JINJINA DA BAN GAJIYA GAREKU HUSAINAWA DA ZAINABAWA

JINJINA DA BAN GAJIYA GAREKU HUSAINAWA DA ZAINABAWA..


@MA'ASUMA NIGERIA NEWS UPDATED.
Ammar Abubakar shadow

LALLAI ABUNDA YA FARU YA FARU.

A kowane yanki na fadin nigeria yan uwa ina mika jinjina a gareku dubada yanda aka jure aka nuna ma duniya cewa mabiya ahlul bait ba'ayi masu barazana da mutuwa.

Ta bangare guda kuma inaba jami'an tsaro ko ince gomnati shawara koda zatayi mana barazana da mutuwa to tayi amma ba a taron Ashura ba!!!

Domin kuwa Dalilin taruwarmu wani aka kashe muke juyayin kasheshi. Duk wanda yasan tarihin karbala to kisa baya storatashi wallahi.

Allah ka bamu sabati da juriya domin mu tunkari kafircin duniya mu nuna masa cewa dole sai addini ya tabbata a daron duniya ko suna sooo ko basa sooo addini saiya kafu daram insha Allah .


Kuma yan uwa mu kara daure damara domin kuwa akwai wani aikin a gabanmu wato tattaki shima yana daga cikin abunda ya tsone masu ido. Kuma mun sani mu bazamu fasaba kuma suma sukan iya nuna mana ikonsu amma ikon Allah shine sama akan komai kuma shi muka dogara dashi. Shine zai yi mana maganinsu.

Mukara neman kusanci ga Allah madaukakin sarki shine zai temakemu a kowanne hali mun sani cewa nasara garemu take kuma bashakka saidai mu jira lokaci ko a kusa ko nesa amma zatazo da iznin Allah.


Ahaka zan tsaya amma ina matukar jinjina ma yan uwa da suka jajirce suka tsayu akan tabbatar da addinin Allah a doron kasa.

Allah ya kara bamu sabati.

Nine Almajirin Allama sayyeed zakzaky wato A. A.Shadow

Ina rokonku ku sakani cikin addu'o'inku masu girma. Allah ya yaye mana Abunda y a dame mu.

11/09/2019

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post