder Strike na Dibijin ta daya ya kubutar da su.
Su wadananan matafiyan, suna kan hanyar su daga garin Offa dake a cikin jihar Kwara ne zuwa jihar Kaduna a lokacin da lamarin ya rutsa dasu.
Wadanda akayi garkuwar dasu sun bayyana cewa, wadanda suka sace su, suna sanye ne da kakin soji, inda suka dakatar dasu a kan babban titin
Rijan da musakin karfe 9.30 na yammacin ranar da abin ya faru suka kuma umarce su su shiga Daji.
Sai dai, GOC Majo Janar Faruk Yahaya ya bayyana jin dadinsa a kan nasarar da jami’an suke samu wajen yakar masu yin garkuwar.



An Tallafawa Manoma 94,000 A Kano Da Jigawa Don Noman Auduga

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post