DOMIN KAI DA UWAR GIDA
Sinadarin Iron kuwa daya ne daga cikin sinadaran Mineral salts, dan adam baligi akan sami gram 5 a jikinsa na sinadarin, wanda kashi 60% daga ciki yana qunshe ne a qwayoyin jini da hanta, saifa, qoda da 6argo da ga6o6in jikin dan adam, yakan shiga cikin gamammen jini.
Hemoglobin wanda yake hada qwayoyin jan jinin da yake nado Oxygen daga huhu zuwa 6angarorin jiki, domin cika aikin Oxidation, ya nada kuma Carbondioxide daga huhu don fitar dashi alokacin numfashi, akan tsatso shine ta hanyar qananan hanjin sama tare da taimakawar Gastric Juice na cikin tumbi da Vitamin C, matuqar babu sinadaran Alkali, Oxalat, Tannic acid da ake samunsa a shayi ko Kofi.
Wannan sinadari na Iron yakan taru ne a hantar mutum, saifa, 6argo har zuwa lokacin da jikin mutum zai buqace shi, yakan qarfafa garkuwan jiki ya qara mata qarfi wajen yaqar cututtuka, to wajen tsotso sinadarin dole a sami taimakon Hydro chloric acid a cikin tumbi, shi kuma yana buqatar Element copper, Vitamin A da B, samun Vitamin C zai iya taimakawa da kusan kashi 30%.
Akan sami sinadarin Iron ne a :-Nama, hantar dabbobi, qoda, rawayar qwai, alayyaho, celery, latas, garin hatsi, dankalin Hausa, 'ya'yan kabewa, ridi, alkama, qwan agwagwa, albasa, ayaba, tumaturi, dabino, 6aure, zabibi, zuma da waken soya.
Qarancin wannan sinadarin a jikin mutum yakan haifar da:-Gajiya, toshewar numfashi, qaiqayin jiki, karyewan faratu, kumburin harshe da tsattsagewarsa,bushewar baki da maqogwaro, wahala wurin hadiyar yawu da rasa dandano.
Qarancin wannan sinadarin a jikin mutum yakan haifar da:-Gajiya, toshewar numfashi, qaiqayin jiki, karyewan faratu, kumburin harshe da tsattsagewarsa,bushewar baki da maqogwaro, wahala wurin hadiyar yawu da rasa dandano.
Haka in yayi yawa a jiki yakan haifar da:- Raunin zuciya, hanta har da ga6o6in saduwa, yana iya haifar da cutar sukari wanda ake kira Bronze Diabetes, yana kuma da illa ga sabbin qarin jini, akwai kuma yuwuwan kamuwa da kansar maqogwaro da na tumbi, amma samun isasshen sinadarin Zinc zai iya taimakawa.
A taqaice yin tsari da canja baki a abinci shine mafita ga rayuwar dan adam, ba shan magungunan gargajiya ko na likita ba tsari ba, galibin cututtukan mu daga abincin mu ne.
Sinadarorin Vitamins suna da matuqar mahimmanci ajikin ma'aurata da ma gwagwaren gabadaya, don aikin su shine, tsara amfanuwar abinci a jikin dan adam, qarfin amfanuwar jiki da nau'o'in abinci ya ta'allaqa ne da yalwatattun Vitamins din da ake buqata, a zahiri wadannan sinadarai (Vitamins) basa tattare da kuzari (Energy), kuma basa turawa jiki wani energy sai dai sukan sanya kuzarin ne yin aikin da ya kamata.
Kenan duk da muhimmancin wadannan sinadaren na Vitamins, buqatum mu da suka danne a kowace rana, zama mu iya samo su acikin abincin da muke ci ba sai mun ga likita ba.
Zamu iya cewa Vitamins suna da matuqar muhimmanci na kaitsaye ko ta wata hanyar dangane da lamarin shimfida, mafi mahimmanci a ciki shine Vitamin A, musamman ga mace, don yakan gyara mata fatar jiki ta yita walqiya,qarancin sinadarin kuwa yakan kawo bushewar fata,da tsattsagewarta, mace kuwa tana da kaso mai girma a fatar jikinta dangane da sha'awarta da saduwa.
Sinadarin kan qarawa tsukin mahaifarta lafiya, namiji kuwa yakan amfana da Vitamin A ne ta wurin lafiyar ma6u66ugar maniyyinsa, wato Prostate da maraina, da kuma lafiyar ruwan maniyyin kansa, qarancinsa yakan kawo illa ga hanci, baki, matsukin numfashi da na fitsari da ma na ruwan maniyyi, masana suna ganin sinadarin yana iya maganin duk wani inflammation. Ana iya samun sa a naman dabbobi musamman hanta, rawayan qwai, kindirmo da awaran qwai, haka kuma karas, kankana (water melon), shammam (sweetmelon), tumatur, latas da alayyahu.
To amma cinsa da yawa yana da matuqar illa ga rayuwar dan adam, abi a hankali, Musamman wadanda suke shan qwayoyinsa don jin dadin jima'i ba tare da shawarar likita ba, yawaita shi yakan haifar da bushewar fata, da kakkaryewan suma.
Qaruwar Carotene a cikin jini, ko fatar mutum ta canza zuwa launin rawaya, kumburin hanta da saifa, kenan abincin da muke ci ya ishe mu ba sai mun janyo wa kawunan mu cututtuka ba. Vitamin D sananne ne wajen hana raunin qashi, ga wani aiki da yake yi wajen gyara shimfidunmu(saduwa), duk da cewa hanyoyin samo wannan sinadari basu da yawa.
Amma Allah(S.W.T) cikin qudurarsa yaba jikin mu ikon samar mana dashi basai mun ga likita ba, domin sinadarin Argustrol dake qarqashin fatar jikin mu yakan juya zuwa wannan sinadarin na Vitamin D, aduk lokacin da zafin rana ya dake mu, shi yasa iyayen mu na karkara sukan tsufa da karfin su ba kamar mu da muke cikin A/C kullum ba, ana kuma iya samun wannan sinadarin a rawayan qwai, hanta, da sauran kifin da basu bushe ba.
Yawaita wannan sinadari na Vitamin D ta hanyar qwayoyi, yakan haifar da yawan sinadarin Calcium da yake daskarewa a zuciya ya 6ata tsarin bugawarta, ko qoda ya kawo tsakuwoyi aciki, in abu yayi tsanani ana iya samun doguwar suma ko ma rasuwa.
•Vitamin E kuwa shi akafi sani da taimakawa wajen magance illar da take hana samun ciki, abin mamaki tana qunshene acikin latas, Misiriyawa sun san wannan tun dubannin shekarun da suka gabata.
Wannan sinadari yakan taimaka wa uwar gida da ma mai gida gaba daya, domin qarancin sa a jikin namiji yana kashe qwayoyin Germ cell wajen yabanya, wanda hakan yana iya haifar da rashin samun haihuwa, mace kuwa in ta rasa, yana iya haifar da 6arin jaririnta a farkon ciki, inma cikin bai zuba ba, da yawa dan yakan fito ba rai.
Akan same shine a ganyayyaki musamman latas, jarjir (water cress) da alayyaho, akan same shi a man alkama, da qwayar gyada, rawayar qwai da kuma nono.
Yau da izinin Allah mun gangaro kan Vitamin B1 ko kuma Thimin, kodayake ban son yin zurfi acikinsa gudun barin tsayayyen batu, amma wannan sinadarin yana da tasiri mai girman gaske dangane da qwanyin namiji da mace, qarancinsa ma yakan sa gaban namiji ya daina buqatar mace gaba daya, ko kuwa asami rauni dangane da 6angaren sha'awar mace(Lust) domin gazawar jiki wajen tasar da sha'awar saduwa.
Shi ma hakan dalili ne na gazawar jiki wajen samar da E strogens Hormones, kazalika qarancin sinadarin yakan kawo qarancin nono ga mai shayarwa, da rauni wurin saduwa, qarancin Thimin har
yakan kawo matsala ga shimfida, akan same shine a hatsin da ba a surfe ba da irin su hanta, kifi, nono da sauran ganyayyakin da basu ga wuta ba.
Sinadarin Vitamin B2 ko riboflavin kuwa shine na mata, mai sanya kyawun fata da naso,
qarancinsa yakan haifar da tsagewar le6e da 6angarorin cikin baki, ko ya haifar da afata, kaga baki yayi ja zuwa launin malmo, le6en ido daga ciki ya sami matsala idon ya riqa hawaye.
Ya zamo bai son haske, ana iya samun mafita akan sinadarin Riboflavin ta hanyar ganyayyakin da basu ga wuta ba, da nono.
•Niacin ko Nicotinic Acid yakan magance cutar fata wace take kirci har launin ta yayi duhu ga (farin mutum) a fuska da wuya da hannu, har mutum ya riqa fama da ciwon kai, mutuwar 6arin jiki ko matsalar shimfida, ko ya fara sababi akan qaramin abu, akan sami Niacin ne ta wurin nama, hanta, kifi, alayyaho da karas.
Sinadarin Vitamin B3 ko Pantothinic acid yakan taimaka matuqa, masamman wajen kiyaye daidaituwan abinci a 6angarorin jiki, da taimaka wa gashi, musamman na kai yadda yake hana saurin furfura, domin qarancin sa yakan haifar da zuban suma, da matsalar gudanan jini har ta kai ga matsalolin shimfida, akan samo shine ta hanyar hanta, rawayar qwai, danyen ganyayyaki, gyada, nama, hatsi da nono, wasu daga ciki sukan zama sinadarin Pyridoxine ko Vitamin B6, kusan aikinsu guda ne.
Sinadarin Biotin kuwa shima a jerin sinadarorin vitamin B din ne, wanda qarancin sa yakan haifar da inflammation na fata, da bushewarta, a daidai lokacin da ake samun raunin jiki gabadaya, da mutuwar sha'awa, wannan kuwa yakan kawo wa shimfida matsala, akan same shine a qwai, qoda, hanta, mafi yawan ganyayyaki, da 'ya'yan bishiya, Vitamin B9.
Yana da muhimmanci ga manya musamman ga mai ciki, sai dai qarancinsa yakan kawo cutar rashin jini, musamman bayan girma ko yayin juna biyu, hakan yakan shafi shimfida qwarai.
Wannan sinadarin yakan taimaki masu juna biyu a wurin haihuwa, qarancinsa yakan haifar da sumewa, akan same shine a ganyayyaki musamman na alayyaho, mai yiwuwa cin alayyahon na gram 250 a rana yayi maganin matsalar da ake fama da ita, akan same ta ne a latas, qoda da nono.
Vitamin K kuwa yakan taimaka wajen tsare jini don karya kwarara, kenan yana da kyau ga mata masu dab da haihuwa, akan sameshi a man gyada ko na waken soya, akan sameshi kadan a nono, qwai ko kuwa sinadarorin hanjin mutum kan bashi babban gudummawa wajen samo shi.
Sinadarin Vitamin C yakan taimaka wajen kiyaye magudanar jini, da lafiyar harshe, qarancinsa kan kawo matsalar lafiya a jiki, qurarrajin harshe da zuban haqori, samunsa a jikin mace yakan kare ta wurin, kamuwa da zawayi ko yoyon fitsari, anfi samun sa a lemon zaqi da na tsami, tumatur, karas, strawberry, ayaba, gwaiba, da tuffaha ko nono da hanta.
Amma kar mutum ya sayo qwayoyi kawai yayi ta sha ba da izinin likita ba, ko saka wadannan abubuwan a gaba yayi musu cin qoshi, mun dai ambato illolinsu a baya.
Ga kayayyakin abincin uwar gida nan:-
•Kayan gina jiki (Protein) sune:-Nau'o'in nama, qwai, madaran dabbobi da duk abinda akayi da ita, hanta, qoda, kifaye, waken Pea, adas, farin wake, na miya da waken Larabawa, gyada, alkama.
•Vitamin A:-Rawayan qwai, kindirmo, madara, karas, alayyaho, latas, tumatur, kabeji, albasa, celery, berry, shammam, gwaba, mangwaro, strawberry.
•Vitamin B:- Hanta, alkama, zuma, kindirmo, burodi.
•Vitamin C:- Hanta, qoda, lemon zaqi da na tsami, latas, tumatir, barkono, alayyaho, karas, kabeji, albasa, ayaba, inabi, mangwaro, gwaba.
•Vitamin E:- Nama, hanta, qoda, madara, alkama, rawayar qwai, latas, gyada, lansir, ridi, man kwantulora.
•Abincin da ake samun (Calcium):-Madara da abinda aka yi da ita, baqar zuma, adas, baure.
• Ana samun (Iron) a:- Hanta, qwai, baqar zuma, gyada, karas, dabino.
• Zinc kuwa kan fita daga cikin:-alkamar da ba a surfe ba, karas, masara, sha'ir, wadannan duk suna da muhimmancinsu.
Na kawo ne don uwar gida ta san yadda za ta riqa hada dangogin abinci wajen gabatar wa mai gida, banda hada dangi daya, yafi kyau a nau'anta, kar a hada qwai da nama da madara, don dukansu 'yan gida daya ne, idan mutum ya hada kifi da nono yayi zawo ba abin mamaki bane don dukansu 'yan gida daya ne.
in suka wuce yadda ake buqatar su tabbas abu mai kamar haka yana iya faruwa, amma kuma zai
yiwu a hada 'yan gida daya mabambanta, kamar qwai a bangaren jikin dabba da wake a 6angaren tsirrai, wannan yafi qara lafiya, sai a dan yayyanka tumatur da latas daidai a watsa aciki, sai kaci da burodin ka, ga dadi ga lafiya.
Abincin gina jiki (Proteins) na jikin dabbobi sun fi kowanne bada kuzari a shimfida, da qarfafa sha'awar saduwa, to amma fa in suka yi yawa sukan kawo tsamin jini, shi kuma yakan raunana sha'awar saduwa sosai, ciki har da mazakuta, ana iya kamuwa da amai, da rudun ciki.
Yawaita ci sama da qima yakan kawo tsakuwar qoda da kumburin ma6u66ugan maniyyi, ya zama wanda yake buqata na (Protein) a rana kada ya wuce Gram 75, gram 50 daga jikin dabba, 25 daga tsirrai, in za a qimanta sai ya zamanto kamar haka Jan nama 20%, tantabara 22%, hanta 18%, zuciya da qoda 17%, kifi 15-20%, qwai 11%, madara 3.5%.
A tsirrai kuma:-Dangogin wake, 17.8%, gyada 26%, alkama 24%, kodayake madara daga jikin dabba take amma bata sanya tsamin jini, to amma akwai abubuwan da in suka yi yawa sukan kawo hakan misali, sukari, alawoyi, farar fulawa da dangogin cincin.
To amma in aka sami madara ko 'ya'yan itace aka dora sukan dawo da jinin daidai, kamar lemon zaqi ko natsami (bafa na kanti ba), tuffaha da sauran ganyayyaki, to amma lemon zaqi da tsami duk da cewa suna qunshe da tsamin, amma fa basa haifar da tsamin jini ko kadan.
Tags:
Taskar Ma'aurata