✍️Rahama Abdulmajid
A jiya ne kasar Masar ta sake fadawa wata sabuwar zanga-zangar nuna kyamar Gwamnatin Sisi wadda rabon da a yi irinta tun juyin juya halin shekara 2011 da ya karade kasashen larabawa.
Hotunan Dandalin yanci na Tahrir da wasu sassa na Birnin Iskandariyya tare da kalaman musababbin wannan zanga zangar su ya kamata shugabannin Najeriya su kurawa idanu su yi ta nazari akai.
Hoton na kunshe ne da zallar talakawan kasar wadanda suka kyamaci gwamnatin Mubarak kwatankwacin yadda talakawan Najeriya suka kyamaci PDP suka rungumi APC.
Kwalayen zangazangar tare da furucin jamaa na nuna Ummul Haba'isun Zangazangar kan manufofin gwamnati ne kan sake farfado da tattalin arzikin kasar wanda ya jefa talaka kadai a kunci mai kudi na watayawarsa. Wannan ba Shi da maraba da halin da talakan Najeriya ya tsinci kansa ciki.
Wasu Makaloli da ke yawo a shafukan sadarwar kasar na nuna yadda shugaba Sisi ke watayawa cikin rayuwar Alfarma nesa da yadda yake nuna damuwarsa da talaka. Kwatankwacin yadda lamarin yake a Najeriya Inda mahukumta ke tafiye tafiye na alfarma da bike bike har yan majalisa na kara alawus da motoci a yayinda ake shirin karawa talaka haraji don kawai za a bashi Naira dubu daya tal talk a rana (albashin dubu30)
Ba fatanmu a shiga irin wannan yanayi na zaman dardar a Najeriya ba, Amma mahukumta su sani irin wannan halin tilasta kansa yake wa jamaa sakamakon kunci ba don fata ba, haka zalika abin kunya ne a ce gwamnatin talakawa ta koma fito na fito da talakawan.

Tags:
Daga marubata