12 SATUMBA 1996: SHEKARU 23 DA YUNKURIN ABACHA NA GAMAWA DA HARKAR MUSULUNCI (1)

@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE

TARE DA SAIFULLAHI M KABIR

Shekaru 23 da suka gabata, a rana mai kamar yau, Alhamis 12
ga Satumba, 1996 Janaral Sani Abacha ya yi yunkurin dirarwa
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da almajiransa a wani shirinsa na
shafe Harkar Musulunci a Nigeria da kawo karshenta baki
daya.

Marigayi Sani Abacha ya shirya bin matakai ne daki-daki wajen
kokarin cimma burinsa na kawar da Harka Islamiyyah da kashe
Jagoranta a wancan lokacin, a yayin da ya fara da matakin
kama Shaikh Zakzaky (H) a farko. Ko da yake ya san bayan kamun
ba zai yiwu almajiransa su zauna ba, za su fito Muzahara, don
haka sai ya bude wuta a kan masu Muzaharar a wannan
lokacin da kisan ba ji ba gani. Daga baya kuma aka je mataki
na uku, wanda shine bin garuruwan ‘yan uwa ana kamu, dauri a kurkuku da azabtarwa.

Na taba ji daga Shaikh Zakzaky (H) cewa, shirin Abacha a
lokacin shine ya kama Malam din, bayan kamun ya san za a
fito Muzaharori, don haka sai ya yi kokarin murkushe
Muzaharorin har sadda za a dena jin motsin ‘yan'uwa kwata-
kwata, in ya ji tsit daga ‘yan uwa, sai ya kashe Malam din,
shigen yadda tsohon shugaban Iraq, Saddam Husaini ya yi a
kan Sayyid Bakir, wanda ya kama shi, ya ji tsit daga
almajiransa, har ma ya fitar da jita-jitan cewa an kashe shi,
amma ya ji tsit, sai ya fuskanci ba wata barazana ko ya kashe
shi din, don haka ya kashe shin.

Amma a lokacin sai ba a yi tsit din ba, ‘yan uwa duk da
barazanar mulkin soja da haukarsa, sai suka motsa tun daga
washe-garin ranar da aka yi kamun har aka kwashe shekaru
biyu da watanni, Abacha ya mutu, aka saki Shaikh Zakzaky (H) da sauran 'yan'uwa, waki'ar ta kwaranye.

KAMA SHAIKH ZAKZAKY (H)

Ba tare da wani abu ya faru ba, ba tare da ana wani taro ba,
haka kawai, da asubahin ranar Alhamis 12/9/1996, bayan
Shaikh Zakzaky (H) ya yi sallah tare da ‘yan'uwa, dama ya saba ya
kan dan tsaya a gaggaisa a gana da ‘yan'uwa, sai aka ji an kira
wayar tarho din Malam (H), yana dauka ya fara magana sai ya
ji ana kyalkyale dariya. Ashe daidai wannan lokacin an riga an
turo ‘yan sanda ne zuwa gidansa, an kira ne don a tabbatar ko
yana gidan.

Suna zuwa suka mamaye gidan, suka kewaye ko ina da
bindigogi suna ta hayaniya. Da yake jerin gwanon motoci ne na
‘yan sanda da ‘mopol’. Sai Malam Zakzaky (H) ya fito gare su, nan
suka bashi ‘warrant of search’ (takardar da ke nuni da an basu
damar su zo gidansa su yi bincike). Wai suna zargin akwai
makamai a gidan. Suka cewa Malam yana iya chaje ‘yan
sandan da za su shiga su yi binciken ma don kar su shiga
masa da wani abu. Amma Malam (H) yace musu suna iya
shiga ba tare da ya caje sun ba, ba matsala, amma akwai
sashen mata da bai bukatar namiji ya shiga face ‘yan sanda
mata. Don haka suka nemo mace ‘yar sanda ta shiga don binciken.

‘Yan sandana karkashin mataimakin kwamishinan lokacin,
Mukhtar Ibrahim suka shiga suka gama bincikensu ba su samu
komai na makami ba. Da suka fito, sai suka cewa Malam (H)
yanzu za su tafi da shi ya je ofishinsu a Kaduna ya saka hannu
a kan cewa an zo an binciki gidansa amma ba a samu makami ba.

Malam (H) yace musu wane irin abu ne haka? Kun nuna min
takardar bincike ne, baku nuna min na kamu ba, kuce kuna
son ku yi kamu ne, ya za a ce ba a samu makami a gidan
mutum ba kuma sai ya je ofishin ‘yan sanda sannan ya
tabbatar da ba a samun ba? Ba ‘yan sandan ne a nan ba?
ACP Muktar ya dage a kan cewa ba kamu bane, kawai za a je
a rubuta rahoto ne a dawo. Sai Malam Zakzaky yace masa kar
ka mai da ni wawa mana, kuce kun zo ku yi kamu kawai. Ya
shiga gida ya tattaro jakarsa, ya sanya sutura da littafan
addu’o’i a ciki, ya fito.
Nan ‘yan'uwa da suka tattaru a wajen suka ce ba a isa a tafi da
Malam din ba. Amma sai Malam (H) ya musu jawabi, a ciki
yake cewa, kar yan uwa su damu, ko da yake sun ce ba kamu
bane zai je ya dawo ne, amma in ma kamun ne, ai an sha
kama shi a baya, don haka ba matsala. Yai wa ‘yan uwa
wasiyya da cewa: “A yi kokari ya zama Harka ta cigaba, duk
abin da aka sanana yi kar a fasa.”

Wasu ‘yan'uwa sun rika kuka a lokacin, amma Jagora ya basu
hakuri da cewa “Kar ku bamu kunya mana.” Sannan Malam (H)
yace ma Muktar tunda kun ce ba kamu bane, to ku barni na
tafi a cikin motata in ya so kai sai ka shiga cikin motar mu je.
Amma zan tafi tare da kanina Malam Badamsi, kuma Malam
Turi zai tuka mota. Mukhtar ya amince Malam Turi ya tuka
mota, Malam Zakzaky na gaba, Malam Badamasi da Muktar
Ibrahim suna baya, aka tafi.

Wannan Mukhtar Ibrahim din da ya jagoranci kamun ya mutu
yana matakin AIG a aikin dan sanda a ranar 22 ga Disambar
2012, kimanin shekaru bakwai da suka gabata.


A daidai lokacin da ‘yan sandan suka je gidan Malam Zakzaky (H)
da ke Kwarbai da nufin tafiya da shi, ashe wasu kuma sun je
sun kama Malam Abubakar Almizan da Alhaji Hamid Danlami
a gidansa da ke babban dodo, tare kuma da wani ma’aikacin
kamfanin buga takardu mai suna Malam Shittu.

Shi Malam Shittu a lokacin ba Buraza bane, kawai ma’aikacin
kamfanin buga takardu ne, aka aiko shi ya kawo jaridar
Almizan ta wannan makon da aka buga (printing) a wajensu.
Ya shawo kwana kenan rike da jaridun Almizan makil a
hannunsa, kawai yai kicibis da rundunar yan sandan, sai suka
kama shi suka wurga shi da duk Almizan din cikin mota.

To, an tafi da su uku din tare da su Malam Zakzaky (H), amma su
suna wata mota daban. Har zuwa sadda aka kusa isa Kaduna,
sai ACP Mukhtar ya roki Malam Zakzaky (H) a kan ya taimaka
musu su koma wata motar ta daban. Yayin da Malam ya yarda
musu, ana bude mota zai shiga nan yaga ashe an kamo su
Alhaji Danlami, Malam Abubakar Almizan da Malam Shittu da
kuma tulin Almizan ma.

Kai tsaye suka wuce da su ‘Headquater’ din ‘mobile police’ na
Kaduna, yayin da motar Malam aka kai ta wani wajen daban,
aka ce Shaikh Turi da Malam Badamasi su je su karbi motar su
koma gida an sallame su. Sai ya zama yanzu ana tsare ne da
Malam Zakzaky (H), da kuma su Alhaji su uku.

WASHE GARIN KAMA MALAM ZAKZAKY (H)

Wannan abin da ya faru tuni duk kasar ko ina an samu labari
cewa an kama Malam Zakzaky (H), kuma hakan yasa washe gari
Juma’a (13/9/1996) aka shirya gagarumar Muzahara a garin
Zariya don bayyanawa duniya halin da ake ciki da kuma nuna
rashin yarda da kama Shaikh Zakzaky (H) da Janar Abacha ya yi,
wanda aka gabatar da gagarumar

Muzahara a garin Zariya.
Muzaharar da dubun-dubatar ‘yan'uwa suka halarta, sai ya
zamana an turo ‘yan sanda (mopol) sun budewa mata wuta, ta kai ma ga an yi ruwan Shahidai. Domin kuwa wannan ne karon
farko da a take aka samu ‘yan'uwa akalla 15 da suka yi
Shahada nan take a tarihin Harkar Musulunci

An faro Muzaharar ne daga masallacin Juma’a na sabon gari,
aka miko ta kan titin PZ aka nufo cikin garin Zariya, a yayin da
Shaikh Muhammad Turi ke gaban Muzaharar yana jagorantar
‘yan'uwa suna tafe cikin tsari da nizami. A daidai lokacin da
aka iso wajen shatale-talen da ke gaban kofar doka, sai aka ga
‘yan sandan mobayil sun yi layi sun tare kofar shiga Zariya
cikin shirin bude wuta.

Ganin haka sai ‘yan'uwa suka kara chaji, suka ninka kabarbarin
da suke yi tare da hailala, suka tunkari ‘yan sandan, ai kuwa
‘yan Sandan suka fara budewa ‘yan'uwa wutan kan mai uwa da
wabi, wasu suna harba tiyagas, wasu suna harba bindiga akan
‘yan'uwa. Amma sai ya zama ‘yan'uwa sun samu sabati, ana
harbi wasu na fadi kasa amma ‘yan'uwa suna kara dannowa,
har zuwa lokacin da ‘yan Sandar nan suka ga harsashinsu zai
kare, nan suka ari na kare ta hanyar Jos, suka arce.

A yayin da suke harbin, yan'uwa na cidadowa, Malam Turi
Allah ya kara masa yarda, yana karawa ‘yan'uwa chaji, saboda
tsayawar da ya yi da dakewarsa a matsayinsa na jagoran
Muzaharar yasa ‘yan'uwa ma suka dake, sai ya zama ‘yan can
baya ma ba su san an yi harbi ba, sai dai wasu da suka kariso
wajen kofar Doka suka ga jini a kasa, aka ce musu ai an bude
wuta ne, yayin da wasu kuma sun dai ji kamar tiyagas amma
ba su tabbatar ba, wasu kuwa sai da aka je wajen rufewa suka
ga ana daddaga mutane aka ce musu ai an samu Shahidai.

An ayyana cewa za a rufe Muzaharar ne a Babban Dodo,
hakan kuwa aka yi, an iya raka ‘yan Sandan a na-kare, aka
wuce aka shiga Zariya aka yi burki a filin na Babban Dodo,
inda su ma wadanda aka harba aka kwashe su zuwa can.

Bayan da ‘yan uwa suka hadu ne, sai aka gabatar da jawabi
akan dalilin wannan Muzaharar, aka kuma sanar da ‘yan'uwa
irin ta’addancin da ‘yan sanda suka yin a bude wuta akan ‘yan'uwa
masu Muzaharar lumana, inda a nan ne da yawan ‘yan'uwa
suka ma san cewa ashe ‘yan Sanda sun bude wuta.

Kun san a wancan lokacin, shekaru 21 kenan baya, ba kafafen
sadarwa kamar yanzu, kuma ‘yan'uwa sun halarci Muzaharar
sosai, don haka an yi yawan da ya zama har an bude wuta
amma da dama wasu basu sani ba ma. Ko da yake nizamin da
ake da shi a wancan lokacin da tsari ya taimaka sosai, na
cewa kowa yana tsayawa a muhallinsa ne, ana barin kowane
ahalin abu ya gabatar da abin, wani bai cika shiga aikin wani
ba, a yayin da yan'uwa kan zama a sahu ba tare da zaban inda
ya musu, ko yawo a gefen titi a sa’ilin Muzahara ba.

A Babban Dodo ne aka daddago gawarwakin Shahidan da aka
harba, inda nan take wajen ya rude da Kabbarori. Ya zama
Shaikh Muhammad Turi ne ya jagoranci sallar Janazarsu.
Amincin Allah ya kara tabbata a gare su.

‘Yan'uwan da suka samu rabon Shahada a wannan Muzaharar
kamar yadda yake a takardar da Shaikh Muhammad Turi ya
sakawa hannu a ranar Larabar bayan waki’ar 18/9/1996 sune:

1- Shaheed Abdullahi Musa– Shekaru 22
2- Shaheed Yusuf Musa T/Jukum – Shekaru 20
3- Shaheed Usman Sulaiman Kwangila – Shekaru 30
4- Shaheed Usman Ibrahim Waziri Samaru – Shekaru 24
5- Shaheed Salisu Abdullahi Gabari – Shekaru 23
6- Shaheed Alhasan Badamasi D/Tagwai – Shekaru 40
7- Shaheed Musa Muhammad Dumbi
8- Shaheed Jabu Muhyiddeen Kano.
9- Shaheed Ishak Salihu Mahuta
10- Shaheed Ashiru Yusuf Mahuta – Shekaru 21
11- Shaheed Muhammad Auwal T/Wada Zariya.
12- Shaheed Aliyu Alhaji Sadau
13- Shaheed Abubakar Rabi’u – Dan shekara biyu da rabi.
14- Shaheed Nuhu Adamu Dokan Mai jaki.
15- Shaheed Isa Musa Muciya.

Wadannan ne Shahidan da aka samu nan take a wannan
lokacin da ‘yan sanda suka afkawa Muzaharar KAMUN MALAM ZALUNCI NE da aka yi a Zariya ranar Juma’a 13 ga Satumbar
1996. Wanda kuma Larabar da ta biyo bayan wannan, an kuma
yin wata Muzaharar a Kaduna, inda ‘yan Sanda suka kara bude
wuta, aka samu Shahidai.
Zan cigaba.

Ka/ki Dinga bibiyar shafinmu na Ma'asuma Nigerian news update don samun ingantattun labarai. Domin shiga shafinmu Sai ka/ki shiga ta nan👇👇👇

www.maasumah.com.ng

Sai kun zo.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post