KO KASAN ME JAMI'AN TSARO SUKA CE GAMEDA KISAN DA SUKAYI A RANAR ASHURA????

 KASAN ME JAMI'AN TSARO SUKA CE GAMEDA KISAN DA SUKAYI A RANAR ASHURA ?? .


@MA'ASUMA NIGERIA NEWS UPDATED.

Abun ya bani mamaki duba da yadda jami'an tsaron nigeria suka dauki muggan makamai dominsu kashe mutanen da basu da ko wuka bare bindiga.

A haka suka dage wajen  harba masu tiyagas da alburushi mai rai suna ta kashe bayin Allah wadanda basujiba basu ganiba.

Ta bangare guda kuma sukayi sasanci da barayin shanu da kidnappers wai cewar sun tuba bazasu kara kisaba ko kidnappeing ba. Abun yanada rikitarwa wallahi amma Allah ya bayyana mana shi wallahi yanzu munsan suwanene barayin shanu kuma suwanene kidnappers, abun yafito fili ga mai hankali.

Dalilin da yasa nace haka nayi nazari akan barayin shahu da kidnappers sai naga idan ba a daure masu gindiba to yazasu yi su samu makamai  kuma har ace sojan nigeria bazai iya kawo karshen wannan matsalaba. Nasan a kwankin baya ana cewa sojan nigeria shine wanda har wata kasar suna temaka mawa wajen yakar yan ta'adda.

Amma abun kunya sai gashi sojan nigeria shine wanda yake kashe jama'an kasarsa wadanda basuda koda allura wannan abun kunya har ina. Wallahi jami'an tsaron nigeria kunji kunya wallahi  kuma sai Allah ya tambayeku akan hakin mutanen da kuke zalunta.

Ni banga amfanin kuba wallahi babu abunda kuka iya sai yaki da wanda bashida makami.shi kuma mai makami sulhu kuke yi dashi, wallahi Allah ya isa.

Kun kashe mutane a garuruwa daban daban amma dan zalunci kuce baku bane to suwanene ko mune muka kashe kanmu da kanmu koko wasune suka yi shiga irin taku domin su bata maku suna. To yazama dole musan ko suwa suka kashemu idan baku bane to ku fito mana da su. Idan haka bata samu ba to shi kenan sai mu bari sai muje gaban wanda yayi mu kuma shine zai fitarma kowa da hakinsa akan kowa.

Bayan haka ina mika janjina ta ga 'yan uwan da suka jure ma wwannan abun wanda Dalilin juriyarsune Allah yasa basu cimma gurinsu ba. Domin sunso suyi ma wannan harka sharri ta kowanne hali Amma yan uwa suka juru suka tsayu akan nizimi. Allah muna tawassuli da AHLAL BAITI (AS) ka karbi shahidanmu a matsayin da ka karbi shahidan karbala.

'yan uwa mukara hakuri kamar yadda malamanmu suke ta fadi mana cewa haka hanyar take babu shakka bamu jahilci hakan ba kuma munada masaniyar hakan. Saidai mu jira lokaci kawai.

DAGA KARSHE................
Dan Allah 'Dan uwa ko 'yar uwa ida ka/kin tashi Addu'arku ku sakani a ciki domin ina barar addu'arku sosai akan wasu abubuwa da sukaa dameni Allah ya yaye mana baki daya.

Nagode nine kaku ________Ammar Abubakar shadow_______

Wakilin shafin nan mai farin jini wato MA'ASUMA NIGERIA NEWS UPDATED.

Ka rika biybiyar wannan shafin na MA'ASUMA domin akwai  shirye shirye damuke kawo maku ta kowanne bagare na rayuwa.

Idan kana son shiga jeka kasa ka danna wannan sunan zai kaika shafin mu.

www.ma'asuma.com.ng

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post