SUWANENE SUKE KASHE MATA A OTAL NA FATAKWAL??

SUWA NENE SUKE KASHE MATA  A OTAL NA FATAKWAL?? 

Sama da kungiyoyin mata 50 ne suka gudanar da wani tattaki domin nuna bacin ransu dangane da kisan gillar da ake yi wa 'yan mata a Patakwal da ke kudu maso kudancin Nigeria.
Gungun matan da suka shirya zuwa ofishin 'yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya, DSS da fadar gwamnatin jihar Rivers har ma da zauren majalisar dokokin jihar, na neman hukumomi su rubanya kokarinsu wajen kare rayukan al'ummar jihar.
Sun kuma bukaci a gaggauta janye tambarin mata masu zaman kansu da aka yi wa 'yan matan da suka rasu ta wannan hanya.
Wannan zanga-zangar lumana da matan ke yi na zuwa ne kwana guda bayan 'yan sanda sun tabbatar da kame wasu mutane uku bisa samun su da hannu a batun kisan 'yan matan
Di women dey protest
Kwamishinan 'yan sanda a jihar ta Rivers, Mustapha Dandaura ya fada wa 'yan jarida cewa mata takwas ne suka mutu ta hanyar shake su a wasu gidajen otal-otal da ke jihar.
Port Harcourt Significant GirlsHakkin mallakar hotoPORT HARCOURT SIGNIFICANT GIRLS
Image captionMata sun yi zanga zanga ranar Litinin game da kashe kashen 'yan mata a Patakwal.
Dandaura ya ce sun yi nasarar damke daya daga cikin wadanda ake zargi ranar Litinin lokacin da wata matashiya ta sanar da su cewa akwai wani mutum da ya yi tayin biyan ta naira dubu 30 idan ta amince masa, abin da ya sa a cewar sa, suka bibiyi mutumin tare da cafke domin yin holensa

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post