NAJERIYA KI KARA KULLE BODOJINKI DOMIN MAKWAFTA SU SAN MUHIMMANCINKI.


Tabbas! Muna fuskantar matsin rayuwa a kasar mu ta najeriya, musamman da aka rufe kanun iyakarmu da sauran makwafta, domin kasuwancin mu ya samu tawaya matuka.

To amma duk mai nazari da bibiyar lamura, zai fahimci cewa daukar wannan mataki, zaiyi tasiri ga darajar najeriya a idon makwaftanta, musamman kasar jamhuriyar Benin data maidamu fitila mai haskawa, muke raya su, sukuma suna kokarin kashemu.

Jamhuriyar Benin itace kasa ta shidda a duniya datake yo oda ta shinkafa, duk da mutanen ta basu wuce miliyan ashirin ba, saboda haka idan aka lura kaso tamanin na wannan shinkafa najeriya ake kawota kuma sai an biyasu haraji. Bayaga sauran kayayyaki da suka hada da motoci, kayansawa, kayan kallo, da sauransu.

Kamar yadda nasamu labari najeriya karkashin wannan gwamnati ta taba Neman goyon bayan jamhuriyar Benin akan ta rika karbarwa najeriya haraji a akan iyakar kasar Benin idan an biya nasu sai a biya namu tunda mutanen mu suna bin dokar kasar Benin, amma sai kasar Benin tayi tutsu taki yarda.

Haka kuma a wani labarin ance sau biyu shugaban kwastam Hamid Ali yana zuwa Benin domin ganawa da shugaban kasar amma yaki yarda su gana, saidai ya dawo haka nan. Domin suna ganin kamar mu zasu taimaka, sun mance akwai wani shugabansu dayace najeriya jaha 37 ce idan aka hada da jamhuriyar Benin.

Saboda haka yakamata mutanen kasa ta  najeriya su fahimci cewa Neman yanci baya samuwa cikin sauki domin wani lokacin har da mutuwa ake haduwa bawai wahala ba kadai, shi kuma wannan mataki na nemamana yanci ne, domin muna noman shinkafa, a kasar mu, amma wata kasa ta kashemu ita tana raya kanta, ana amfani da kasarsu ana shigo mana da miyagun kwayoyi da makamai.

To yanzu gaskiya tafara halinta domin ko yanzu da safen nan naji rahoto a BBC Hausa cewa rufe boda ya nakasa tattalin arzikin jamhuriyar benin, suna cikin matsanancin hali, haka kuma sauran makwafta suma sun shiga taitayinsu. DA WANNAN NAKE KIRA GA GWAMNATIN NAJERIYA KADA TA SAUSAUTA HAR SAI ANCIMMA KYAKKYAWAR MATSAYA WADDA ZATA AMFANEMU FIYE DA YADDA SUKE AMFANUWA, IDAN BA HAKA BA MUJE ZUWA, AGA KASASHHSE. Kuma dama bahaushe na cewa makaho baisan ana ganinsa ba har sai an tabashi.

Musa Ibrahim Daura.
18-9-2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post